Daily Trust Aminiya - Yadda Musulmi ke azumin Ramadan da dokar hana fita
Subscribe

Musulmin Najeriya da dama sun ce ba su taba yin azumi a irin wannan yanayin ba

Yadda Musulmi ke azumin Ramadan da dokar hana fita

Watan Ramadan wata ne mai alfarma ga miliyoyin Musulmin duniya wanda a cikinsa ne sukan taru don gudanar da salloli da addu’o’i.

Watan Ramadan a kowace shekara lokaci ne da Musulmi a fadin duniya ke gani a matsayin lokacin ibada wanda yake zuwa sau daya tal a shekara.

Sai dai kuma a wannan shekarar haduwar da masu ibadar kan yi don yin salloli da gabatar da addu’o’i ka iya zama jidali ganin yadda ya ritso cikin dokar takaita zirga-zirga da gwamnati ta saka a jihohi don hana yaduwar annobar coronavirus wadda ake yiwa lakabi da COVID-19.

Kamar dai yadda annobar ta shafi yadda ake gudanar da sauran al’amuran yau da kullum a wannan shekara, azumin watan Ramadan ma za a yi shi ne ba kamar yadda aka saba ba a shekarun baya, domin kuwa ya fado a tsakiyar lokacin da duniya ke yaki da annobar coronavirus wadda ta addabi duniya.

Wani irin hali

Aminiya ta zanta da wasu Musulmi don jin yadda suka shirya yin azumin watan Ramadan na shekarar Musulundi ta 1441 bayan Hijra a cikin wannan yanayi.

“Muna cikin wani hali da ba mu taba gani ba, domin kusan ko’ina a rufe yake.

“Sannan kuma Musulmi ba sa taruwa waje daya su tsaya gab da gab, kowa nesa-nesa yake da dan’uwansa, don haka wannan Ramadan din ya sha bamban da wadanda muka saba gani a shekarun baya.

” Zai yi wuya mu iya yin abubuwan da muka saba, kamar su sallar jam’i da taruwa da abokai don yin bude baki da dai sauran abubuwa da muke haduwa muna yi.” Inji Ahmed Doyin Balogun.

Babu kudin abinci

Husaini Adamu kuwa cewa ya yi “Muna cikin mawuyacin hali”, sannan ya ci gaba da cewa, “Babu kudin da za mu sayi kayan abinci, sannan kuma ba za mu samu damar haduwa mu ci abinci tare da ‘yan uwa da abokai ba.”

Samir Ali, wani mai sayar da dabino, wato dan itaciyar da aka fi so a bude baki da shi a cikin watan azumi, cewa ya yi wannan shekarar bai taba ganin irinta ba wajen rashin ciniki.

“A shekarun baya, da zarar azumin watan Ramadan ya karato da mako daya, za ka ga muna ta hada- hada, amma yanzu saboda coronavirus ban sayar da ko daya bisa hudun abin nake sayarwa ba a shekarun baya”, Inji Ali.

Abin sha’awa

Da aka tambayi Aishah Lawal game da abin da ta shirya wa wannan wata mai tsarki sai fuskarta ta sauya.

“Annobar coronavirus ta sa duk hadahadar da ke gudana kwanaki ko makwanni kafin zuwan Ramada duk ba armashi. Ina kewar watan Ramadan na shekarun baya.

“Abin takaici ne b azan samu sallar Tarawih a cikin jam’I ba, sai dai abin sha’awa shi ne zan yi salla a cikin gida da iyalina don yin biyayya ga umarnin gwamnati nah ana fita”, inji ta.

Kasashe da dama dai sun shawarci al’ummominsu su guji tarurrukan mutane da yawa kuma su sha ruwa a daidaikunsu ko kuma tare da iyalansu a gida.

A yi azumi lafiya.

More Stories