Daily Trust Aminiya - Yadda mahari ya hallaka mutum 5 da kibiya a Norway

Kwari da baka

Yadda mahari ya hallaka mutum 5 da kibiya a Norway

Wani dan asalin kasar Denmark ya hallaka akalla mutum biyar a wani hari da ya kai da ki kibiya kan mutanen ba su ji ba, ba su gani ba a wani kauyen kasar Norway.

Shagaban ’Yan Sandan kasar, Ole B. Saeverud, ya shaida wa wani taron manema labarai ranar Alhamis cewa tun gabanin harin dama ana fargabar cewa mutumin ya na da tsattsauran ra’ayi.

Harin dai wanda har yanzu ba a san makasudin kai shi ba an kai shi ne ranar Laraba da yamma a kauyen Kongsberg, mai nisan kilomita 68, Kudu maso Yammacin Oslo, babban birnin kasar.

An sami nasarar kama maharin ne mintuna 20 da fara harin, wanda ’yan sanda suka ce shi kadai ne ya kai shi.

’Yan sandan dai sun ce wanda ake zargin dai ya rika zagaya garin yana harbin kan mai uwa da wabi da kibiya.

Sun ce za su binciki ko dai harin na da alaka da ta’addanci ko kuma a’a.

Wani babban jami’in dan sanda, Oyvind Aas ya ce, “La’akari da yadda abubuwa ke faruwa, ba abin mamaki ba ne in an yi zargin cewa ko na ta’addanci ne.

“Mun kama mutumin kuma muna yi masa tambayoyi, amma ya yi wuri yanzu a ce ga dalilinsa na kai harin,” inji shi.

Firaministan kasar, Erna Solberg, ya bayyana rahotannin harin a matsayin masu sosa rai.

An kai harin ne a tsakiyar garin na Kongsberg, wanda yake da mutane kusan N28,000.

’Yan sanda sun kuma ce an kai harin ne da wajen misalin karfe 6:30 na kasar, kuma yanzu haka maharin yana can an tsare shi a wani ofishinsu da ke wani garin Drammen da ke kusa da Kongsberg din.

Karin Labarai