✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na yi gamo da kura a wajen neman kudi —Aminu Dantata

Yana kwance da dare ya ji motsi, da ya leka sai ya ga kura ce ke neman shigowa dakinsa

Aminiya ta yi tattaki zuwa gidan fitaccen attajirin nan na Kano, Alhaji Aminu Alhassan Dantata, a unguwarsu da ke Koki, a birnin Kanon Dabo.

Alhaji Aminu Dantata na daya daga cikin tsofaffin masu arzikin da ake maganarsu, har yau a Najeriya, kuma ya fara neman kudi ne tun yana matashi.

A hirar ta musammanan da ya yi daAminiya, Alhaji Aminu Dantata ya ce a lokacin da yake matashi, bai taba jin kunyar yin duk wata sana’a da za ta kawo masa kudi ba.

Ya ce duk wani abu da mutumin da ke zaune a kauye yake yi, domin ya samu kudi, ya yi a lokacin da yake matashi.

Ya kuma yi kananan sana’o’i da dama da ake yi a kauye, tun daga sayar da ruwa da sayen kayan amfanin gona duk ya yi.

  • Gamon Alhaji Aminu Dantata da kura

Alhaji Aminu Dantata ya yi tafiye-tafiye zuwa garuruwa da kauyuka da dama a Arewacin Najeriya, don sayen gyada da sauran kayan amfanin gona.

A wadannan tafiye-tafiye da ya yi, wata rana wani abu ya faru da shi, wanda ba zai taba mantawa  ba.

Wannan abu kuwa shi ne wata rana da daddare ya hadu da kura a lokacin da ya je Daura, don sayen kayan amfanin gona.

Yana kwance da daddare a dakin da ya kama na jinka, bayan ya gama sayen kayan gona, sai ya ji motsin dabbobi, a bayan dakin.

Da ya leka waje sai ya ga ashe kura ce, take kokarin shigowa dakin.

A lokacin ya firgita, amma Allah cikin ikonSa kurar ba ta samu damar shiga dakin ba, balle ta ji masa ciwo.