✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda ma’aikatun gwamnati ke watsi da ’yan Najeriya

Sai ’yan Najeriya sun yi jibin goshi hukumomi ke ba su bayanan ayyukansu.

Wani bincike da aka gudanar ya gano yadda wasu ma’aikatu da hukumomin gwamnati a Najeriya ke watsi da dokokin da suka wajabta musu gabatar wa ’yan kasa bayanan ayyukan da suke gudanarwa.

Binciken, wanda wata cibiya mai nazari kan yaki da cin hanci da tabbatar da daidaito (FTIW) ta gudanar ya ce Asusun Tallafa wa Iyali na Kasa ne ya yi zarra wurin samar da irin wadannan bayanan, amma duk da hakan makin da asusun bai wuce kashi 34.92 cikin 100 ba.

Bayan shi sai wasu ma’aikatun Gwamnatin Tarayya guda tara da ke bi masa da kashi 33.37 cikin 100.

Da yake gabatar da rahoton, shugaban cibiyar, Umar Yakubu, ya ce sun gudanar da binciken ne a ma’aikatu da hukumomin Gwamnatin Tarayya da jihohi 36 da kuma kananan hukumomi 774 da ke fadin Najeriya.

A cewarsa, abun da suka gani a zahiri shi ne akwai koma baya matuka wurin amfani da tsari ba wa ’yan kasa bayanan ayyukan da hukumomin gwamanti suke gudanarwa.

A jihohi Najeriya kuwa, Jihar Kaduna ita ce ta farko wurin bin tsarin tsarin da kashi 76.67 cikin 100, sai Jihar Ekiti a mataki na biyu da maki 73.33  sannan Jihar Kwara a matsayi na uku da maki 65 cikin 100.

Binciken ya nuna jihohin Neja da Sakkwato da kuma Zamfara su ne a can karshen jadawalin bin tsarin.

Umar Yakubu ya ce, binciken ya nuna ma’aikatun kula da harkokin kudade na gwamnatin tarayya ne kan gaba da kashi 21.87 cikin 100 sai bangaren man fetur da iskar gas da kashi 18.48 cikin 100.

Da ya ke jawabi a wurin kaddamar da rahoton, tsohon Shugaban Hukumar EFCC, Malam Nuhu Ribado, ya ce  tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya yi abun da ya kamata a bangaren yaki da rashawa tsakanin ma’aikatan gwamnati ta hanyar samar da wasu muhimman matakai da za su taimaka wurin kaiwa ga nasara.

Ribado ya yaba da kokarin cibiyar CeFTIW saboda shirya taron da samar da nagartattun hanyoyin magance matsalolin rashawa a Najeriya gami da wayar da kan ’yan kasa don sanin yadda ake tafiyar da al’amuran gwamnati.

Ya kuma yi fatan cibiyar za ta ci gaba da jajircewa kan wannan aiki har a kai ga fitar da jaki daga duma.