✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na haihu a hannun ’yan bindiga —Mai jego

Ina goye da dana ga kuma tsohon ciki a lokacin da suka yi garkuwa da ni

A ranar Asabar 26 ga Disamba, 2020 ne ’yan bindiga suka yi garkuwa da Suwaiba Naziru mai tsohon ciki tare da danta mai shekara biyu a kauyen Biya Ki Kwana da ke Karamar Hukumar Batsari, Jihar Katsina.

Da misalin karfe 8 na dare ne ’yan bindiga da suka far wa kauyen da harbe-harbe suka jikkata matasa biyu tare da yin awo gaba da matan aure da ’yan mata 10.

Daga nan ’yan bindiga suka tisa keyarsu da bakin bindidga, inda suka shafe tsawon dare suna tafiya a cikin kungurmin jeji inda ta haifi jaririya a hannun masu garkuwar.

Bayan na sai masu garkuwar suka kira ’yan uwanta ta waya suka yi musu albishir suka kuma bukaci su je da lafiyayyen mashin cike da mai su dauki mai jegon a Sabon Garin Dumburawa, kamar yadda wani dan uwanta ya shaida wa Aminiya.

“Ba mu nutsu da su ba, wanda zai je ya dauko ta na tsoron kar ’yan bindigar su rike shi a maimakonta ko su kwace babur din a matsayin kudin fansa, saboda haka sai ya ki zuwa,” inji shi.

Da masu garkwar suka sake kira don su ji ko an tafi a dauko ta sai aka ce da su ba a samu mashin ba, saboda haka sai su da kansu suka kai ta kauyen Dangeza, daga nan kuma aka dauke ta a kan wani babur zuwa gida.

A tattaunawarta ta musamman da Aminiya, Malama Suwaiba ta bayyana irin halin da ta shiga a ranar da aka yi garkuwa da ita da kuma abin da ya biyo baya.

Ko za ki iya tuna abin da ya faru a ranar da aka yi garkuwa da ke?

Mijina ya tafi Kudu ci-rani domin nemo mana abinci, ga shi abin da ya rage a rumubunmu ya kare.

Da misalin karfe 8 na dare sai na tafi neman wayar don in kira in ce masa ya yi kokari ya turo mana kudin abinci.

A hanyar ce na yi kicibus da ’yan bindigar tare da wasu matan kauyen da suka yi garkuwa da su.

Daga nan sai ’yan bindigar suka ce ni ma in bi su amma na ce musu  inda da tsohon ciki, amma suka ce karya nake yi, suka tirsasa mini bin su cikin jeji tare da suran matan kamar tumaki.

Shin ba su ga tsohon cikin da kike dauke da shi ba ne?

Kamar yadda na ce, na gaya musu amma suka karyata ni, sai da suka ga na fara nakuda kafin suka yarda.

Yaya tafiyar ta kasance miki, ga shi a lokacin kina da tsohon ciki?

Ba zai kwatantu ba. Ban san yawan kilomitocin da muka shafe muna tafiya a kasa ba, amma da muka isa wani kauye da ke bayan garin Rinji sai suka goya mu a babura zuwa maboyarsu.

Ga shi bayan tsohon ciki da nake dauke da shi, ina kuma goye da dana mai shekara uku a lokacin.

Haka na yi ta fama, mutum shi kadai ma yaya ya kare, balantana a ce ga tsohon ciki ga kuma goyo.

Mun shafe tsawon dare muna tafiya, muka isa daf da wayewar gari.

Yaya nakudarki ta kasance, ganin cewa kina hannun ’yan bindiga?

Da na fara nakuda sai daya daga cikin matan da aka sace mu tare ta rika taimaka min a matsayin ungozoma.

Ita ce ta kanance tare da ni har bayan da na haihu —su ne suka ba ta reza ta yanke cibiya.

Yaya masu garkuwar suka yi bayan kin haihu?

Sun kawo min ruwan zafi na yi wanka, aka wanke jaririn, suka kuma ba da reza aka yanke cibiya, kamar yadda na shaida maka.

Bayan nan sai suka ce za su sanar da shugabansu ya ba da izinin saki na; suka yi tafiyarsu suka dade, daga baya shugaban nasu ya aiko cewa a mayar da ni gida.

Sun dauke ni tare da ’ya’yana biyu a kan babur suka kai ni kauyen Dangeza, daga nan kuma wani mai babur ne ya kawo ni gida.

’Ya’yanki nawa?

Haihuwata ta biyu ke nan. Na farkon ne nake goye da shi a lokacin da suka yi garkuwa da mu, shekarunsa biyu da rabi, ya kusa kaiwa uku.

Yaya za ki kwatanta haihuwan biyu, wanda kika yi a gida da kuma wanda kika yi a hannun ’yan bindiga?

To, akan ce haihuwar fari ta fi wa mata wahala da zafi kasancewar karon farko ke nan.

Amma ni ta wannan ta biyun ta fi min zafi saboda irin wahalar da na sha kafin haihuwar.

Ko a tafiyar da muka yi a kan babura, tsananin gudun da suke yi da  rashin kyan hanyar kadai sun ishi mutum wahala.

Bacin wannan wahalar, uwa uba kuma ga yunwa, duk sun sa na yi rauni sosai, don haka nakudar ta jigata ni, amma na gode Allah tunda na haihu lafiya abin da na haifa ma lafiya.

Sun ba ku waurin kwana ne ko kuma a fili kuke barci?

Akwai ’yan bukkoki da muke barci a ciki amma babu tabarmi a cikinsu, a kasa muke kwanciya, ko da yake kwanana daya ne a wurin banda ranar da muka kwana a hanyar zuwa wurin.

A ranar da na haihu suka sake ni aka mayar da ni gida.

Yanzu yaya yanayin da kike ji ke da jaririn?

Dukkanmu biyun muna cikin koshin lafiya.

Shin an kai ki asibiti bayan dawowarki?

A’a. Ban je asibiti amma lafiyata lau, babu wata alamar rashin lafiya.

Yaya sunan jaririn da kika haifa?

Ba a cika kwana bakwai ba tukuna. A al’adarmu sai bayan kwana bakwai da haihuwa ake sanar da sunan jariri a wurin taron suna.

Yaya labarin sauran matan da aka yi garkuwa da su?

Har yanzu suna can a hannunsu, amma da za mu dawo sun ce in gaya wa jama’a cewa don Allah ko roko ne a yi don a samu kudi a kubutar da su daga mummunar rayuwar da suke ciki a hannun masu garkuwar.