✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda maza ke gumurzu a Gidan Damben Gargajiya na Kano

Wakilin Aminiya ya leka gidan damben gargajiya da ke a harabar filin wasanni na Ado Bayero Square da ke a birnin Kano, inda ya ga…

Wakilin Aminiya ya leka gidan damben gargajiya da ke a harabar filin wasanni na Ado Bayero Square da ke a birnin Kano, inda ya ga yadda wasan ke gudana tare da kayatar da ’yan kallo.

Ya kuma yi nazarin yadda zamani ke yin tasiri a wasan da ma wasu batutuwan na daban.

Dambe wasa ne na gargajiya da ake alakanta shi da tarihin qasar Hausa. Yana xaukar sabon salo, musamman a Jihar Kano.

Dambe wasa ne na gargajiya da ake alakanta shi da tarihin kasar Hausa.

Yana daukar sabon salo, musamman a Jihar Kano.

Ganin yadda wasan ya karbu a wannan zamani izina ce ga yadda lokaci kan kitsa al’ada cikin zamani, musamman a wannan karni.

Akasin yadda yake a shekarun baya can, wani abin sha’awa ga wasan na dambe a wannan karni shi ne, yadda mahukunta suka haramata amfani da dukkan wani abu wanda ake ganin zai iya yi wa dan wasa illa, kamar burbushin kwalba da kan tabarya da dai sauransu.

Masu shirya irin wannan wasa suna yin amfani da salon gargajiya da kuma kimiyya wajen ganin sun sama wa wannan wasa matsuguni a wasannin zamani.

Shi dai wannan wasa yana karewa ne cikin turmi uku ba tare da iyakance lokaci ba.

Dan wasa ko alkalin wasa kan yi izini da wasa ya tsaya sakamakon wani dalili ko kuma idan dan wasa ya kashe abokin karawarsa.

Burin duk wani dan wasa a yayin damben shi ne ya buge abokin burminsa.

Hakar dan wasa kan cin ma ruwa ne idan har ya sami nasarar doke abokin karawar tasa.

Dambe kan iya zama mugun wasan da ya bar ’yan wasa da dama da karyayyun habobi da tabbai da kumburarrun mukamukai ko wawulo.

Amma wani abin sha’awa game da wasan shi ne, yadda yake debe wa ’yan kallo kewa sakamakon yadda suke samun nishandantuwa.

Kade-kade da wake-wake ga masu aikin gayya da dakarun yaki na da tsohon tarihi a al’adar Hausawa.

Su ma mawakan gargajiya na taka muhimmiyar rawar gani wajen zuga da tada tsimin ’yan wasan.

“Dambe na da tsohon tarihi a al’adar Hausawa, tamkar dai wasan kokawa, wasa ne da ake gudanar da shi a baya a lokacin girbi.

“Masunta kan takali mahauta. Jarumi zai takali abokin gwabzawarsa, duk wanda ya buge wani shi ya yi nasara,” a cewar wani dan kallo, Habu Dikko.

Masu shirya wasan

Wasan dambe na ci gaba da samun karbuwa a Jihar Kano, la’akari da yadda yake farfado da shahararren filin wasannin motsa jiki na Ado Bayero Square da ke a birnin Kano.

A bayyane take wasan zai iya farfado da filin wasan motsa jiki, wanda martabarsa ta yi kasa a baya-bayan nan.

Kewaye filin wasan yake da langa-langa, yayin da aka jera kujerun zama a gabar da’irar gwabzawa domin zaman ’yan kallo.

Ba abin da kake ji sai shewar ’yan kallo wanda ke zaune a kan kujeru ko kuma kututturen itatuwa, wasu kuma a tsaye ko a kasa.

Tsakiyar filin kuwa ba abin da kake gani cikinsa sai ’yan wasa sanye da kayan gwabzawa; yayin da hannun da ake bugu da shi yake nannade da igiya da ake kira kara, hannun kariya kuma an daga shi sama.

“Wuk wani wasa da ka sani kamar kwallon kafa ko wasan gora, asalinsa wasan gargajiya ne; daga baya ne yake gyara zama domin dacewa da zamani.

“Wasan dambe kuwa ya fara bunkasa ne bayan sanya shi cikin jerin wasannin kasa a shekarar 1998 a Jihar Imo.

“Muna ta yunkuri tun lokacin da muka karbi shugabanci domin ganin wannan wasa ya samu karbuwa a idon jama’a yadda ya dace.

“Sakamakon sauye-sauyen da muka kawo, da yawa daga cikin ’yan wasan sun yi watsi da wasan kan titi.

“A nan mukan shirya wasanni mabanbanta kuma ’yan wasa na samun alheri,” a cewar shugaban gidan filin damben, Muhammad Danlami.

Daruruwan matasa da manya da tsoffaffi da maza da mata ke tururuwa domin kashe kwarkwartar idanunsu yayin wannan wasa a kowane yammaci.

Akida na da tasiri a dambe

Akida ba ta kebanta da addini ko siyasa ba kawai.

A wasan dambe akida na da matukar tasiri ganin yadda magoya baya ke yin alfahari da nuni da akidunsu.

Duk da cewa Arewa (wadda aka fi sani da Jamus), Kudawa da Guramada manyan akidu ne a irin wannan wasa na gargajiya.

Wasan na daukar hankalin wasu magoya baya ne kawai domin nishadantar da su da yake yi.

“Ni Ba’are ne (Jamus) kuma ina alfahari da hakan.

“Na fara kallon dambe ne tun lokacin gwamnan farko na Jihar Kano, wato Audu Bako.

“Mahaifina ne ke kama hannuna zuwa fagen famar. Tun wancan lokaci nake kallon dambe har zuwa yau din nan,” inji wani dan kallo Auwalu Yakubu Dankano.

’Yan Wasa na da Sarkinsu

Sarauta a dambe na da matukar tasiri.

Martaba ce ga dan wasa wanda takan kuma sa shi ya yi fice cikin tsaransa.

Gasa daya bayan daya ake shiryawa duk shekara a filin wasan.

Amma wannan matsayi na iya samuwa ne kawai idan dan wasa ya yi nasara a gasar Kofin Sarkin Kano.

Gargajiya da zamani

A wannan zamani ’yan wasan dambe ba su da wani katabus illa su dora kafa daya cikin kogin al’ada, dayar kuma su saka ta cikin iskar zmani.

Masu daukar nauyin wasa da aka fi sani da Dambe Trador sun dogara ne kacokan kan kimiyya domin tallata wasan da kuma samin kudin shiga musamman ta hanyar amfani da kafar sadarwa ta Youtube.

Tsibbu a dambe ba bakon abu ba ne.

’Yan wasa kan tsattsaga hannuwansu tare da shafe su da maganin gargajiya har sai sun warke.

Imaninsu shi ne hakan na kara musu karfin bugu lokacin da suke gwabzawa.

Al’ada da kimiyya sun kasance kadangaren bakin tulu ga wannan wasa na dambe a wannan zamani.

Rashin amfani da kimiyya wajen tallata wasan domin samun kudin shiga na iya haddasa durkushewar wasan.

Duk wani yunkuri na watsi da tsibbu na iya sanyaya wa ’yan wasan gwiwa wajen guje wa wasan.

Babban abin al’ajabi game da wasan dambe shi ne, yadda aka kitsa al’ada cikin zamani domin sama wa wasan matsuguni a wannan karni da muke ciki.