✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda mutanen kauye suka ceci direban jirgin da ’yan bindiga suka harbo

Karo na biyu da ’yan bindiga suka harbo jirgin sojin Najeriya a 2021.

Mutanen kauyen da jirgin sojin da ’yan bindaga suka harbo ya fadi sun bayyana yadda suka taimaki matukin jirgin har ya koma sansanin soji.

Majiyarmu ta tabbatar da cewa jirgin ya fadi ne a wani kauye kusa da Dansadau bayan matukinsa ya yi saukar lema a ranar Lahadi.

Wani mazaunin kauyen (an sakaya sunan kauyen) ya ce, “Matukin jirgin ya yi saukar lema sannan daga baya ya shiga kauyen.

“Da mutanen kauyen suka gane abin da ya faru, sai suka boye shi saboda kada ’yan bindigar su gane shi.

“Jim kadan bayan jirgin ya fadi, ’yan bindigar sun je wajen watakila domin su ga ko akwai wanda ya tsira,” kamar yadda ya bayyana.

Bayan an boye shi ya kwana, washegari da safe sai ya yi shiga irin ta mutanen kauyen suka tafi da shi zuwa wajen sojoji mafi kusa.

Kakakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya, Edward Gabkwet, ya ce jirgin samfurin Alpha Jet ya fado ne bayan ’yan bindiga sun bude masa wuta a tsakanin iyakar jihohin Zamfara da Kaduna a ranar Lahadin.

Ya tabbatar wa ’yan jarida cewa, “Ta hanyar amfani da tunaninsa na tsira, matukin jirgin, wanda ya gamu da mummunar hari daga ’yan binidga, ya kauce musu ya nemi mafaka a garuruwan da suke kusa har zuwa faduwar rana.”

Jami’in ya ce bayan saukar lemar, matukin jirgin, Filayi Laftana Abayomi Dairo, ya yi ta sanda yana kauce wa mafakan ’yan bindigar har ya isa wani sansani na sojin kasa.

Dajin da aka harbo jirgin yana da iyaka da jihohin Zamfara da Kebbi da Neja da Kaduna, kuma akwai sansanonin ’yan bindiga na Dogo Gide da wani mai suna Sani Mochoko.

Ana tunanin Dogo Gide yana da alaka da Kungiyar Boko Haram ko ISWAP.

Harin shi ne na biyu da aka harbo jirgin sojoji a bana — kodayake ana takaddama kan ikirarin Kungiyar Boko Haram na harbo na farko a Jihar Borno.

Karo hudu kuma ke nan da jiragen sojin Najeriya suka yi hadari a bana.