✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda mutuwa ta yi wa ‘ya’yana 10 dauki dai-dai

Magidancin ya ce, “Bayan ni da mahaifiyarsu babu ko da daya da ya rage a duniya”.

Wani magidanci da ’ya’yansa 10 suka rika mutuwa daya-bayan daya a lokaci ya bayyana yadda abin ya faru.

Abdullahi Bello, wanda ke cikin tsananin kaduwa ya ce mutuwa ta yi wa ’ya’yan nasa su 10 dauki dai-dai ne tare da kanwarsa da ta kawo masa ziyara.

“Bayan ni da mahaifiyarsu, babu kom mutum daya da ya rage; duk sun mutu,” inji shi.

Mahaifin yaran, wanda ke zaune a kauyen Jangeme na Karamar Hukumar Gusau ya ce kanwar tasa ce ta dafa tuwon bayan ta debo dawa daga rumbu an niko.

A cewarsa, wani zomo ya mutu bayan da ya ci garin, tun ma kafin a dora sanwar.

Bayan cin abincin ne iyalan nasa suka shiga ta kansu, inda ’ya’yan nasa 10 suka rika mutuwa daya bayan daya.

“Mutuwar ’ya’ya da yawa haka a lokaci guda babban abin tashin hankali ne; Na yi kwanaki ba na iya barci.

“Ita kuma matata sai da aka kwantar da asibiti sabota tashin hankalin da ta shiga. Za mu dade abin yana damunmu.”

Ya ci gaba da cewa bayan mutuwar wadanda suka mutu a gida, “Mun kai ragowar yaran asibiti a Gusau, a can ne biyu daga cikinsu suka rasu.

“Bayan mun dawo gida muna shirin yi musu jana’iza sai aka kira ni a waya cewa wasu uku sun rasu ciki har da kanwata da ta dafa tuwon.

“’Ya’yana 10 da kuma kanwata ke nan suka rasa ransu, babu abin da za mu yi sai dai mu dauki abin da ya faru a matsayin kaddara, mu fawwalla wa wa Allah al’amarinSa.”

Wakilinmu ya gano cewa Sadiq mai shekara 11 shi ne na 10 daga cikin ’ya’yan mutumin, kuma a rasu ne a Asibitin Kwararru na Gusau inda aka kwantar da shi.