✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda na yi mako bakwai da tsohon ciki a hannun masu garkuwa’

Thamina ta bayyana yadda ta shafe mako bakwai a hannunsu.

Daya daga cikin fasinjojin da ’yan ta’adda suka saki bayan sace ta a harin jirgin qasan Kaduna zuwa Abuja, Thamina Mahmood ta ce tausayi ne ya sa aka sake ta, kuma ko sisi maharan ba su karba ba kafin sako ta.

A tattaunawarta da Aminiya, Thamina, wacce aka sako ta saboda tana da juna-biyu, kuma take tsammanin haihuwa yau ko gobe, ta ce karfin bindiga ba zai iya kubutar da wadanda suke hannun maharani.

Thamina ta yi kira ga Gwamnatin Tarayya ta kara azama wajen kubutar da sauran mutanen, musamman la’akari da halin da wadansu daga cikinsu suka fada, ciki har da wata tsohuwa da kananan yara.

Yadda abin ya faru

Thamina ta ce, “Muna hanyar tafiya Kaduna daga Abuja a wannan rana ta Litinin a jirgin karfe shida, lokacin mun kusa isa Kaduna, saura bai fi kamar minti 15 ba zuwa 20 ba, sai muka ji jirgi ya fara girgiza, sai kara irin ta bam. “Daga nan dai abubuwa da yawa suka yi ta faruwa.

“Sai maharan suka fara bin tarago-tarago, suna fitar da wadanda za su fitar, wadanda kwanansu kuma ya kare suka harbe su.

“To ina cikin mutanen da suka kada zuwa cikin daji, ni da mijina. Mun yi tafiya mai tsawo da sauran mutane, kamar mutum 60 da wani abu haka, a cikin daji. Wani gun a kafa, wani wajen kuma a kan babur.

“Bayan kamar kwana uku zuwa hudu, muka isa inda suka ajiye mu, a kungurmin daji, cikin duwatsu da bishiyoyi haka suka ajiye mu.

“Abin da suka fara yi shi ne suka nema mana abin da za mu ci da wanda za mu sha. Kuma a cikin ’yan kwanakin idan aka dan yi tafiya mai tsawo sai a tsaya a huta, a sha ruwa a ci abinci, a tsaya a huta. A haka har muka isa daidai inda suke so su ajiye mu.

“Da farko ba mu ma gane mutanen da suka kama mu ba, amma bayan ’yan kwanaki sai muka fahimci ’yan Boko Haram ne, kuma suka fadi dalilin da ya sa suka kama mu,” inji Thamina.

Dalilin da suka kama mu

Ta ce, “Dalilin kama mu a cewarsu wai suna da wata bukata a wajen gwamnati, shi ne suke so su ja hankalin gwamnati don ta saurare su, ta bas u abin da suke so.

“Amma tsakani da Allah tun da suka kama mu, babu wani cin zarafi. Na san dai sun yi duka sau daya, sun daki mazanmu, amma tun daga nan ba su kuma dukansu ba, wadanda suka ji rauni suka ce bayan kwanaki za a kawo musu magani. Iya gwargwado suna ba mu abinci,” inji ta.

Ba su taba hana mu Sallah ba

“Suna Sallah kuma mu ma muna yi. Har wadanda ma ba su da kallabi, a kan ba su mayafi su suturce jikinsu yadda za su iya yin Sallar. “Ta bangaren shimfida kuwa, gaskiya da a kasa mu ke kwanciya. Amma daga baya sai suka fara dubawa akwai tsofaffi, akwai masu yara, akwai kuma kamar ni ina da juna-biyu, sai suka fara kawo mana abin kwanciya kamar buhu haka.

“Daga baya sai suka kawo tamfol. Da ruwa ya fara kankama, saboda gaskiya ana yin ruwa a-kai- a-kai a wajen, sai suka fara kawo bargo ga masu raunin cikinmu. Kamar ni suka ce ko akwai magungunan da nake sha a cikin irin wadanda suka kawo? Na ce musu, a’a.

“Sai suka tambaya da me da me nake sha, saboda su tabbatar ban wahala ba. Duk magungunan da mace mai ciki take sha ba wanda ba su kawo min ba. In ma na ce ina bukatar wani abu, za su kawo su ba ni. Iya gwargwado sun kula da mu, babu wanda suka ci zarafi,” inji ta.

Ko sisi ba a ba su ba kafin su sako ni

“Ko Naira daya ba su karba ba. Ai ’yan uwana ma za su fada muku tun bayan kiran farko da suka sanar muna hannunsu ba su sake tuntubar kowa ba.

“Kuma mako bakwai na yi a hannunsu, sai na koka musu cewa lokacin haihuwata ya matso, kuma ni aiki ake yi min, ba na iya haihuwa da kaina. Sai suka zauna suka yi nazari.

“Bayan ’yan kwanaki da suka tabbatar ba zan iya haihuwa da kaina ba, (saboda ba ni ce mai cikin da suka taba kamawa ba, wadansu a baya sun sha haihuwa a hannunsu), sai suka ga wannan ba za su iya ba.

“Sai suka ce min na san dai in don kudi ne, kudina ba za su sa in fita ba, sun duba yanayin da nake ciki sun tausaya, sai suka ga abin da ya fi dacewa shi ne a bar ni in tafi,” inji ta.

Game da yadda suka sake ta kuwa, Thamina ta ce, “Sun nuna min hanya kawai suka ce in bi in tafi.

‘Sakon da suka ba ni in fada wa gwamnati’

“Babban sakon da suka ba mu, mu ba gwamnati shi ne yaransu da aka kama ta sakar musu, wadansu ma a cikinsu suna shan nono aka raba su da mahaifansu, aka kai su gidan marayu.

“To sun ce lallai gwamnati, kamar yadda suka nuna tausayi a kaina, saboda ba na ji sun taba yin haka, ya kamata a ce gwamnati ta saurare su, ta ba su ’ya’yansu da sauran mutane, sun ce ’ya’yansu takwas ne.

“Sun ce in aka sakar musu yara, mu ma akwai yaranmu a hannunsu. In an saki yaran, sai su duba wasu masu rauni a cikinmu, su saki. Sun ce sakin yaran ne zai sa gwamnati ta nuna musu ita ma mai tausayi ce.

“Wannan kuma zai bude kafar tattaunawa a samu mafita,” inji ta.

‘Ni ma a duniya na ji labarin wai na haihu a hannunsu’

Dangane da labarin da aka rika yadawa cewa ta haihu a hannunsu, har ma da hoton jaririn, Thamina ta ce ita ma haka ta ji a duniya.

“Yadda ka ji labari ni ma haka na ji. Ni ban ma san me ake cewa na haifa ba, ko namiji ne ko mace. Muna cikin dajin haka muka ji labarin, ba mu san wa ya kirkiro wannan labarin ba,” inji ta.

Ta ce yanzu haka ta kusa haihuwa. Ta kuma ce ta roke su kan su sako yaran da ke hannunsu da wata tsohuwa mai kimanin shekara 85.

“Ina kira ga gwamnati ta taimaka musu, saboda akwai masu hawan jini, akwai masu rauni, akwai wadanda suka jigata, an zaunar da su sama da wata biyu, to ko ba a taba su ba, hakan zai cutar da kwakwalwarsu.

“Kirana ga gwamnati shi ne ta duba irin dawainiyar da suka yi suka sako ni ba ko sisi, ba wani sharadi, ta yi wani abu a kai.,” inji ta.

Thamina ta ce, “A gaskiya mutannen dajin suna kirana a waya suna tambayata halin da nake ciki. Sukan ce min yaya jikina. Duk bayan kwana biyu sukan kira ni su tambaye ni ko na samu sauki da sauransu. Sukan tambaye ni lokacin da za a yi min aiki da sauransu. Wallahi har nuna damuwa suke yi a duk yayin da suka ji muryata ta canza.”

Malama Thamina ta yi kira ga gwamnati ta farka daga barcin da take tare da kokarin yin abin da ya dace kan matsalar tsaro.

Ta yi kira ga gwamnati cewa batun yaki da ’yan ta’adda ba shi ba ne, inda ta ce sulhu da su zai fi kyau.

“A gaskiya babu maganar yaki a cikin wananan lamari. Magana ce ta sulhu kawai, fada ba ya taba kawo zaman lafiya. Kamata ya yi a zauna da su a yi magana ta fahimta don samun sulhu a tsakani. Muna so su sako mana yaran nan da tsofaffi da mazanmu da suke tsare a hannun ’yan bindigar,” inji ta.

Ta kuma goyi bayan matsayar da ’yan bindingar suka tsaya na neman gwamnati ta amince a yi musayar mutanen da suka kama da wadanda gwamnati ta kama musu a lokutan baya.