✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda matan Kano ke gogayya da maza a harkar kwallon kafa

Buga kwallo, ko bibiyarsa abu ne da a Najeriya ake alakantawa da maza; Yawanci idan aka ji ana tada na tada jijiyoyin wuya a taron…

Buga kwallo, ko bibiyarsa abu ne da a Najeriya ake alakantawa da maza; Yawanci idan aka ji ana tada na tada jijiyoyin wuya a taron maza, dayan abu biyu ne, idan ba siyasa ake zance ko ba to kwallo wa — da wuya a samu mace.

Sau da dama wannan lamari na ci wa mata da dama tuwo a kwarya kasancewar ba su ga abin so a kwallon kafar da maza ke zuzutawa ba.

Hakan ya sanya har matsala hakan ke kawo wa wasu matan da mazajensu, domin da dama mata, musamman a Arewacin Najeriya sun fi karfi a kallon fina-finan Indiya da na Hausa, abin da su kuma mazan ke wa kallon bata lokaci.

Akan samu a mata na taruwa a kafofin sada zumunta suna tattauna wannan dabi’a ta maza da ke bata musu rai, suna kuma mamakin yadda dabi’ar ta zamo bai daya ba manya ba yara, a tsakanin yawancin maza.

Yadda mata ke gogayya da maza

To amma sai ga shi a hankali, ta fara bayyana cewa akwai matan da su ma ke gogayya da maza a fannin sharhi da bibiyar harkar kwalon kafar.

Zainab Naseer Ahmad da Nadiya Ibrahim Fagge, matasan mata ne da ke gugar kafada da maza wajen tsefe tufkar kwallon kafa, musamman na kungiyoyin da suke goyon baya.

Hakan ya sanya kowaccensu ke da dimbin magoya baya a Facebook da ke tsokano su duk lokacin da ake taka leda da kulob dinsu, aka samu nasara ko akasinta.

Zainab Nasir Ahmad

Zainab Nasir Ahmad mai goyon bayan kungiyar Arenala ce, ta kuma ce ta fara kallon kwallon kafa ne tun ta na karama, lokacin kalar kayan dan kwallo kawai take gani, idan burge ta, ta ce shi take so ya samu nasara a wasan.

“Na taso tsakanin yayyena da kannena maza muna kallo, to su suka ja ra’ayina har na fara fahimtar ta sosai ta shiga raina.

“Kuma sai na ga Arsenal ta fi burge ni, lokacin ma ana kiransu da O2 ne, kuma dan wasan Najeriya, Kanu Nwonko, na buga wasa a kulob din, kasancewar yana birge ni saboda dan kasata ne, sannan ga Jersey dinsu ya sa na fara son su sosai da sosai”, in ji ta.

Ta ci gaba da cewa, “Lokacin suna ma dan cin kwallon har suna zuwa Champions League, ba irin yanzu ba.

“Amma ni duk da haka a yanzun ma ina son su haka, domin duk da haka muna kokartawa, kuma matsaloli ne da za mu gyara, don kowane kulob da matsalar da yake fama da ita.

“Har Madrid din ma sukan shiga irin wannan yanayin da ba sa kokari, wani lokacin kuma su taso suna yi ”.

Zainab Naseer Ahmad
Zainab Naseer Ahmad

Nadiya Ibrahim Fagge

A nata bangaren, Nadiya Ibrahim Fagge da ke goyon bayan ’Yan Madara wato Kungiyar Kwallon kafa ta Real Madrid, ta ce soyayyarta da kwallon kafa ta samo asali ne tun kuruciya.

Ta ce A lokacin, mahifinsu kan zo ya samu suna kallo, shi kuma ya sauya tasha zuwa wacce ake buga kwallon, sai kowa zai watse.

Amma ita saboda soyyayrta da tabaijin sai ita ta zauna ta ci gaba da kallo a haka, daga nan ne kuma ta shiga ranta har ta fara fahimta, ta fi son masu sanya fararen kaya.

“Wani abin kuma shi ne da yake gidanmu akwai maza, duk lokacin da ake buga wani wasan, ba mu da janareto a lokacin.

“Amma a wani shagon mai hoto da ke kasan gidanmu akwai, babanmu saboda ba ya so mazan su dinga zuwa gidan kallo, sai ya sa aka siyo doguwar waya, aka jono ta daga benenmu zuwa shagon.

“Sai ya siya mai a zuba a injin, mu dinga kallon ta haka, kuma ni kadai ce mace a cikinsu, duk haka ake taruwa har da samarin unguwa a yi ta yi”, in ji ta.

Ta ce “Daga nan na zabi kasar Spain a matsayin wacce nake goyon baya, daga Spain kuma, na zabi kungiyar Kwallon Kafa ta Real Madrid, saboda iya taka ledarsu.

“Salon takun ’yan kwallonsu na wancan lokacin irinsu Zidane da Raul da Ronaldo na kasar Brazil ya sa na fara kaunar su ba kadan ba”.

Kallon da ake musu kan kwallon kafa

Zainab Naseer ta ce, “Mutane na mamaki sosai idan suka ji ina maganar kwallon kafa mai zurfi, sai abin ya birge su, har su dinga tambayar ya aka yi na san wadannan abubuwan?

“Wasu kuma lokacin za su fara min kallon wata bambarakwai, saboda a ganinsu sabgar ta maza ce ba mata ba, duk da ni ban ga dalilin da zai sanya a ce na maza ba ne tunda harkar nishadi ce”.

Ita kuma Nadiya, cewa ta yi, “Na samu kalubale gaskiya, domin ba na mantawa akwai lokacin da na je Kofar Mata Stadium, Kano Pillars za su buga kwallo, na je ne ma a matsayin ma’aikaciya, amma da irin kayan Kano Pillars din, to kafin na bar stadium har an dauki hotona an tura wa mahaifina.

“Duk da tare da shi muke kallon Kwallon, amma saboda yanayin Al’adarmu da kuma mutanen banza aka fi gani a wurare irin haka, ya sanya mahaifina ya yi min fada sosai a lokacin.

“A wannan lokacin sai na ji kamar na daina kallon kwallon kafar har abada, to amma shi mahaifin nawa ko fita ya yi ya dawo zai tambaye ni kina kallon wasa kaza kuwa? Yanzun nan aka yi kaza, har ma na dawo na manta waccan maganar.

“Saboda shi dan Barcelona ne, ni ’yar Madrid ce, don haka a takaice dai wasu muna burge su, wasu kuma suna mana kallon bambarakwai, don wani idan ya yabo miki wata maganar kan kalllon kwallon kafa, sai kin ji kamar ki yi kuka,” in ji Nadiya.

Dangane da ko akwai mata da ke zaman hirar kwallon kafa da su sosai kuwa, sun bayyana cewa akwai, sai dai ba su kai yawan maza ba.

Amma kasancewar akwai kafafen sada zumunta, musamman Facebook da suka fi magoya baya, suna jin dadin a yi kwallo domin za su tarar da tarin sakonni daga ’yan adawa da masoya da za a tsokani juna a yi wasa da dariya sosai.

Gasar da suka fi Kallo

Zainab ta  bayyan cewa a duk gasar kwallon kafar da ake bugawa a duniya, ta fi so da kallon Firimiyar Ingila, da kuma duk wani wasa da Najeriya za ta buga, sai kuma Gasar Zakarun Turai.

Ta ce duk da cewa kungiyarsu ta Arsenal ta yi shekaru ba ta fito ba, amma duk da haka tana kallo, sai kuma Europa da Laliga da Serie A, da ‘league’ da dama, domin har na ’yan Scotland tana kallo.

“Kinga ko a Spain ina son Barcelona kadan, amma bana son Madrid don adawa na ke da su, amma baya hana ni kallon wasansu. Amma dai kankat shi ne English Premier League, musamman a ce a ranakun karshen mako ake yi.

Nadiya kuwa cewa ta yi ta fi kallon na nahiyarsu wato Laliga, sai Gasar Zakarun Turai da na Nahiyar Afirka, saboda acewarta, suna yin kwallo da gaske, domin tana kashe awa biyu tana kallon kwallo.

Shawarwarinsu kan matsalolin Kulob dinsu

“Ni kin ga a Arsenal matsalarmu ita ce zaben wadanda ba su kamata ba a kwallo.

“Misali akwai ’yan wasan da ya kamata a ce su suke buga mana manyan wasanni, amma ba a saka su, sai kuma yanayin canjin da ake mana.

“Ni ina ganin matsala ce daga shugabanninmu kuma ya kamata a sayo mana sababbin ’yan wasa tunda mu kulob din duniya ne da aka san mu, bai kamata a ce muna baya ba gaskiya”, in ji Zainab.

Nadiya Ibrahim Fagge
Nadiya Ibrahim Fagge

Nadiya ta ce: “Idan za a cire son rai, a yi amfani da iyawa, a kuma cire nuna bamabamcin launin fata, to za a rage matsaloli a duniyar kwallon kafa;

“Domin sai ka ga don ka samu matsala da mai horas da ku sai ya ajiye ka a gefe ya ki saka ka a wasa tsawon lokaci duk iyawarka, wannan ba matsala ce da a iya Afirka ake yi ba, duk duniyar kwallon kafa ne”.

Shawara ga ma masu yi musu kallon banza

Sun bukaci masu tsangwamar su su sani ba wani abin da addini ya haramta suke yi ba, hasali ma babu wata rubutacciyar doka da ta ce mata ba su da hurumin kallo ko bibiyar harkar kwallon kafa, domin abu ne na nishadi, kuma ra’ayi ne.

“Abinda kawai ya kamata ka yi shi ne kar ka bari ya sa ka shagala ka bar sallah saboda shi.

“Don ni burina duniya na ganni na je Emirate (filin wasan Arsenal), na zauna a stadium ina kallo; ina ji suma zan yi saboda murnar ina kallon kungiyar da na fi so’, in ji Zainab Naseer.

Nadiya kuwa ta shawarci matan aure su dinga fahimtar soyayyar mazajensu da kwallo, su daina cewa ba za su kalla ba saboda su ba sa so.

Ya ce ya kamata mta su dinga yi wa mazansu musu uzuri don a zauna lafiya, kasancewar abu ne da idan ya zame wa mutum jiki, sai hakuri.

“Ni ma ina burin na je  na kalli wasan, don ni ban taba jin ina so na je ba sai sanda muka yi sallama da Maselo da zai tafi ya bar Madrid din.

“To lokacin da ake bankwanan nan abin ya taba min zuciya, na ji ina ma ina can don ya san ni ma masoyiyarsa ce, don shi da Banzema su na fi so a kulob dinmu”.