✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda mahara suka kashe mutane a Katsina da Taraba, suka sace 36 a Kaduna

’Yan bindiga sun hallaka mutum uku da sace wasu ’yan mata biyar, hadi da shugaban jami’an tsaron sa-kai a Jalingo, jihar Taraba. Lamarin ya faru…

’Yan bindiga sun hallaka mutum uku da sace wasu ’yan mata biyar, hadi da shugaban jami’an tsaron sa-kai a Jalingo, jihar Taraba.

Lamarin ya faru ne a ranakun Asabar da Litinin a sassan kwaryar birnin jihar.

Aminiya ta gano ’yan bindigar sun kashe wani dan sanda da wani farar hula , sannan suka sace jami’in tsaron sa-kan mai suna Bashir tare da wasu mata biyar ne a shataletalen Saminaka da misalin karfe 1.30 na dare ranar Litinin, suka kuma kashe wani dan sanda da wani farar hula a unguwannin Lasandi, da BabaYau da kuma Sabongari.

Kafin su samu sace jami’in sa-kan, ’yan bindigar sun shiga unguwar a kan babura inda suka bude wuta kan mai uwa da wabi.

Unguwar dai na kusa da Dajin Kwando da ke Karamar Hukumar Ardo-Kola inda aka sace mutane 20, yayin da aka kashe mutane hudu ciki har da shugaban karamar hukumar ba da jimawa ba.

Mazauna yankin dai sun sanar da Aminiya halin firgicin da su ke ciki sakamakon rashin sanin ta ina da kuma lokacin da za a kawo musu hari.

“A tsorace muke saboda hare-haren `yan Bindiga sun fara yawa a yankinmu, rashin tabbasa ya sanya da ido daya muke bacci”, in ji wani mai suna Musa Garba da ke zaune a yankin.

Duk yunkurin da muka yi domin ji ta bakin kakakin rundunar ’yan sanda jihar, Usman Abdullahi ya ci tura.

Harin Katsina

A wani labarin mai kama da wannan a Jihar Katsina, a daren ranar Litinin din ne ’yan bindiga sun hallaka mutum uku a wasu kauyukan Karamar Hukumar Funtuwa.

Kauyukan dai sun hada da Yartafki da suka kai wa hari da karfe 11:00 na dare suka sace Shugaban Makarantar Gwamnatin Makera, Malam Bala Magaji.

Guda daga ’yan uwan shugaban makarantar ya ce daga nan ne suka afka wa kauyen Unguwar Isiyaka da karfe 11:15 na dare, suna harbe-harbe har suka samu kashe mutum uku.

“Hare-haren dai sun faru ne a wuarare daban-daban a lokaci guda inda aka kashe mutum uku, aka sace takwas, ciki har da mai unguwa”, in ji dan uwan shugaban makarantar.

Harin Kaduna

A jihar Kaduna ma mutane 36 ’yan bindigar suka sace a unguwar Keke B da ke Karamar Hukumar Chikun, da dare ranar Litinin.

Wani da abin ya faru kan idonsa mai suna Muhammad Salihu ya bayyana mana cewa gida-gida suka dinga shiga suna diban mutane.

“Karfe 8:30 na dare lamarin ya faru, kuma da yawansu suka zo suka fara harbe-harbe har suka sace mutane 38 da fari, amma sai wasu biyu suka tsere dag baya”, in ji shi.

Ya zuwa yanzu dai mahukunta ba su ce komai ba kan lamarin, kuma yunkurinmu na jin ta bakin kakakin runudunar ’yan sandan jihar, Muhammad Jalige ya ci tura.

 

Daga Magaji Hunkuyi, Jalingo da Maryam Ahmadu-Suka, Kaduna da Tijjani Ibrahim da Mahmoud Idris, Katsina da Rahima Shehu Dokaji