✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda likita ya yanke min hanji’

Irin tsaka-mai-wuyar da wata matar aure ta shiga da kuma yadda ta tsallake rijiya da baya

Wata matar aure da likita ya yanke wa hanji a wurin yi mata tiyata a asibiti ta bayyana irin tsaka-mai-wuyar da ta shiga da kuma yadda ta tsallake rijiya da baya.

Matar ta ce, bayan tiyatar da likitan ya yanke mata hanji a Abuja, bayan gida ya rika fitowa da al’aurarta, karshe dai sai wani asibiti ya tura ta aka yi mata wani sabon aiki, inda suka kashe makudan kudade, aka fitar da hanjin nata waje na tsawon wata shida.

Matar mai suna Irene Emmanuel, ta ce duk da haka, yanzu likitan da ya yi mata wancan aika-aika, yana neman ta biya shi cikon kudin aikin da ya yanke mata hanji, cewa kuskuren da aka samu ba wani abu ba ne.

Likitan ya tura wa mijinta sako cewa, “Kar ka manta, har yanzu ina bin ku cikon N200,000 na tiyatar da na yi ta biyu da kudin gwaji da na karin jini da ba ku biya ba. Na bari kun tafi ba tare da na nemi ku biya cikon kudin ba ne saboda ina so matarka ta samu lafiya tukuna.”

Likitan ya ci gaba da cewa, “Ka sani cewa ni kwararren likitane, kuma na yi aikin tiyata sama da 500, sama da kashi 99 cikin 100 daga cikinsu, sun yi nasara.”

Ya ce, “Da a asibitin gwamnati ne irin hakan ta faru, za ka iya yi min wata barazana? Kada ku bari a yaudare ku, a can [asibitin] Gwagwaladan da kuka je ma hakan za ta iya kasancewa.”

Sakacin likitoci

Marasa lafiya dai kan je asibiti ne domin samun kulawa da magani daga lalurar da ke damun su; Inda mutane da dama kan yi duk mai yiwuwa wajen bin duk abin da likitoci suka ce su yi, sau da kafa, kama daga shan magunguna, wankin rauni, yin gwaji da sauransu.

Amma duk da hakan, ita wannan matar, zuwanta asibiti ne ya bar baya da kura, domin likita ne da kansa ya yi mata aika-aika bisa kuskure, sai daga baya ita da mijinta suka ga bayan gida yana fitowa daga al’aurarta da kuma wurin da aka yi mata dinki bayan an yi aikin.

Mutane da dama irin Misis Iren Emmanuel, da suka je asibiti domin samun kulawa sun sha a wayi gari sun rasa rayukansu, ko kuma a kara jefa su cikin matsalar da ta fi wadda ta kawo su asibitin, a sakamakon ‘sacaki ko kuskuren’ likitoci ko malaman jinya.

Irin wadannan matsalolin sun hada da yin gwaji ba daidai ba, bayar da maganin da bai dace ba, sallamar mara lafiya lokacin da bai dace ba, ji wa mara lafiya rauni a wurin tiyata, mantawa da kayan aiki a cijin jikin mara lafiya, da sauransu.

A duk lokacin da aka samu irin wadannan matsalolin, sukan jefa ba ma mara lafiya kawai ba, hatta iyalansa da abokan arziki cikin tashin hankali, wani lokaci ma har ta kai ga asarar rayuka, bayan  kashe makudan kudade da kuma matsananciyar wahalar da suke sha, sai wanda ya gani.

Yadda likita ya yanke min hanji

Matar ta bayyana wa Aminiya yadda ta tsallake rijiya da baya a hannun irin wadannan likitoci, bayan an yi mata tiyatar haihuwa a wani asibitin kudi a Abuja.

Misis Irene Emmanuel ta ce, “Abin ya faru ne a ranar 5 ga watan Nuwamban bara 2021 lokacin za a yi min aikin tiyatar haihuwa na uku.

“Nakan yi awo ne a Asitin Kula da Lafiya a Matakin Farko, idan lokacin haihuwata ya zo kuma sai su tura ni zuwa babban asibiti domin a yi min aiki — Abin da kuma ya faru ke nan, da ma kuma suna yajin aiki.

“Amma da na je babban asibitin sai suka ce babu gadon da za su karbe ni, masu cikin da suka yi awo a wurinsu ma maneji suke yi, in koma zuwa asibitin da ya turo ni wurinsu.

“Daga nan sai na koma cibiyar kula da lafiyar na shaida wa likitan cewa babban asibitin sun ki su karbe ni, ba su da gado.

“Sai ya ce kada mu damu, akwai wani likita kwararre a wani asibitin kudi da ya sani, zai yi min aikin yadda ya kamata.

“Har mijina ya tambaye shi ko ya san tarihin wancan likitan, ya ce ai ya san shi kuma ya sha yin aikin tiyata kuma cikin nasara, saboda haka zai gayyato shi ya zo.

“Da wancan likitan ya zo shi ne ya dauke mu zuwa asibitinshi, bayan mun je an gama komai sai aka shigar da ni dakin tiyata, aka yi aikin lafiya har na fito.

“Daga baya sai na ji ba na jin dadin jikina, ina jin radadi su kuma suna ta fadi-tashin ganin yadda zan rika samu ina yin tusa, amma ba na iya yin ko da tusar ballantana bayan gida.

“A rana ta shida sai likitan ya ce za a yi min tawa tiyatar domin a fito da hanjina a wanke; Aka sake shigar da ni dakin tiyata.

“Washegari, bayan da aka yi tiyatar sai bayan gida ya fara fitowa a jikina, ta al’aurata da kuma wurin da aka yi aikin, babu kakkautawa.

“Washegari ya sa mijina ya sayo min nafkin din manya, na fara amfani da shi, sai da muka yi amfani da kusan fakiti uku a asibitinsa.

“Kullum jikina sai kara rauni yake ta yi, ba na iya yin magana ko wani abu, duk wanda ya zo duba ni, sai dai in bi shi da kallo, ko magana ba na iyawa.

“Daga baya likitan ya ce mana abin yana neman fin karfinsa, sai ya tura mu zuwa Asibitin Kwararru na Gwagwalada.

“Da muka je can din ma sa’a muka ci, da taimakon Allah, saboda ko’ina a cike yake. Ina cikin mota, mijina ne ke ta kai-komo domin mu samu ganin likita.

“Suka ce wa mijina cewa ba su da wurin da za su ajiye mu, amma ya ce musu matsalarmu ta gaggawa ce, matarsa ce, ko numfashi ba ta iya yi.

“Da suka zo suka ga jaririna, suka tambaya ina uwarsa? Aka ce musu ai ni ce. Shi ne likitan ya ce, ‘Ai jaririn ya yi kankanta sosai, bai kamata a bari mutuwa ta raba shi da mahaifiyarsa ba, bari mu ga yadda za a yi.’

“Sai ya shiga ciki, bayan dan lokaci sai aka zo aka shigar da ni, likitoci suka ce washegari da safe za su yi min tiyatar gaggawa.

“Bayan sun yi min aikin washegari, sai suka samu maigidana suka ce masa, ‘Matarka ta auna arziki — abin da muka gani a jikinta a dakin tiyata na da matukar tayar da hankali — wane irin likita ne ma zai yi irin wannan kuskuren, ya yanke mata hanji a bisa kuskure.’

“Suka ce ikon Allah ne ma da har yanzu nake raye, abin da kawai za a iya shi ne a fitar da hanjin nawa ya dawo waje, amma idan har aka sake jona su, to ba zan rayu ba.

“Suka ce hanjin nawa zai ci gaba da kasancewa a waje na tsawon wata shida, kafin a mayar da shi.

“Muka ce ta yaya za mu rika kula da hanji haka na tsawon wata shida? Suka ce mana jakar bayan gida ta hanji za mu rika saya ana amfani da ita, wadda muke sayen daya a kan N18,000 a kowane mako.

“Wani lokacin ma guda biyu muke saye a mako saboda abin yakan fita daga jikina, sai an canza shi,” inji Irene.