✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda komawar su Kawu Sumaila NNPP ta jijjiga siyasar Kano

Tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sauka a Kano tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da ke…

Tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran jam’iyar NNPP na kasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso ya sauka a Kano tare da wasu jiga-jigan jam’iyyar APC da ke shirin sauya sheka zuwa jam’iyarsa.

Kwankaso da tawagar tasa sun ne sauka a Filin Jirgi na Malam Aminu Kano ne da yammacin Juma’a, ciki har da tsohon Shugaban Majalisar Dokokin Kano, Alhassan Rurum, da Daraktan yakin neman zaben Tinubu, Abdulmumin Jibrin Kofa.

Sauran sun hada da dan Majalisar Tarayya mai wakiltar mazabar Tofa/Dawakin Tofa/da Rimin Gado, Abdulkadir Jobe, sai kuma tsohon Mashawarcin Shugaban Kasa kan Bangaren Shari’a wato Kawu Sumaila.

Dukkanin tawagar dai daga jam’iyar APC suka fice, kuma ana sa ran za su bayyana komawarsu NNPPn a hukumance a taron jam’iyar da za a gudanar a gidan Kwankwasiyya da ke titin Miller Road a Kano.

Cikin wadanda ake sa ran gani a taron tare da bayyana komawarsa da jama’arsa jam’iyar  amma bai halarta ba shi ne tsohon gwamnan Kano, Sanata Ibrahim Shekarau.

Aminiya ta gano cewa ba a ga Sanata Shekarau a tawagar ba ne sakamakon tattaunawa da yake yi da masu ruwa da tsaki kan komawar tasa.

To sai dai wata majiya mai tushe ta bayyana mana cewa Shekarau ya gama shirye-shiryen dangwarar da jam’iyar APC ya koma NNPP, inda zai bayyana hakan a hukumance ranara Asabar.