Yadda Kilisa ke jawo lalacewar ‘kananan yara’ a Kano | Aminiya

Yadda Kilisa ke jawo lalacewar ‘kananan yara’ a Kano

    Abubakar Muhammad Usman

Kilisa ko hawan doki wata al’ada ce da ta jibanci wadanda suka gaji ko suke da alaka da sarauta a kasar Hausa.

Akan yi Kilisa ne musamman a lokutan bukukuwa a kasar Hausa; kamar bikin Sallah karama da babba, suna ko daurin aure.

Kilisa ta dauki sabon salo a  birnin Kano, inda yara masu kananan shekaru ke cin karensu babu babbaka a baya-bayan nan.

Sai dai karbar ragamar yin Kilisa da kananan yaran suka yi a cikin unguwannin da ke kwaryar birnin Kano da kewaye ya bar baya da kura, inda yake haifar da matsaloli masu tarin yawa.

Illar yin Kilisa a tsakanin yara kanana 

Iyaye da dama sun koka kan yadda Kilisa a yanzu ke yin barazana ga tarbiyyar ’ya’yansu a Kano.

Aminiya ta yi bincike ta karkashin kasa tare da gano irin illar da Kilisar take haifarwa a tsakanin kananan yara da ke yin ta.

Binciken ya gano yadda yara wadanda shekarunsu ba su gaza 13 zuwa 17 ba ke daukar wasu dabi’u a sanadin hakan.

An gano cewa a dalilin shiga harkar, yara da dama sun fandare sun daina zuwa makaranta, lamarin da ya bude musu kofar lalacewa da bijire wa umarnin iyayensu.

Wasu yaran kuma, sun shiga yin harkar shaye-shaye ko kuma fadan daba tsakaninsu da ’yan wata unguwar ko abokan hamayya.

Wasu majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa yara na shiga yin sace-sace duk da nufin samun abin da za su hayi doki domin yin kilisa.

Kazalika, a lokutan da ake yin kilisa doki kan kwace ya taka ko doke ’yan kallo, wani lokaci kuma masu yin kilisar ne ke jin rauni, idan kuma abun ya zo da tsautsayi a kan yi asarar rai ko dukiya.

Dalilin da ake yin Kilisa

Yayin zantawarsa da Aminiya, Barden Galadiman Masarautar Karaye a Kano, Muhammad Suraj Karaye, ya bayyana yadda ake yin Kilisa da kuma irin illoli da ta haifar a cikin unguwannin Kano.

“Kilisa abu ne na al’ada kuma yana da tsari, saraki sukan yi hawa da doki don ba shi horo kar ya lalace ya daina yin abin da ake so, wannan shi ne ya kawo ake yin Kilisa a lokutan bukuwan Sallar Gani ko Sallar Idi.

“Hadimin sarki da yaransa sukan fita yin Kilisa don horar da doki ya san hanya, ya saba da yanayin gari, shi ne dalilin da ya sa ake fita ran gadi.

“Kilisa abu ne da yake da tsari, ba a tsara shi don yi a cikin unguwanni ko kan kwalta ba, ba a tsara shi don yin sa barkatai ba kan gado ba.

“Amma yanzu za ka ga kananan yara na sukuwa da dawaki a cikin unguwanni ko kan kwalta suna buge mutane, wannan ba tsari ba ne,” a cewarsa.

Masarauta ta taka musu burki

Shi ma wani barasake da muka zanta da shi daga Masarautar Rano a Jihar Kano, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tofa albarkacin bakinsa kan abin da sukuwar ke haifarwa.

“Yanzu yara ne wadanda ma ba su san doki ba ne ke hada kudi su dauki hayar doki ko kuma yara biyu su hada kudi su sayi doki don yin kilisa, wanda akasarinsu ba su iya dokin ba.

“Wasu lokutan akan samu tsautsayi idan sun fita suna buge mutane, wanda daga baya aka samu rahoto aka kawo wajen Hakimi, shi kuma ya sa aka yi yekuwa aka hana.”

Ya kara da cewa bayan hana yaran, sun sake dawowa wanda lamarin ya kai ga sarki, shi kuma ya bayar da umarnin hanawa tare da bada umarnin cafke duk wanda aka samu yana yi a fadin yankin Masarautar Rano.

“Sarki ya bayar da umarnin samun Hakimi a shaida masa baya son ya sake ji ko ganin ana yin kilisa,” inji sarakin.

A wurin kilisa dan uwana ya rasu

Wasu magidanta a kwaryar Kano sun bayyana yadda masu yin kilisar suka addabe su.

Amina Idris Sa’eed daga unguwar Gwammaja, ta bayyana wa Aminiya yadda kilisa ta ta yi ajalin kaninta a ranar 24 ga watan Disamba 2021.

“Kamar watanni hudu da suka wuce ya taba zuwa kilisa ya fado daga kan doki ya samu rauni bayan ya warke ya sake komawa.

“A ranar Juma’a 24 ga watan Disamba sun shirya kilisa shi da abokansa, wanda a rashin sani ita ce sanadin ajalinsa.

“Doki ne ya kade shi sannan ya taka shi sai abokansa suka dauke shi zuwa Asibitin Kwararru na Murtala, kafin su karasa ya rasu, sai aka ajiye gawarsa a dakin ajiye gawarwaki.

“Ba a jima ba aka kira mu a waya aka sanar da mu cewa doki ya taka shi amma ya rasu, gawarsa na Asibitin Murtala an ajiye ta,” kamar yadda ta shaida mana.

Yadda masu kilisa suka addabi Kanawa

Wani mazaunin unguwar Dorayi, Munir Muhammad Usman ya ce, “Babbar illar kilisa ga kananan yara a nan Kano [ita ce] tana haifar da rashin tarbiyya ga kananan yara, sannan tana sa su sace-sace.

“Idan karamin yaro ya fara wannan harkar kilisar, in har babu doki a gidansu, to zai shiga duk inda zai samu kudi don ya hayi doki.

“Sannan tana koyar da daba ko shaye-shaye, saboda shamakan da ake ajiye dawakan za ka ga yawanci akwai ’yan shaye-shaye a wurin, daga wannan shamakin zuwa wannan shamakin sai a ga yaro ya fara shaye-shaye ko ya shiga daba.

“Sannan za ka ga yaro ya hau doki ya shigo unguwa a guje idan ya buge wani aka masa magana sai ya shiga zagin mutane saboda ya koyi daba,” a cewarsa.

Shi kuma Imam Auwal, wani matashin dan kasuwa da ke zaune a unguwar Warure a cikin birnin Kano, cewa ya yi, “Gaskiya barin yara masu karancin shekaru suna yin kilisa ko hawan doki a cikin unguwannin Kano yana da hatsari ga su kansu da kuma al’ummar da suke tare da ita.

“Za ka ga suna yin sukuwar ne ba tare da ainihin kulawa ba ko karfin sarrafa dokin wanda idan ya kwace zai iya yi musu illa.

“Sannan akwai kwararar bata-gari a ciki, saboda wannan abun ya dade yana ci wa mutane tuwo a kwarya.

“Za ka ga tarbiyyar yara tana tabuwa, ka ga wasu yaran na shaye-shaye ko wani abu da bai kamata ba.

“Yawanci sai sun yi shaye-shayen suke hawa dokin, ko da sun iya sarrafa shi, babu cikakkaen hankalin iya tafiyar da shi tunda suna cikin maye.

Wata majiya ta bayyana cewa bata-gari na amfani yayin da ake kilisa a matsayin  wata dama ta yi wa masu kallo kwacen waya, da aikata sauran laifuka.

Wane mataki aka dauka?

A ranar 14 ga watan Yulin 2020, Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero ya bayar da sanarwar hana yin Kilisa a fadin jihar sakamakon korafe-korafe kan yadda masu yin ta suke ji wa mutane rauni da barnatar da dukiyoyin jama’a.

Kazalika, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kano ta sha yin farautar masu yin sukuwa da dawakai a lokutan bukukuwa ba tare da neman izini ba.

Barden Galadiman Masarautar Karaye a Kano, Muhammad Suraj Karaye, ya yi karin haske a kan hakan.

“Masarauta ta dauki matakai musamman Masarautar Kano, saboda tun lokacin marigayi Sarkin Kano Ado Bayero zuwa Sarkin Kano Halifa na 14 har zuwa Sarkin yanzu na 15, duk abin da ya kamata a yin a tura sakonni zuwa ga hakimai da dagatai sun yi.

“Har hawan angwanci da ’ya’yan masarauta suke yi don murnar bikinsu sai sun nemi izini, sannan a turawa hukumar ’yan sanda — Sai ma an ba wa mutum dama sannan zai yi hawan angwancin.

“Don haka ka ga an fitar da matakai da za a bi kafin yin kilisar.”

Mun tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Kano don jin ta bakinsa game da hukunci da aka tanadar ga masu yin Kilisa a jihar ta Kano, amma bai daga waya ko dawo da rubutaccen sakon da wakilinmu ya aike masa ba.