✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mutanen Jingir suka yi wa ’yan bindiga kofar rago

Hadin kan mutanen Jingir abin koyi ne ga ’yan Najeriya

Sau biyu mutanen yankin Jingir suna yi wa ’yan bindiga taron dangi su kama su tare da kwace makamansu.

Tun da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da mashawarcinsa kan tsaro suka kirayi ’yan Najeriya da su tashi tsaye su taimaka wa kokarin da gwamnati da jami’an tsaro ke yi na yaki da ta’addaci, masu satar mutane da ’yan bindiga, su daina nuna musu tsoro da barin su suna ta’annati ba tare da an dakatar da su ba, ta hanyar hadin kai da kishin kasa, ’yan Najeriya da dama ke bayyana ra’ayoyi mabambanta, bisa la’akari da ganin yadda talakawa marasa kwarewa da makami za su iya tunkarar masu rike da muggan makamai, marasa tausayi da imani.

Duk da yadda masu irin wannan tunani ke kashe gwiwar wasu ’yan Najeriya daga tunanin fuskantar masu ta’addanci da makamai, wannan bai hana al’ummar yankin Jingir da ke Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato tashi tsaye, da cire tsoro a ransu su tunkari wani gungun mutane da ake zargin masu garkuwa da mutane suna karbar kudin fansa ne, da wasu ’yan fashi da suka addabi yankin ba.

Ga duk wanda ya san hanyar Jingir zuwa Jos ko kuma Jingir zuwa Saminaka a Jihar Kaduna, ya san hanya ce da take fama da bata-gari masu tare hanya suna yi wa matafiya fashi ko satar mutane suna garkuwa da su a cikin dazuka, musamman ma ranar Lahadi, da ta zama zama ranar Kasuwa Jingir, babbar kasuwar da ta hade garuruwa da dama da ke iyakokin jihohin Filato, Bauchi da Kaduna.

A irin wannan rana ta Lahadi ne 14 ga watan Maris, 2021 wasu masu garkuwa da mutane suka kai hari wani kauye kusa da Jingir mai suna Mun-Tsira, inda suka sace wasu mutane uku tare da kashe wani matashi magidanci da ya yi ihun neman taimakon jama’a.

Labarin wannan al’amari ya watsu kusan a ko’ina a tsakanin kauyukan da ke kewaye da yankin kuma babu shakka ya sanya tsoro da firgici a zukatan jama’a.

Washegari Litinin da rana wasu mazauna kauyen Bauda da ke kusa da Mun-Tsira suka ga ayarin wasu mutane a kan babura da yawansu ya kai kimanin 17.

Wannan dandazo da suka gani ya haifar musu da zargi da kokwanto kan gaskiyar mutanen da kuma abin da ya shigar da su yanki, duba da yadda ake labarin irin barnar da ’yan bindiga ke yi a wasu jihohin Arewa, irin su Zamfara, Katsina, Neja da Kaduna.

Wannan tunani shi ya zaburar da mutanen kauyen musamman matasa, Musulmi da Kiristan su, suka hada kai suka tunkari inda suka ga mutanen da ke kan babur sun nufa.

Suka kuma kira wasu daga cikin mutanen kauyen Mun-Tsira don su ma su tashi su tunkari ayarin mutanen da ke nufo kauyen su, yayin da su kuma suka bi su a baya, aka sa masu baburan a tsakiya.

Da masu baburan suka an biyo su, sai suka nemi mafaka suka boye a cikin cikin daji.

Su kuma mutanen da ke bin su suka ja tunga a bakin wajen, suka kuma gayyato karin mutane daga kauyuka na kusa, suka kewaye wajen kowannensu dauke da sanduna da gorori.

Da suka tabbata sun yi wa dajin kawanya sai aka aika da wasu da suka sanar da jami’an tsaro da ke cikin gari.

Bayanai sun tabbatar da cewa mutanen sun kwana suna gadi don kada miyagun da ake zargi su fita su gudu.

Washegari da sanyin asuba jami’an tsaro suka isa wajen suka kutsa kai cikin dajin da wadanda ake zargin masu garkuwa da mutane ne suke boye, aka fitar da su tare da bindigogin da aka ce an samu a tare da su.

Wannan al’amari ya kara hada kan jama’a a yankin sosai, ganin yadda aka kawar da bambance-bambance aka tunkari wannan matsala da ake ganin za ta iya jefa yankin cikin babbar damuwar tsaro.

Ko da yake ba a rasa masu fargabar yiwuwar kawo ramukon gayya daga ’yan uwan mutanen da ake zargin ’yan bindiga ne ba.

Abin da ya faru ya sake karfafa wa mutane gwiwa sosai tare da cire musu tsoro.

Ko a ranar Laraba 17 ga watan Maris, da aka samu wasu ’yan fashi su uku da suka far wa wani dan kasuwa a cikin garin Jingir, mutane ba su yi wata-wata ba suka fatattaki ’yan fashin da suka ranta a na kare.

Ko da yake ba a samu nasarar kama su duka ba, amma an cimma dayansu, wanda ya gamu da fushin jama’a.

Yayin da jami’an tsaro ke ci gaba da gudanar da bincike game da wadannan batagari da ake zargi, ya zama dole a kara jinjina wa jaruman matasan Jingir da kewaye, bisa hadin kan da suka nuna da kuma jajircewarsu wajen tallafa wa jami’an tsaro da ’yan sa-kai wajen kare yankin.

A karshe muna kira ga jama’ar yankin Arewa da ma Najeriya baki daya, su hada kansu su kawar da siyasa da bambance-bambancen da ke tsakaninsu, don taimaka wa kasarmu ta samu cigaba.

Abbas Sadi Jikan Liman, shi ne shugaban Kungiyar Arewa Media Writers, reshen Karamar Hukumar Bassa a Jihar Filato.