✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Kannywood: Yadda kafar YouTube ke sauya akalar fina-finan Hausa

Aminiya ta gano jadawalin yadda ake samun kudi a kafar YouTube.

Masana’antar fina-finan Hausa Kannywood ta fara shiga matsala tun lokacin da kasuwar faya-faya CD ta fara samun matsala biyo bayan fama da matsalolin satar fasaha da tabarbarewar tattalin arziki.

An yi ta kokarin farfado da harkar tare da kirkiro wasu hanyoyin da masu ruwa da tsaki a harkar suke ganin za su dawo da kasuwancin fim din domin gyara masana’antar.

  1. Ambaliyar ruwa ta lalata gidaje sama da 200 a Taraba
  2. Mukabala: An bai wa Abduljabbar damar kare kansa —Kwamishina

A zabukan shekarar 2015 da 2019, ’yan Kannywood da dama sun ce sun shiga harkokin siyasa ne da tunanin cewa idan aka samu nasarar kafa gwamnati za a taimaka musu wajen gyara masana’antar.

Sai dai Aminiya ta lura maimakon gyara masana’antar, siyasa ta zo ta kara raba masana’antar ne, inda jaruman suke fitowa fili suna sukar juna akan bambancin ra’ayin siyasa, musamman a lokutan zaben.

Kazalika, an koma haska fina-finai a sinima, inda masu ruwa da tsaki da masoya a harkar suka fara murna da tunanin cewa masana’antar za ta dawo da karsashinta ganin yadda ake zuwa kallon fim a sinimar da ke rukunin kantunan Ado Bayero Mall a Kano, da gidajen kallo a wasu jihohin na arewacin Najeriya.

Fim din da ya fi tara kudi a Kannywood

Binciken Aminiya ya gano cewar, ba wani kudin kirki ake samu a nuna fim a sinima ba, wanda hakan bai rasa nasaba da kasancewa sinimar mai kyau da tsari guda daya ce kawai a Kano.

Binciken da Aminiya ta yi daga Box office Kannywood, inda a nan ne aka sanya fina-finai da kudaden da suka samar a sinimar Kano, Aminiya ta gano cewa fim din ya fi tara kudi shi ne fim din ‘Ka yi na yi’ na Abubakar Maishadda wanda aka kammala haskawa a makon jiya.

Fim din ya tara kudi Naira miliyan 5.46 a mako uku da aka yi ana haskawa a sinimar ta Kano.

Fina-finai 10 da suka fi tara kudi a masana’antar Kannywood a sinimar Kano

1. Ka yi na yi – ₦5.46m

2. Mati A Zazzau – ₦4.84m

3. Tsakaninmu – ₦3.69m

4. Bana Bakwai – ₦3,61m

5. Hauwa Kulu – ₦3.56m

6. Kar ki Manta Da ni – ₦3.54m

7. Fati – ₦3.13m

8. Yaki A Soyyaya – ₦2.43m

9. Wakili – ₦2.16m

10. Hafeez – ₦1.94m

Daga cikin fina-finai guda 10, guda biyar na Abubakar Bashir Maishadda ne, wanda hakan ya sa ake masa lakabi da ‘King of box office’.

Fim din da ya fi tara kudi a Nollywood na Kudancin Najeriya

A wani binciken kuma da Aminiya ta yi a wani bangaren kuma, fina-finan Kudancin Najeriya na samar da miliyoyin kudade ga masu shirya fina-finai.

Fim din ‘Omo Ghetto’ na Funke Akindele ne kan gaba a masana’antar Nollyood din, inda ya tara makudan kudi har sama da Naira miliyan 468.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwar Kungiyar Masu Lura da Sinimomi ta Najeriya (CEAN), kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito.

An rawaito tare da taya murna ga mai shirya fim din ne lokacin da fim din ya tara wannan kudi a makonsa na hudu cikin makonni bakwai da zai yi ana haskawa domin ya kere wanda a da shi ne kan gaba da Naira miliyan 450.

Sannan bayan nan, an kuma ci gaba da haska shirin na mako uku.

A wani binciken na Aminiya kuma, mun gano cewa fim din Kudancin na 100 a kasan jerin wadanda suka fi tara kudi shi ne, ‘The Miracle Center’, na Niyi Towolawi wanda ya tara kudi sama da Naira miliyan 11.

Wakokin Kannyood

A da can masu waka a masana’antar ba su cika samun kudi sosai ba, domin sai dai su rika yin waka a saya a sa a fim kawai.

Daga baya sai suka fara yin kundin wakoki suna sayarwa a kasuwa kamar fina-finai.

Sai dai kamar yadda kasuwancin CD ya lalace, haka kasuwancin wakokin suma, inda dole suka dakatar da shirya kundin domin a lokuta da dama ko kudin da aka kashe ma ba sa dawowa.

Hakan ya sa mawakan suka sauya akalar wakokinsu zuwa ga wakokin siyasa, inda mawakan da dama suka sami tagomashi.

Baya ga wakokin siyasa, sai mawakan suka koma kafar YouTube, inda suke wakokinsu, suna sanyawa a kafar, ana kallo ana biyansu kudade masu yawa.

Aminiya ta garzaya kafar YouTube domin ganin irin wainar da ake toyawa, inda ta ga yadda wakokin Hausa suke cin kasuwa.

Wakar Hamisu Breaker ta ‘Jaruma’ mutum miliyan 5.9 suka kalle ta zuwa ranar Laraba da muka ziyarci tasharsa ta shafin na YouTube .

Akwai kuma wakar Hamisu Breaker mai taken ‘Karshen Kauna’, wadda ita kuma mutum miliyan 3.9 suka kalla.

Wakar Umar M. Shareef ta ‘Ciwon Idanu’, wacce aka yi a fim din Ciwon Idanu an kalla sau miliyan uku.

Da muka garzaya tashar Garzali Miko kuwa, wakarsa ta ‘So da Kauna’ sama da mutum miliyan uku suka kalla, sai wata wakarsa ‘Ruwan zuma’ da mutum miliyan 2.3 suka kalla.

Kudin da ake samu a YouTube

Babu takamaiman yanayin kudin da za a samu idan an sa waka a YouTube, domin yanayin kudin da za a samu yana da alaka ne da yawan mabiya da yawan kallo da aka yi da kuma talla, wanda YouTube din ne da kansu suke saka wa.

Sannan kudin na bambanta da kasashe, inda kudin Najeriya bai kai kudin da za a samu wasu kasashen waje ba.

Aminiya ta tambayi wasu ’yan fim da mawaka kan yanayin kudin, inda suka tabbatar da cewa ba za su iya fadar ko nawa ne kudin ba.

Sai dai a binciken Aminiya a wani shafin intanet mai wayar da kan mutane kan amfani da kafar YouTube, ta gano cewa za a iya samun Dalar Amurka 4.18 idan mutum 1,000 suka kalli abin da ka sa a shafin YouTube.

Idan aka canja Dalar zuwa Naira a musayar Naira 410 akan Dala daya, za a samu Naira 1,713.0 a duk mutum dubu 1. Idan aka lissafa a haka, za a samu N1,713,800 a kallo miliyan daya.

Hakan na nufin za a iya samun sama da Naira miliyan daya da rabi a duk kallo miliyan daya, wanda kuma kudin zai iya fin haka idan tashar na da mabiya da yawa.

A daya bangaren kuma, ba a kashe kudi da yawa wajen shirya waka, sannan kuma kyauta ake sanyawa a tashar YouTube, idan kuma an kalla a biya ka.

Shi kuwa fim, ana bukatar kudade da yawa domin biyan jarumai da sauran ma’aikatan bayan fage da sauransu.

Fina-finai sun fara komawa YouTube

A wani bangaren kuma, akwai fina-finai da dama da yanzu haka a YouTube din ake cin kasuwarsu.

Fitacce daga cikinsu shi ne ‘Izzar So’, wanda Aminiya ta gano yana samun masu kallo miliyan daya ko sama da hakan, kuma duk mako yake fita.

Akwai sauransu irinsu ‘A Duniya’ da ‘Haram’ ga kuma yanzu za a fara haska ‘Labarina’ da kuma ‘Gidan Danja’ a YouTube din.

‘Dalilin da wakoki suka fi samar da kudi’

Aminiya ta zanta da mawaki MD Anas, mai kamfanin Sabuwa Concept, inda ya ce kamata ya yi a ce fim ya fi samar da kudi, amma sai aka samu akasi.

“Da a ce muna da manyan sinimomi a Arewa, da fim ya fi samar da kudi. Ka ga wannan kididdigar da ka yi, a sinima daya ce kawai. To ina a ce akwai irin wannan kamar a jihohi 10, sai a lissafa hakan sau 10. Ka ga za a samu kusan Naira miliyan 50 ke nan.

“Amma dalilin da ya sa yanzu muke cin kasuwar waka shi ne ka ga ita waka kowa na ji ana ce mata general language, wato yare ne da kowa ke ji. Sabanin fim da dole sai mai jin harshenka, kuma ko yana jin harshen zai iya yiwuwa ba ya sha’awar jigon fim din. Sannan kuma ka ga waka bata da tsawo. Mutum zai shiga YouTube ya kalla dan minti biyar zuwa 10 ya gama.”

‘Abin da ya sa wakokin ke danne fina-finai a yanzu’

Aminiya ta tuntubi fitaccen furodusa a masana’antar Kannywood, Naziru Auwal, wanda aka fi sani da Naziru Danhajiya, inda ya ce lallai a yanzu wakokin sun fi fina-finai samar da kudi.

A cewarsa, “Da gaske ne saboda a yanzu ba mu da kafar da muke ba masu kallonmu fim suna kallo sai a film house da ke Kano sannan mutumin da ke Legas yana son ya kalli fim, Abuja ta masa nisa. Wanda ke Kaduna ma ba zai iya zuwa Kano ba.

“Ita kuma waka kana gida duk lokacin da ka so kana kunna YouTube da an sa za ka kalla. Shi kuma fim duk tallar da za ka masa duk mutumin da yake nesa ko da yana so ya kalla sai dai ya hakura sai dai watakila idan ya zo YouTube ya kalla.

“Don haka nisan da ake da shi, saboda yanzu hanya daya kawai muke da ita wajen kawo wa masoya fim, dole waka ta danne fim a yanzu. Ba mu san ko nan gaba idan an samu wasu kafofin da za a rika samar a makallata fim.”

Da Aminiya ta tambaye shi yadda yake ganin za a shawo kan lamarin, sai ya ce, “Abu daya da ya kamata shi ne fina-finan da muke yi a kara musu inganci.

“Ka ga yanzu ’yan Kudu suna kai fina-finansu manhajar Netflix, inda suke samun makudan kudade. Yanzu haka mun samu irin wannan damar muna ta tura fina-finai kuma mun tura musu muna jira su duba su tantance domin amincewa da su.

“Da zarar mun samu fina-finanmu sun shiga Netflix, za mu samu masu zuba hannun-jari da yawa da za a kara habaka harkar. Don haka abu mafi muhimmanci kawai a yanzu shi ne inganta fina-finan,” inji shi.

Alakar Nollywood da Kannywood

Kabiru Musa Jammaje, wanda malami ne da ke koyar da harshen Turanci, ya shiga masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, wanda ya fi mayar da hankali wajen shirya fina-finai cikin harshen Turanci.

Jammaje ya shirye fina-finai kamar su; ‘This is the Way’, ‘Light and Darkness’, ‘In search of the king’ da kuma ‘The Best Choice’ wanda aka kashe kudi sama da miliyan 30 wajen shirya shi.

Alaka tsakanin Nollywood da Kannywood ta fara kulluwa tun wasu shekaru da dama da suka shude, inda Nollywood ke gayyatar jarumai irin su Ali Nuhu, Sani Danja da sauransu cikin fina-finansu.

Fim din ‘Karangiya’ na daga cikin irin fina-finan da aka gayyaci jaruman Nollywood suka taka rawa a cikinsa.

A wannan karon kuma Jammaje ne daga  Kannywood, ya gayyaci wasu manyan jarumai daga Nollywood cikin fim dinsa na ‘The Best Choice’.

Jarumai kamar su Sola Sobowale, Enyinna Nwigwe, Nancy Isime, Segun Arinze da sauransu za su taka rawa a fim din.

Tuni masu ruwa da tsaki a masana’antar ta Kannywood suka fara mai da hankali wajen bude kafofi a YouTube, ganin yadda ake samun kudi.

Kazalika, wasu sun karkata hankalinsu wajen shirya fina-finai masu dogon zango, inda suke kashe kudi kadan, sannan su dora shi a YouTube, wanda cikin kankanin lokaci ake samun dubban mutane su kalla, kuma su samu kudi cikin sauki.