✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda matasa 29 suka rasu a nutsewar jirgin ruwa a Sakkwato

An gano gawar mata 26 da maza shida bayan jirgin ya rabe gida biya a Karamar Hukumar Shagari.

Matasa 29 ne suka rasu nan take bayan jirgin ruwan da suke ciki ya rabi biyu a tsakiyar ruwa a kauyen Gidan Magana da ke Karamar Hukumar Shagari ta Jihar Sakkwato.

Da yake tabbatar wa Aminiya da nutsewar jirgin ruwan a ranar Laraba, Kansilan mazabar, Bilyaminu Abubakar Ginga, ya tabbatar da rasuwar mutum 29, da suka hada da mata 23 da maza shida, daga cikin mutum 33 da ke cikin jirgin.

“Jirgin yana daukar mutum 32 zuwa 33, matasa ne a cikinsa daga bakin shekara 16 zuwa kasa, suna kan haya ne jirgin ya samu hadari a sanadiyar bugun icce da ya yi a cikin ruwan.

“[Jirgin] ya dauke su ne sufuri domin a kai su wasu kauyukka makwabta da karfe 10 na safen Laraba lamarin ya faru da su,” a cewar Kansilan.

Ya bayyana cewa mutanen gari sun yi kokarin aikin gayya inda suka samu nasarar dauko gawa 29 ta matasan da ke cikin jirgin, an kuma ci gaba da neman ragowar.

Jirgin ruwan da ya yi hadari ya dauke su ne a hanyarsu ta zuwa daji domin samar da itacen girki da sauran wasu bukatu a wasu kauyukka na kusa da su.

A hanyarsu ta tafiya ce jirgin ya hadu da wani busasshen icen Giginya, abin da ya sanya ya rabu gida biyu matasan maza da mata suka nutse a tsakiyar ruwan.

Mutane sun yi cirko-cirko bayan an kwaso gawar matasa 29 da suka rasu a nutsewar jirgin ruwan. (Hoto: Nasiru Bello).

Ba yanzu  farau ba

Dan majalisa mai wakiltar Karamar Hukumar Shagari a Majalisar Dokokin Jihar Sakkwato, Honarabul Alhaji Maidawa Kajiji, ya ce an yi wa mutum 29 din da suka rasa rayukkansu a cikin jirgin sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.

“Ko a shekarar data gabata an samu irin wannan hadarin, kusan shekara uku ke nan a jere ana samun salwantar rayuwa a ruwan nan sai dai a koyaushe yanayin rasuwar yana bambanta.

“Wannan jirgin da ya tuntsure sanadin bugun busasshen ice da ke kasan ruwa, na zamani ne da wani ya saya domin yin kasuwanci a yankin, hakan ya sa muka dauka wannan abu ne daga Allah,” a cewar Maidawa Kajiji.

Ya yi kira ga Gwamnatin Jihar Sakkwato ta hada hannu da Gwamnatin Tarayya domin samar da babbar gada a saman gulbin, wanda hakan zai sa a tsiratar da rayuwar mutanen yankin domin ba su da wata hanya da suke mu’amala da junansu sai an tsallaka ruwan.