✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda maudu’in Manzon Allah (SAW) ke tashe a Twitter

Dubun dubatar mutane na amfani da Maudu’in #Prophet Muhammad a Twitter

An wayi gari a safiyar Alhamis da ganin Hadisan Manzon Allah (SAW) suna tashe a shafin sada zumunta na Twitter.

Dubun dubatar Musulmai daga Najeriya sassan duniya ne suka rika kawo Hadisan Manzon Allah (SAW), yabon sa, nasihohi da bayyana farinci cikinsu kan tashen maudu’in #ProphetMuhammad suna wallafawa a shafukansu.

Ranar Alhamis daya ce daga ranakun da Musulmi kan yi azumin nafila kamar yadda Annabi Muhammad (SAW) ya kasance yana yi a lokacin rayuwarsa.

Daga cikin sakonnin sanu, Aliyu Shu’aibu ya kawo Hadisin da Manzon Allah (SAW) ya ce, “Da mutane sun san irin alherin da ke cikin Sallar Isha da ta Asuba, da sun halarce su (a masallaci) ko da da jan ciki ne.”

Ita ko Ammah (@ammahbukar), Hadisin da ta kawo shi ne fadar Manzon Allah (SAW) cewa, “Idan ka yi fushi to kar ka yi magana.”

Wakeuptoislam (@wakeuptoislam) kuma sun wallafa ce, “Mu yi kokarin ganin cewa ba mu da abin koyi fiye da Annabi Muhammad (SAW). #Sunnah.”

OluBebeji (Abdul_bebji) kuma ambato Hadisin “Ku yada kaututtuka za ku so juna.”

Sai Balogun Yusuf (@_Yusufbalogun) da ya kawo na “Ya ku mutane ku yada sallama a tsakaninsu, ku sada zumunci, ku ciyar da abinci, sannan ku yi (sallar) tsayuwar dare a lokacin da mutane ke barci, da haka za ku shiga Aljannar Ubangijinku cikin aminci.”

Herboo 0 (abubakarhayus) ya rubuta Hadisin da ke cewa, “Mafi alherin cikinsu shi ne wanda ya fi alheri ga iyalansa.”

@sir_zeesu kuma ya ambato fadin Manzon Allah (SAW) cewa: “Raka’a biyu na nafila Sallar Subahi ta fi duk abin da rana ta fito a kansa alheri. Duk wanda ya sallace ta zai kasance cikin kariyar Allah.”

Hadisinda  A.H Gumel, (@lol_blauster) ya kawo shi ne: “Mafi alherin aure shi ne mafi saukin sadaki.”