✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda malaman Birnin Gwari suka tsere daga hannun ’yan bindiga

Sai dai biyu daga cikinsu sun yi rashin sa'ar fadawa a hannun wasu ’yan bindiga kuuma

Malamai uku na makarantar firamare da ke Rama a Birnin Gwari, Jihar Kaduna sun tsere daga hannun ’yan bindiga da suka yi garkuwa da su.

Daya daga cikin malaman ya ce shi ne ya fara tserewa bayan ya yaudari mai gadin da ’yan bindigar suka bari tsaron mutanen aka yi garkuwa da su.

A watan Maris, Aminiya ta kawo rahoton yadda ’yan bindiga suka auka wa makantar suka tafi da malamai uku da dalibai uku.

Daga baya malaman makarantar sun shaida wa wakilinmu cewa yaran sun tsere sun dawo gida, amma malaman na hannun ’yan bindigar.

Malaman da aka sace din suna koyarwa ne a aji daya, aji biyu da kuma aji shida; kuma masu garkuwar na neman kudin fansa Naira miliyan biyar.

Malamin aji shidan da ya kubuta ba tare da biyan kudin fansa ba, ya ce ya yi hakan ne bayan da ’yan bindigar sun tafi domin su kai waji hari, sauran mutum biyun da aka bar wa tsaron su kuma, dayan ya tafi wanka a kududdufi da bindigar da ta rage a hannunsu.

Malam Rabiu ya ce: “Da na ga shi kadai ne kuma babu makami a hannunsa sai na ce masa zan yi ba-haya, daga can sai dai kawai ya hange ni ina ta gudu. Na lura su ma abokan aikina sun tsere da sansanin ’yan bindigar.”

Sai dai ya ce daga baya abokan aikin nasa sun rashin sa’ar fadawa a hannun gungun wasu ’yan bindiga wadanda a halin yanzu suke neman kudin fansa Naira dubu dari bakwai da hamsin a kan kowannensu.

A halin yanzu dai malam Rabiu na asibiti ana jinyar sa.