✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda mafarauci ya kashe makiyayi a Ogun, ya birne shi a daji

Mafaraucin ya kashe Bafulatanin sannan ya birne gawarsa a daji.

Rundunar ’yan sandan Jihar Ogun, ta ce ta kama wani mafarauci bisa zarginsa da kisan wani makiyayi a Karamar Hukumar Ewekoro sannan ya birne gawar a gonarsa.

Kwamishinan ’yan sandan Jihar, Lanre Bankole, ne ya bayyana hakan ne a lokacin da ya gabatar da wanda ake zargin tare da wasu mutum 14 da aka kama da laifin satar mutane da kuma fashi da makami a hedikwatar rundunar da ke Abeokuta.

A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne a ranar 13 ga Maris, bisa laifin kashe wani Bafulatani makiyayi.

Ya bayyana cewa mafaraucin, bayan ya kashe makiyayin, ya ​​birne shi a gonarsa da ke Ewekoro.

Mafaraucin dai ya amsa cewa ya harbe Bafulatanin har lahira sannan ya birne gawar shi a daji.

Sai dai Kwamishinan ya ce an tono gawar makiyayin kuma an kai ta babban asibitin Ifo domin gudanar da bincike.