✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na kubuta daga hannun ’yan bindiga —Dalibin GSSS Kankara

Dalibin da ya kubuta ya ce su 520 ne ’yan bindiga suka shiga da su cikin daji

Daya daga cikin daliban da ’yan bindiga suka sace a Makarantar GSSS Kankara, Jihar Katsina, ya ce ya samu ya tserewa daga hannun masu garkuwar ne bayan maharan sun tursasa su shiga cikin daji. 

Dalibin wanda ya ce ba su farga cewa garkuwa da su aka yi ba sai da masu garkuwar suka tara sa a wuri daya, ya ce su 520 ne ’yan bindiga suka dauke.

“Da muka fara jin karar harbin bindiga a sama sai muka fara gudun neman tsira, ashe maharan tuni sun mamaye mu”.

Ya shaida wa Sashen Hausa na BBC cewa: “Lamarin ya faru ranar Juma’a da misalin karfe 9:30 na dare bayan mun dawo cikin ajujuwanmu daga karatun dare, kwatsam sai muka fara jin karar harbin bindiga.

“Sai muka fara zaton ba a cikin makarantarmu ba ne, can sai muka fara ganin suna shigowa inda muke”, inji dalibin mai shekara 17 da mahaifinsa ya bukaci a sakaya sunansa.

“Muka fara guduwa hanyar fita daga cikin makaranta, sai suka fara amfani da hasken cocila suna haska mu, suna cewa mu dawo.

“Sai muka fara tunanin jami’an tsaro ne, sai da suka tattara mu wuri guda sai muka gano masu garkuwa da mutane ne”.

Ya bayyana cewa, ’yan bindigar sun daddake su sun kuma tursasa su shiga cikin daji da dai sauransu.

Dalibai 520 ne ’yan bindiga suka dauke

“Bayan sun shigar da mu cikin daji sai suka sa daya daga cikinmu ya kirga yawanmu, inda ya kirga yara 520.

“Saboda lokacin dare ne ban iya fahimtar ina suka kaimu ba, sun daddake mu, mun kwashe kusan ilahirin daren muna tattaki a cikin dajin duk da kayoyin da ke dajin.

“Bayan minti 30 da wayewar gari sai suka ce mu kwanta mu yi barci”, kamar yadda ya bayyana.

Yadda na kubuta daga wurin ‘yan bindiga —Dalibi

Da yake magana game da yadda ya kubuta daga hannun ’yan bindigar, dalibin ya ce Allah ne kadai Ya san yadda ya samu ya tserewa daga hannunsu.

Ya ce da farko ya buya ne a bayan wata bishiya, kafin daga baya kuma ya samu ya tsere a cikin dajin.

“Lokacin da suka ce mu zauna na samu nasarar labewa a bayan wata bishiya bayan sun tafi da wata tawagar ’yan uwana dalibai, sai na fara bi ta wuraren gefen babbar hanyar dake kusa da garin.

“Daga nan sai na gudu, ina tafiya ba na iya ganin komai kuma; ban san ina suka nufa da sauran ’yan uwana daliban ba, kawai dai sun shiga da su cikin daji”, inji kubutaccen dalibin.