✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Na Lashe Gasar Adabi Duk Da Ana Hana Ni Rubutu –Gwarzuwar Hikayata

Aishatu Musa Dalil matashiya ce mai shekara 18 a duniya; tana karanta Kimiyyar Harsuna a jami’a tare da neman kwarewa a Ingilishi da Faransanci. Ita…

Aishatu Musa Dalil matashiya ce mai shekara 18 a duniya; tana karanta Kimiyyar Harsuna a jami’a tare da neman kwarewa a Ingilishi da Faransanci.

Ita ce kuma ta lashe Gasar BBC Hausa ta Rubutun Gajerun Labarai ta Mata, wato Hikayata, ta bana.

A wannan hirar da Aminiya, ta bayyana yadda ake hana ta rubutun adabi, amma duk da haka ta rubuta littattafan kagaggun labarai na Hausa, ga shi kuma ta ciri tuta a wata gasa ta rubutu.