Daily Trust Aminiya - Yadda kamfanin Gotel na Atiku ya sallami ma’aikata 54
Subscribe

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar

Yadda kamfanin Gotel na Atiku ya sallami ma’aikata 54

Ranar 1 ga watan Mayu rana ce mai muhimmanci ga ma’aikata saboda a wannan yinin ake bikin Ranar Ma’aikata ta Duniya da nufin tunawa ko yabawa da kwazon ma’aikata.

Sai dai a bana ba ta zo wa ma’aikatan kamfanin Gotel Communications da dadi ba, domin a maimakon yabo, takardun sallama aka bai wa 54 daga cikinsu a jajiberin ranar.

Kamfanin, wanda ya mallaki gidajen rediyo da talabijin na Gotel a Yola, babban birnin jihar Adamawa, yana karkashin Rukunin Kamfanoni na PRIAM ne, mallakar tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar.

Daya daga cikin takardun sallamar da ke yawo a intanet na dauke da sa hannun shugaban kamfanin na Gotel Communications, Mohammed El-Yakub.

Shawara nan take

Wasikar ta fara ne da cewa, “Hukumar gudanarwa ta yanke shawarar dakatar da ayyukanka ba tare da bata lokaci ba…” daga nan ta yi alkawarin biyan su hakkokinsu, sannan ta rufe da yabawa da gudummawar da ma’aikatan suka bayar tana musu fatan alheri.

Biyar daga cikin ma’aikatan da aka sallama dai manyan ma’aikata ne, sauran kuma kanana.

Ko da yake ba a bayyana dalilin sallamar a cikin wasikar ba, wasu rahotanni na alakanta matakin da halin ha’ula’i da tattalin arzikin Najeriya da ma sauran kasashen duniya ya fada ciki sakamakon mamayar da annobar coronavirus take ci gaba da yi.

Wasu rahotannin sun kuma ce da ma kamfanin yana fama da matsalar kudade.

Dalilin daukar matakin

Sai dai kuma wasu kafofin yada labarai sun ambato El-Yakub yana cewa an sallami ma’aikatan ne a yunkurin sake wa kamfanin fasali, wanda aka fara tuni.

Ko a karshen shekarar 2019 ma mai magana da yawun Atiku Abubakar din, Paul Ibe, ya fitar da sanarwa a kan cewa tsohon mataimakin shugaban kasar ya tattara kamfanoninsa a karkashin inuwa daya kuma ya tsame hannunsa daga tafiyar da su.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa da ma dai tun kafin samar da rukunin na PRIAM tsohon mataimakin shugaban kasar ba ya tsoma baki a harkar gudanar da kamfanin duk da cewa shi yake samar da kudin gudanar da shi.

‘A hana sallamar ma’aikata…’

Yayin da wannan lamari ke faruwa dai, a wata sanarwa da ya fitar ranar Alhamis albarkacin bikin Ranar Ma’aikata, Atiku Abubakar ya yi kira ga Majalisar Dokoki ta Kasa ta haramta wa masu masana’antu da ma’aikatu sallamar ma’aikata ko rage musu albashi sakamkon annobar coronavirus.

Tsohon mataimakin shugaban kasar dai na cikin mutanen da suka bayar da gudunmawar kudi don yaki da annobar coronavirus a Najeriya, inda Rukunin Kamfanoni na PRIAM ya tallafa da Naira miliyan 50.

A kwanan baya ne dai Kungiyar Masu Gidajen Rediyo ta Talabijin ta Arewacin Najeriya ta yi gargadin cewa tashoshi 40 na yankin ka iya durkushewa saboda matsin da annobar ta jefa tattalin arzikin kasa.

More Stories