✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

Yadda Kannywood ta girgiza da rasuwar Ummi Lollipop

Jarumai da taurarin Kannywood sun bayyana kaduwa da rasuwar tsohuwar jarumar masana’antar, Fadila Muhammad wacce aka fi sani da Ummi Lollipop. Manyan jarumai irinsu Ali…

Jarumai da taurarin Kannywood sun bayyana kaduwa da rasuwar tsohuwar jarumar masana’antar, Fadila Muhammad wacce aka fi sani da Ummi Lollipop.

Manyan jarumai irinsu Ali Nuhu da Adam A. Zango da Hadiza Gabon da sauransu ne suka sanya hotonta a shafukansu na Instagram, inda tare nuna jimamin rasuwarta da kuma aika sakon ta’aziya.

Ali Nuhu ya wallafa a shafinsa na Instagram cewa, “Allah Ya jikan ki diyata (daughter) ya sa mutuwa hutu ce”.

Shi ma Adam A. Zango wanda ya wallafa a shafinsa na Instagram bidiyon wakarsa na Hubbi da marigayiyar, ya ce, “Allah Ya jikanki.”

Ita dai marigayiya Fadila tsohuwar jaruma ce da ta yi fice a baya, musamman a fim din Hubbi, inda ta ja fim din tare da Ali Nuhu da Adam A. Zango.

Sauran jaruman Kannywood da suka aika da jaje sun hada da darakta Aminu S. Bono da Sani Danja, wanda shi ya ce, “Allah Yajikan ki da Rahama Allah Ya sa Aljannah makoma”, a sakon ta’aziyya da ya wallafa tare da hoto marigayiyar a shafinsa na Facebook.

Rahama Sadau ta ce, “Fadila kan kasance mutuniyar kirki kuma ‘yar was mai ban mamaki!! Allah Ya gafarta miki, Ya sa ki a Aljannah Firdausi. Amin summa amin”.