✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mata ta haihu a kan hanya a Zariya

Wata mata da ake zato mara lafiya ce ta haihu a wani rusasshen kango da ke gefen hanya a Zariya. Wani likita da ke hanyarsa…

Wata mata da ake zato mara lafiya ce ta haihu a wani rusasshen kango da ke gefen hanya a Zariya.

Wani likita da ke hanyarsa ta zuwa Samaru, Dokta Mustapha Muhammad ne ya ba wa mai jegon wadda ba a san daga inda ta fito ba kulawar gaggawa.

“Matar ta haihu lafiya sai dai mahaifarta ba ta fita ba kuma ka san tunda ba yadda ta iya don haka sai ta dauki dan ta rungume, ka ji yadda aka yi, amma yanzu Allah Ya sa mahaifar ta fita kuma na yanke cibiyar”, inji shi.

Kangon da matar ta haihu na daura da ofishin Hukumar Kula da Kiyaye Handura ta Kasa (FRSC) a titin da ya tashi daga PZ zuwa Samaru, Karamar Hukumar Sabon Gari, Jihar Kaduna.

Daga baya Jami’an FRSC sun dauki matar a motarsu zuwa Sashen Kula da Walwala da Jin Dadi na karamar hukumar domin ci gaba da lura da ita.