✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda matasa ke rububin neman auren ’yar a-mutun Kwankwaso

Matasan Kwankwasiyya na rige-rigen neman auren budurwar da ta fasa aure saboda Kwankwaso

Wasu mabiya ra’ayin siyasar Kwankwasiya ta tsohon Gwamnan  Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso na rige-rigen farautar soyayyar budurwan nan da ta yi watsi da manemin aurenta saboda ba ya kaunar Kwankwaso.

Bayan bullar labarin budurwar mai suna Lubna, wani saurayi masoyin tsohon Kwankwaso daga Jihar Gombe, Abdulrasheed Sa’id Bajoga, sa sanar da cigiyar ta da zummar auren ta.

Abdulrasheed ya ce, matukar Lubna ’yar a-mutun Kwankwaso ta shirya ta kuma amince ta maye gurbin tsohon saurayin nata da shi, to ya a shirye yake a shafa musu fatiha.

Ana cikin haka, wasu matasan suka bukaci Abdulrasheed ya wa Allah ya hakura, su sun ji, sun gani, za su aure ta saboda kaunarta ga jagoran nasu a siyasance.

Daga cikin matasan akwai wani ‘Real Abu Suhailert’ kamar yadda yake a shafinsa na Facebook, ind ya roki Abdulrasheed ya daga masa kafa shi ya aure ta.

“Don Allah ya yi hakuri domin kuwa na riga shi, yarinyar da ta san darajar masu daraja bai kamata a yi wasa a kanta ba,” inji shi, ya kuma bayar da lambar wayarsa cewa ta kiras hi su tattauna batun aurensu da zarar ta amince da tayin nasa.

Yin maganarsa ke da wuya, sai wani masoyin Kwankwason, Fahad Ibrahim Danladi ya ce, “Ni kuma zan biya sadaki.”

Bai dace ba

A gefe guda wasu na suka tir da matakin budurwar da ma samarin da suka nuna sha’awar auren ta, saboda a cewarsu, don siyasa ake neman kulla alakar auren ba don Allah ba.

Zan iya tarar mutuwa a kan Kwankwaso —Lubna

Aminiya ta kawo labarin yadda budurwar, ’yar asalin Jihar Kano ta lashi takobin watsi da duk wanda zai nemi auren ta matukar ba ya girmama Kwankwaso.

Ta ce a kan Kwakwaso za ta iya rasa ranta, kuma da ta auri wanda ba ya martaba shi, gara ta zauna har ababa ba ta yi aure ba.

“Na yi watsi da baikon manemin aurena saboda Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, duk da cewa Kwankwason ko sani na bai yi ba, amma a kansa zan iya karbar harsashi.”