✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda na sayar wa mutane mushen kaji 6,000

Shekara biyar mutane na sayen mushen kaji a wurinshi ba su sani ba

Wani matashi ya bayyana yadda ya rika sayar da matattun kaji guda 6,000 ga mutanen domin ya samu kudin kashewa.

Matashin mai shekara 33, ya ce ya shekara biyar yana sayar da mushen kajin ne a garin Maiduguri, tun bayan rasuwar mahaifiyarsa don ya samu kudin da zai rika rayuwa.

Wanda ake zargin ya bayyana hakan ne lokacin Rundunar Tsaron ta NSCDC reshen Jihar Borno ke gabatar da shi ga ‘yan jarida a ranar Laraba.

Ya ce yawanci yakan je Kogin Ngadabul, a bayan Gidan Radiyo da Talabijin na Jihar Borno (BRTV), don kwasar matattun kaji da aka jefar daga gidajen kaji.

“Duk mako nakan zabi akalla goma ko ma fiye da hakan, sannan in sarrafa in je in sayar wa mutane, su kuma ba su sani ba.

“Kasuwannin da nake kai kajin su ne kasuwar kifi ta Baga, inda nake sayar da wasu daga a matsayin naman daji; sai kuma Kasuwar Monday, gidajen suya da wasu zababbun gidajen abinci a cikin garin.

“Yawanci nakan sayar a kan N700 zuwa N800. Amma idan suka yi kwanaki, sai in kai su wuraren shan giyar da ke bayan unguwar Ngomari in sayar da su kan Naira 250,”minji shi.

Matashin ya ce shaidan ne ya ingiza shi cikin irin munanan aikin, don haka ya nemi a yi masa afuwa.

Kwamandan NSCDC na Jihar Borno, Abdullahi Ibrahim, ya ce an kama wanda ake zargin ne a lokacin da yake taksa da gyara mushen a bayan gidan BRTV a ranar 2 ga Janairun 2021.

Ibrahim ya ce rundunar ta samu rahotannin sirri ne game da miyagun ayyukansa kafin ta fara aiki don cafke shi.

Ya kara da cewa damke wanda ake zargin ya dakatar da abin da ya kasance mummunan hadari ga mutane.

A nasa bangaren, Babba Jami’in Jihar Borno na Hukumar NAFDAC mai kula da inganci abinci da maguna, Nasiru Mato, ya ce wannan aikin barazana ce ga lafiyar jama’a.