✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda kasuwar ’yan kwallon kafa ke ci a yanzu

Juventus za ta yi musayan Daniele Rugani ko Cristian Romero domin dauko Alexandre Lacazatte daga Arsenal.

Kungiyar Juventus na zawarcin dan wasan gaban Arsenal, Alexandre Lacazatte.

Jaridar Calcio Mercato ta ruwaito Juventus a shirye take ta sanya dan wasan bayanta, Daniele Rugani ko Cristian Romero domin musaya wajen cimma nasarar dauko dan wasan gaban, dan kasar Faransa.

Idan ba a manta, Juventus ta sallami kocinta Sarri, inda ta maye gurbinsa da Andrea Pirlo.

Hakan nan a kasar Italiya, jaridar Guardian ta ruwaito kungiyar Lazio na gab da dauko dan wasan Manchester City da Spain, David Silva wanda kwararren mai buga tsakiya ne.

Ita kuma kungiyar Liverpool, wadda ta lashe gasar Firimiyar Ingila ta samu tsaiko ne wajen dauko dan wasan tsakiyan Bayern Munich Thiago Alcantra duk da cewa dan wasan ya nuna sha’awarsa na zuwa kamar yadda jaridar Sky Sport ta ruwaito.

A bangaren ’yan wasan Najeriya, kungiyar Fenerbahce ce ke zawarcin sayan dan wasan Najeriya Kelechi Iheanacho daga kungiyar Leicester City ta Ingila kamar yadda Fotospor ta ruwaito.

Kungiyar ta Fenerbahche ta taya dan wasan ne a kan Fam miliyan 12.

A wani rahoton kuma da jaridar Mirror ta ruwaito, dan wasan Real Madrid Gareth Bale ba zai bar kungiyar ba duk kuwa da cewa ba ya samun buga wasanni sosai.