✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda manoman shinkafa suka yi asarar Naira biliyan 1

Ambaliyar ruwa ta shafe amfanin gona na biliyoyin Naira a Jihar Kebbi

Shinkafa da sauran amfanin gona da aka kiyasta kudinsu ya kai Naira biliyan daya suke salwanta sakamakon ambaliyar ruwa a sassa daban-daban na Jihar Kebbi.

Kwamishinan Aikin Gona na jihar Attahiru Maccido ne ya bayyana hakan ranar Lahadi yayin wata ziyarar gani da ido da ya kai yankunan da lamarin ya shafa a kananan hukumomin Bagudo da Argungu.

“A Karamar Hukumar Bagudo, mun ziyarci kauyuka kusan 19 wadanda ambaliyar ta yi wa barna, mun kuma ziyarci al’ummomi da dama a Karamar Hukumar Argungu.

“Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta gina mana madatsar ruwa; ina ganin a jihohin da ke kan gaba a harkar noma, Kebbi ce kawai ba ta da madatsar ruwa ta kanta”, inji kwamishinan.

Maccido ya kara da cewa gina madatsar ruwa zai taimaka wajen takaita ambaliya sannan ya karfafa gwiwa wajen amfani da albarkatun ruwa ta hanayar da ta dace a jihar.

Maslaha ta dindindin

Ya kuma ce ambaliyar ruwan ta shafe dubban hektoci na gonaki da gidaje, sannan ta lalata amfanin gona da kayayyakin jama’a a wuraren da lamarin ya shafa.

Yadda ruwa ya mamaye gonaki da gidaje a Karamar Hukumar Bagudo ta Jihar Kebbi

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato Alhaji Attahiru Maccido yana cewa, “Bincike na farko-farko ya nuna cewa amfanin gonar da ambaliyar ta salwantar zai kai na biliyoyin Naira.

“Biyan diyya wata hanya ce ta saukaka radadin asarar, amma muna neman mafita ce ta dindindin ga matsalar mummunar ambaliyar ruwa”.

A cewarsa, Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Jihar Kebbi za ta rarraba abinci da sauran kayan agaji ga manoma da sauran mutanen da abin ya shafa don saukaka masu radadin asarar da suka yi.

Ya kuma yi kira ga mawadata da kamfanonin sarrafa kayan amfanin gona da ke jihar da su tallafa wa manoman da lamarin ya shafa.

Kunnen uwar shegu

A cewar Shugaban Karamar Hukumar Bagudo Muhammadu Kaura, ambaliyar ruwan ta wanke gonakin dawa, da gero, da masara, da shinkafa a yankin.

Wasu daga cikin gonakin da ruwa ya mamaye a Karamar Hukumar Argungu ta Jihar Kebbi

Ya kuma nuna takaici da yadda mazauna yankunan da ke fuskantar barazana suka ki yin kaura su koma wasu yankunan duk da gargadin da hukumomi suka yi, yana mai cewa karamar hukumar za ta bayar da fifiko wajen wayar da kan al’umma game da hadarin ambaliya.

Shi ma da yake tofa albarkacin bakinsa, Mai Unguwar Tunga, daya daga cikin wuraren da lamarin ya shafa, ya ce ruwan ya mamaye al’ummomi da dama da ke karkashin kulawarsa.

Ya kuma nuna damuwa cewa ambaliyar za ta yi mummunan tasiri a kan noman shinkafa a yankin.

Har da dabbobi

Wasu daga cikin manoman da abin ya shafa sun bayyana kaduwarsu da faruwar lamarin.

A cewar Abubakar Maikifi, ambaliyar ta haddasa masu gagarumar asara, ta kuma lalata hanya daya da suke da ita ta samun abin sakawa a bakin salati.

“Ambaliyar ta salwantar mana da amfanin gona da dabbobi.

“Wasu daga cikin manoma a wannan yankin kan noma hekta 50 zuwa 100 ta shinkafa duk shekara.

“Ba mu taba ganin irin wannan bala’i ba; muna kira ga gwamnati ta agaza mana”, inji shi.

NAN ya ruwaito cewa yankunan da ambaliyar ta shafa sun hada da Tungar-Baushe, da Illela, da Buda, da Rimi, da Kurgu, da Tungar-Sha, da Shanbam, da Bargawa, da Garin-Wanzam, da Tungar-Wanzam, da Sabon-Gari da kuma Tungar-Nabayi.

Sauran su ne Tungar-Burtu, da Tungar-Akoda, da Tilleji, da Kala-Kala, da Tungar-Arabi, da Tungar Ayuba da Gefen Farfajiya da kuma Gandun Sarki.