✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda masoya suka tarbi Sanusi II a Kaduna

Ziyarar Sanusi II ta farko ke nan tun bayan komawarsa Legas da zama

Tsohon Sarkin Kano, Muhammadu Sanusi II, na ziyarar aiki a Kaduna, inda ya gana da Gwamna Nasiru El-Rufai.

Ziyarar tsohon Gwamnan Babban Bankin Najeriyan (CBN) na farko ke nan tun bayan komawarsa Legas da zaman bayan sauke shi daga karagar Sarkin Kano.

Saukar jirginsa ke da wuya, manyan jami’an Gwamnatin Jihar Kaduna suka tarbe shi kafin wucewa zuwa gidan Gwamanin Jihar.

Ya bayyana godiya ga El-Rufai bisa goyon bayan da ya ba shi a matsayin aboki sannan ya ba wa Gwamnan tabbacin zai yi bakin kokarinsa a kan amanar da ya ba shi.

Ba a jima ba da sauke shi ba, El-Rufai ya shi Shugaban Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) kuma Mataimakin Shugaban Hukumar Zuba Jari ta jihar (KADIPA).

— Murnar ziyarar Sanusi II

Dubban masoya da masu rike da sarauta daga Jihar Kano sun yi tururuwa a garin Kaduna domin tarbar sa.

An yi ta sanya wakokin yabon Sanusi, wanda ya je ganawa da abokinsa, Gwamna El-Rufai.

Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya karbi bakuncin Muhammadu Sanusi II

A ranar 9 ga watan Maris, 2020 Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje ya sauke Sanusi daga Sarautar Kano, wanda ya hau a ranar 8 ga Yuni, 2018 bayan rasuwar Sarkin Kano na 13, marigayi Alhaji Ado Bayero.

— Kusancin Sanusi II da El-Rufai

Bayan sauke shi bisa zargin rashin biyayya, an tsare Sanusi a Jihar Nasarawa kafin daga baya Kotun Daukaka Kara ta Tarayya ta yi ta ba da umarnin sakinsa.

Ba a jima ba, El-Rufai ya ba shi mukamai biyu a Gwamnatin Jihar Kaduna.

Gwamnan na daga cikin mutanen da suka fara ziyartar Sanusi bayan Ganduje ya sauke shi aka kuma tsare shi, har suka yi sallar Juma’a tare a garin Awe.

Bayan nan ne El-Rufai da Sanusi suka dawo Abuja tare inda tsohon sarkin ya hau jirgi zuwa Legas.

Alhaji Aminu Ado Bayero shi ne ya maye gurbin Sanusi, wanda ya gaji Mahaifinsa, Sarki Ado Bayero da ya rasu bayan shekara fiye da 50 yana Sarkin Kano.