Yadda Na Lashe Gasar Adabi Duk Da Ana Hana Ni Rubutu –Gwarzuwar Hikayata | Aminiya

Yadda Na Lashe Gasar Adabi Duk Da Ana Hana Ni Rubutu –Gwarzuwar Hikayata

    .

Aishatu Musa Dalil matashiya ce mai shekara 18 a duniya; tana karanta Kimiyyar Harsuna a jami’a tare da neman kwarewa a Ingilishi da Faransanci.

Ita ce kuma ta lashe Gasar BBC Hausa ta Rubutun Gajerun Labarai ta Mata, wato Hikayata, ta bana.

A wannan hirar da Aminiya, ta bayyana yadda ake hana ta rubutun adabi, amma duk da haka ta rubuta littattafan kagaggun labarai na Hausa, ga shi kuma ta ciri tuta a wata gasa ta rubutu.