‘Yadda mijina ke lakada min duka saboda ba na koshi’ | Aminiya

‘Yadda mijina ke lakada min duka saboda ba na koshi’

Kotu
Kotu
    Muhammad Kabir Muhammad

Wata mata mai shekara 23 da haihuwa ta bukaci wata kotun Shari’ar Musulunci da ke Magajin Gari a Jihar Kaduna, ta kashe aurenta a bisa zargin cewa mijinta na lakada mata duka saboda, a cewarsa, ba ta koshi.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato matar mai suna Firdausi tana shaida wa kotun cewa mijin nata, Haruna, kan kulle dakin girki idan dare ya yi.

“Mahaifina ne ya tilasta ni auren Haruna ina da shekara 16, kuma a shekara bakwai din da muka yi tare, ba a taba shekara guda cur bai kora ni gida ba.

“Bayan haka, ya hana kowa zuwa wurina – da abin ya ishe ni, iyayena kuma suka ji labarin abin da ke faruwa, suka kai kara wajen mahaifiyarshi, sai ta ce wai ya yi gamo ne”, inji Firdausi.

Lauyan Haruna, M.K. Mustapha, ya ce “Wanda nake karewa bai yi kama da mai tabin hankali ba. Hasali ma, yanzu haka yana Katsina yana wani aiki.”

Alkalin kotun, Nuhu Falalu, ya umarci lauyan Haruna ya gayyato iyayen ma’auratan saboda a warware matsalar cikin ruwan sanyi, sannan ya dage sauraren kara zuwa 4 ga watan Oktoba.