✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mace mai kiba za ta yi kwalliya

Yadda mace mai kiba za ta yi kwalliya daban take da yadda mace marar kiba take yi.

Barkanmu da sake haduwa da ku a wannan filin namu na Kwalliya. Mata da dama ba su san irin kwalliyar da ta dace da fuskarsu ba.

Ina so in jawo hankalinku domin gane cewa, yadda mace mai kiba za ta yi kwalliya daban take da yadda mace marar kiba take kwalliya.

Don haka ne a yau na kawo muku hanyoyi da dama da za a bi domin yin kwalliya ga mace mai kiba.

  • Hodar ‘concealer’: A samu nau’in da ya fi hodar fandesho haske kafin a shafa. Za a iya amfani da irin wannan hodar a saman fatar ido da wajen fatar baki kusa da lebba yadda za ta bayyano da tsarin lebbar.
  • Hodar fandesho: A samu soson hoda wajen shafawa a fuska, sannan a shafa shi a ko’ina yadda duk fuskar za ta samu.
  • Hoda: A samu hodar da ta dace da fatar mace kuma za a iya yin wannan gwajin wajen shafawa a fatar hannu. Idan an samu wadda ta dace, sannan a shafa a fuska. Yana da kyau idan an zo shafa wannan hodar a rika shafa ta yadda zai ta dan taba gashin kai kadan, kamar inci biyu yadda za ta kame fuskar sosai.
  • Bronze: Za a iya shafa wannan hodar a gefen kumatu kadan ba ta yadda za ta bayyana ba.
  • Gira: A tabbata an cika girar da gazal wajen shafa shi yin hakan na kara bayyana kyaun gira.
  • Hodar ‘blush’: Yana da kyau a shafa hodar ‘blush’ a kan kashin kumatu domin ramar da kumatun.
  • Kada a manta idan an tashi shafa hoda a mayar da hankali a wajen da rana ke yawan daka, kamar goshi da kumatu.
  • Man baki: Idan mace ta kasance mai kiba, yana da kyau ta rika shafa man baki da ya dace da lebbanta hakan yakan kara mata kyau kuma zai boye kibar fuskar da ta kumatu.
  • Yana daukar akalla minti 10 ko 15 wajen yin irin wannan kwalliyar don haka nake ba da shawara cewa, ba a kullum za a yi irin wannan kwalliyar ba, sai lokaci-lokaci.