✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mahara suka ci karensu babu babbaka a Katsina

'Yan bindiga sun yi ta harbe-harbe, suka yi awanni suna yin fashi suka kuma sace mutum 17

‘Yan bindiga sun kashe mutum biyu suka yi garkuwa da mutum 17 tare da sace dabbobi masu yawa a wasu hare-hare a Jihar Katsina.

Maharan sun harbe mutum biyu a kauyen Kandawa da ke karamar Hukumar Batsari a ranar Laraba.

‘Yan garin sun kai gawar mamatan gidan Mai Garin, wanda ya ba su hakuri da cewa su dauki hakan a matsayin kaddara.

Ya kuma yi musu akawarin neman dauki daga jami’an tsaro domin magance matsalar.

Gabanin nan mahara sun sace mutum 17 cikinsu har da yarinya mai wata biyar da kuma dabbobi a Karamar Hukumar Dagana.

‘Yan bindigar sun kutsa cikin garin ne da talatainin daren Lahadi, suna ta harbe-harbe sannan suka yi awanni suna cin karensu babu babbaka.

“Sun kwashe shanu da dama da tumaki sannan suka shiga gida-gida suna kwatar dukiyar mutane kafin su tafi da mata da ‘yan mata 17”, wani dan garin ya shaida wa BBC.

Sai dai ya ce daga baya ‘yan fashin sun dawo da wata yarinya ‘yar wata biyar da haihuwa da kuma hudu daga cikin matan da suka dauka.

Ko a bara, ‘yan fashin daji sun kai hari a garin na Zakka da ke jihar Katsina da baya-bayan nan aka fi samu hare-haren ‘yan bindiga.

Rundunar’Yan Sandan Jihar Katsina ta tabbatar da faruwar lamarin sai dai ta ce mutum tara ne suka rage ba a gani.

Kakakin rundunar, ASP Gambo Isa ya ce jami’an tsaro da hadin gwiwar tubabbun ‘yan bindiga sun yi nasarar ceto wasu daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su.