✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda matasa ke neman rusa gadar da ta hada yankunan garin Jos

Wata babbar gada da ta hada unguwannin Nasarawa da Majema da Bulbula da Dilimi da ake kira Gadar Sogai a garin Jos a Jihar Filato…

Wata babbar gada da ta hada unguwannin Nasarawa da Majema da Bulbula da Dilimi da ake kira Gadar Sogai a garin Jos a Jihar Filato na fuskantar barazanar rushewa, bayan da wadansu matasa da ke neman karafa ke hake kankarenta suna cire karafun rodinta da kwashe duwatsunta suna sayarwa.

Gadar wadda aka gina a 1977, ta fara fuskantar wannan barazana ce shekaru hudu da suka gabata.

Wani dan kungiyar ’yan sintiri ta Neighborhood da gidansa ke kusa da gadar, mai suna Zakari Lawal ya shaida wa Aminiya cewa wadansu matasa suna yanke karafunan gadar.

Ya ce da farko sharar da ake zubawa a gadar ce, idan ta yi yawa sai a sa wuta don ta kone.

Sai ta rika cin turken gadar karafunansa suka rika fitowa waje, daga nan kuma matasan suka fara fasawa suna yanke karafunan da daddare.

“Wani lokaci idan ina barci, sai in rika jin karar yanke karafunan gadar. Da farko matasan suna fakewa ne da sunan neman Kuza a kasan turakunan gadar.

“Kuma akwai wasu duwatsu a wajen, suna bi suna diba su sayar. Idan muka yi magana, sai ’yan unguwa su ce yara suna sana’arsu an hana su.

“Babu shakka muna samun kalubale daga iyayen yaran da suke wannan aika-aika,” inji shi.

Dan sintirin ya ce an kai shekara hudu ana wannan aika aika; Kuma abin da ya jawo hankalin mutane shi ne fitowar da aka fara gani na rodi-rodin gadar.

Ya ce turke daya ne karafunansa suka fara fitowa. Kuma saboda duwatsun da ake hakewa a kasarta abin ya shafi sauran turakun.

A cewarsa, yanzu gadar tana nuna alamun za ta fadi, domin tana rawa idan mota ta hau kanta. Ya ce masu gidajen da ke kusa da gadar na jin kararta idan motoci suka zo wucewa.

“Don haka mu ’yan banga da mai unguwar wurin da wadansu shugabanni mun kai shekara hudu muna gadin gadar da daddare.

“Amma wani lokaci yaran suna zuwa ne lokacin Sallar Asuba bayan mun tashi,” inji shi.

Wani mai shago da ke kusa da gadar, mai suna A.D Al-Mustafa, ya ce suna cike da damuwa kan gadar sama da shekara 10 da suka gabata.

Ya ce sun yi ta yi wa gwamnati korafi kan lamarin, amma babu abin da ta yi.

Al-Mustafa ya ce sharar da ake zubawa a gadar ana kunna wuta, hayaki na damunsu da kuma kurar da hakan ke haifarwa da illa ga lafiyarsu.

Ya ce ko ruwan sha ba sa iya ajiyewa saboda kurar da take tasowa daga gadar.

“Kusan dukkan sharar gefen garin Jos nan ake kawo ta, don haka muna kira ga gwamnati ta hana zuba sharar, domin illar da take yi na gurbata muhalli ya yi yawa,” inji shi.

Sulaiman Abdullahi Jaji mazaunin unguwar ya ce, ya kai shekara uku, yana tsawatar wa masu zuba shara a wurin.

Ya ce zuba shara a gadar ce matsala ta farko. Don haka suna rokon gwamnati ta katange gadar, don hana zuba shara a cikinta, kafin a zo kan yadda za a gyara ta.

Mai unguwar da gadar take, Umar Yakubu Umar (Abba), ya ce da suka gane matasa na taba gadar sun tashi tsaye don hana hakan.

Ya ce akwai ranar da suka yi artabu da yaran suka kore su, har suna cewa tunda ana hana su aiki a wurin, sai a ba su sana’ar da za su yi.

Ya ce matasan suna neman dutse ne a gadar, a haka suke cire karfen su je su sayar.

“Ganin haka na tafi na gaya wa Kwamandan Soja da ke kula da garin Jos, ya turo motar soja da matasan suka ga haka sai suka gudu, kuma sojojin sun fi wata shida suna gadin gadar.

“Da suka tafi, sai yaran suka dawo daga nan muka hada kai da ’yan bangarmu muna kwana a wurin don hana yarar ta’asar,” inji shi.

Mai Unguwa Umar ya ce abin takaici, wadansu mutanen da gidajensu ke kusa da gadar ne suke taimaka wa yaran idan aka bi su sai su shige gidajensu, sai iyayen su ce babu kowa.

Ya ce tuni sun sanar da hukumomin soja da na ’yan sanda da Karamar Hukumar Jos ta Arewa da Hukumar Bunkasa Birnin Jos da Kewaye (JMDB) da gwamnatin Filato don magance wannan lamari.

Ya tunatar da mutanen unguwar cewa wannan gada tasu ce, su ne suke amfani da ita.

“Idan mutanen unguwar ba su sanya ido kan gadar ba, in ta rushe, da wuya a sake gina mana a yanzu. Don haka mu tashi mu tsare gadar,” inji shi.

Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin, Kwamishinan Ayyuka na Jihar Filato, Mista Pam Botman kan lamarin ta waya, amma bai dauki wayar ba, sai dai wata majiya ta ce an kai korafi kan gadar ga gwamnati.