✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda na zama ’Yar takarar Mataimakin Shugaban Kasa – Khadija Abdullahi Iya

Khadija Abdullahi  Iya, Mace ce wacce ba ta son a danganta ta da wani yanki na kasan nan, ita dai ta fi son a kira…

Khadija Abdullahi  Iya, Mace ce wacce ba ta son a danganta ta da wani yanki na kasan nan, ita dai ta fi son a kira ta ’yar Najeriya sak. Ta fito ne daga wani babban gida da ake kira Gidan Audu Kwangila. Mahaifinta yana da ’yaýa 18 amma ita kadai ce mahaifiyarta ta haifa. Ita ce Mataimakiyar Dantakarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar Alliance For New Nigeria (ANN) wato Fela Durotoye a zaben Shugaban Kasa da ya gabata. A tattaunawarta da Aminiya, ta yi bayanin abin da sanya ta kafa Kungiyarta ta Agaji mai suna Beyond Mentors da sauran fadi tashi.

 

Ilmi

Na yi karatun Firamare na ne a Legas. A daya daga cikin makarantun unguwar Jakande wato Army Children school. Daga nan sai na wuce Kuramo College amma ina aji na biyu sai aka maida ni Makarantar ’Yan mata ta Gwamnatin Tarayya da ke Bida (FGGC). Bayan na kammala Makarantar gaba da Firamare sai na wuce zuwa Jami’ar Bayero inda na yi karatun Dibulomar Kwarewar aiki a fannin Sadarwa a inda na share watanni 18 a Kano. Bayan na kammala sai na tafi Gidan Talabijin na Kasa wato NTA na Abuja inda na yi aikin sanin Makamar aiki kuma na gama. Daga nan kuma sai na samu gurbin karatun Lauya a Jamiár Abuja inda bayan na gama sai na wuce zuwa Jamiár Jos inda a can kuma na yi Digirina na biyu a fannin aikin Lauya da kuma Dubulomasiyya.

Aiki

Da yake ban koyi komai ba a lokacin da ina aikin yi ma kasa hidima (NYSC) saboda inda aka tura ni ban karu da komai ba a can, shi ya sanya ma bana sanya shi a matsayin wani mataki da na fara yin aiki. Na bata lokaci ne kawai don haka ne ma yanzu duk wani mai yi ma kasa hidima da aka turo don ya yi aiki a Kamfanina ina sa ido in tabbatar da cewa ya samu duk horon da ya kamata . bayan na kammala yi ma kasa hidima sai na fada kasuwanci, na yi kasuwanci da dama saboda dama ni ’Yar kasuwa ce tun ina Jami’a. Ba zan iya kidaya irin sanaóín da na yi ba bayan na kammmala Jamiá domin suna da dama kuma sau da yawa bana cin nasara amma wannan ba wani abu ba ne a wurina saboda nasan dama haka abin yake. Daga nan kuma sai aka bani aiki a Bankin Aso Sabing, na share watanni 18 ina wannan aiki inda daga bisani kuma sai na ajiye aikin saboda iyalina suna bukatata sosai bai kuma bai yiwuwa in bar su saboda ina son yin aiki. A haka na daure na bar aikin saboda kula da iyalin ya fiye mini aiki.

Na fara Digirina na 2 a shekarar da na bar aikin ne sannan kuma sai na rungumi harkar rubutu, na kasance mai yin sharhi a Jaridar LEADESHIP. Sannan na rubuta littafinTatsiniyoyina saboda ina da raáyin cewa ya kamata a samu littattafai na Yara irin na mu na gargajiya a Nijeriya ba wai sai mun dogara ga na kasashen waje ba. Daga nan sai na kafa Kungiyar Beyond Mentors da  mujallata da kuma sauran ayyuka.

 

Ko me ya ba ki kwarin gwiwar kafa Beyond Mentors?

Bayan na bar aiki da Bankin Aso Sabings sai na fara bada shawara ga Yara, wanda haka ya sanya na rinka bin makarantu, wannan kuma shi ne abin da ya bani kwarin gwiwar kafa Beyond Mentors inda kuma ta tsaya da kanta. Na fahimci cewa akwai bukatar yara su san yadda za su zabi irin aikin da suke son yi da kuma abin da suke so su zama in sun girma tun suna a makarantar Firamare. Don haka sai na fara zagayawa makarantu ina fadakar da yara akan yadda za su yi ma kansu zabi.

 

Me ya sanya ba ki ci gaba da aikin Lauya ba?

Tun farko bana son karatun Lauya , mijina ne ya bani kwarin gwiwa cewa in karanta shi saboda shi yana jin yafi mini. Amma ni dama harshen Ingilshi nake son in karanta tun ina yarinya saboda ina da shaáwarsa. Don haka bayan na kamala karatun Lauya sai na dauki takardar shaidar karatun na mika masa tunda dama shi ne yake son in yi wannan karatun. Amma dai duk da haka karatun Lauya ya bude mini idanu sosai akan yadda zan cimma burikana.

 

Mata ba su faye yin suna a fagen siyasa ba, ke mene ne ya ja hankalinki har kika fada siyasa?

Ban taba shaáwar siyasa ba a rayuwata kuma duk wanda ya san ni ya san haka. Saboda haka shigata siyasa abu ne mai ban mamaki a gare ni da kuma wadanda suka sanni. Domin ni ban faye son shiga gaba-gaba ba wajen duk wani abu, na fi son dai komai za ta kasance ina a tsakiya.

 

To me ya sanya kika tsaya takara? Ko kin taba tunanin ki janye daga takarar bayan kin tsaya?

A wurina siyasa kamar kaddara ce, ko a lokacin da aka tsaida ni a matsayin wacce za ta kasance ýar takarar Mataimakiyar Shugaban Kasa sai da mijina ya fada min “kin ga akwai Ýan Arewa da yawa da za su iya zaba don su yi masu wannan mukami, amma sai Allah ya sanya suka zabo ki, saboda haka akwai wani dalili da ya sanya Allah ya sanya aka sanya ki.” Wannan shi ne ya sanyaya mini gwiwa.  Kuma gaskiya ne akwai lokacin da na yi yunkurin janyewa ammma sai wata zuciya ta fada mini ka da in janye don ka da in bawa Mata musamman matasa kunya.

 

Abin da kika fi alfahari da shi a ayyukanki

Abin da nafi alfahari da shi a ayyyukana shi ne idan na ga Yaran da inganta tunaninsu. Misali a duk lokacin da  na yi masu bayanai kan cin zarafin Yara, sai kuma in ga sun rike kuma sun kiyaye. Ina jin dadin hakan saboda ina fatan wata rana za su girma su kuma inganta rayuwarsu da kuma kawo ci gaban kasarmu.

 

Kalubale

Akwai kalubale amma ba sosai ba, sai dai kawai a ce mutane sun dora mini nauyin da ya yi yawa, suna mantawa da cewa ni ma fa mutum ce kamar kowa. Lokacin da aka yi mahawarar ýan takara, sun bani sanarwar mahawarar ne cikin awoyi 24 kuma a lokacin ma ina Naija.  Saboda haka na dawo ranar Alhamis kuma na je na yi mahawarar ranar Jumaá ka ga ba lokacin da zan shirya mata. Mutane suna sa ran za ka san komai da komai amma ai abin ba haka yake ba. Wasu mutane sai su turo maka bidiyon wani Dan siyasa yana Magana sannan su ce wai irin haka za ka yi.  Wasu suna son su ga na yi magana kamar Yadda Fela Durotoye yake yi amma ai ni da shi ba daya ba ne.

 

Ta ya ya kike tafiyar da harkar iyali da kuma aiki?

Ina kokarin in ga na bar wurin aiki da karfe 3pm na yamma in kuma zan je aiki ina zuwa ne wajen karfe 7 na safe don in tabbatar na isa da wuri kuma na dawo gida da wuri. Sannnan kuma bana yin aiki a ranakun Jumaá da Asabar da Lahadi saboda in samu cikakken lokaci tare da iyalina.

 

A Nijeriya ana kashe kudi masu yawa wajen zabe, ke ina ki ka samo kudinki na kamfe?

Mun dan yi wata ýar gidauniya ta ’Yan’uwa da abokanin arziki sannan kuma akwai wadanda suka dauki nauyinmu. Amma ni tun da fari sai nan a fada ma Allah  cewa tunda shi ne ya sanya aka zabo ni to ya taimake ni da kudin da zan yi kamfe din. Haka kuma ýan jamíyyarmu sun taka rawar gani.

 

Ko za ki sake tsayawa takara a zabe mai zuwa na 2023?

Kasan ba ni na yi shawarar tsayawa ba a 2019, Allah ne don haka in ya nufe ni da sake tsayawa sai in tsaya.

 

Ya ya ki ka taso da kuruciya?

Abin shaáwa ne, don na tashi ne a Legas yayin da kuma iyayena suna Kaduna. Na samu kyakkyawar tarbiyya, kuma na sha shagalna saboda an nuna mini gata sa ’in da ina karama.

 

Mene ne ba za ki iya mantawa ba sadda kina Yarinya?

Lokacin ina karama ina zaune ne da  ’Yar ’uwar Mahaifina a Legas, amma ko da yaushe Babana yana yi mini saye-saye kai kace makaranta zan tafi. Kuma akwai wani abu da ya faru da ba zan manta da shi ba wasu abokanin wasanmu suka zo mana ziyara sai suka ce “ai wannan Yarinyar ba wani abu da za ta fada ma Babanta ya yi mata ba tare da ya yi mata ba.” Don haka sai suka fada mini cewa in je in same shi in fada masa cewa ina son cin nama. Ni kuwa sai na je na same shi na fada masa. Washe gari da safe sai ya aika aka sawo mini Saniya aka yanka ta. A cewarsa tilas akwai wani dalili da ya sanya ni na same shi yana barci na fada masa cewa ina son cin nama. Saboda haka da aka soya naman sai ya ce mini to ga shi nan sai ki yi ta cin nama har sai hakoranki sun yi ciwo tukuna. Don haka bayan Annabi Muhammadu ba ni da wani jigo da ya wuce mahaifina.

 

Kasancewarki Uwa fa, ya kike ji?

Ina da ’Yaýa 5 amma dai yara 8 ne a gabana. Tun fiye da shekaru 30 na fara renon yara domin ina rike ’Yar Yayana wanda Injiniyan Zanen gidaje ne. Dana na fari yana karatun Likita ne  na biyun yana karatun Lissafi na ukkun ma yana likitanci ne ga su nan dai dodar kowannensu yana karatu. Don haka ni sai shukura domin kuwa burin kowa ce uwa shi ne ta ga yaranta sun san abin da suke yi.

 

Ta ya ya kika hadu da mijinki?

Na hadu da mijina ne a gidan innata wato Yayar Mahaifiyata. Tun daga wancan ranar ya nanike mini har sai da muka yi aure sadda ina karatu a B.U.K.

 

Me kike so game da shi?

Shi mutum ne mai kirki matuka. Amma abin da na fi so game da shi, shi ne, shi mutum ne mai son yara sosai. Wannan yana faranta mini rai.

 

Wakar da kike so?

Ina son wakokin bege

 

Kayan da ki ka fi so?

Hijabina

 

Wace sutura ce ba za a taba ganinki da ita ba?

Dangalallun kaya

 

Ranar da kike so a cikin mako?

Litinin, saboda ranar aiki ce wacce take zuwa da sabon tunani mai cike da fata da kuma zimma.

 

Wace shawara ce da Mahaifiyarki ta taba ba ki wacce ba za ki iya mantawa da ita ba?

Mahaifiyata a kodayaushe ta kan fada mini cewa ‘kin ga za ki ji mutane suna fada maki cewa mahaifinki ya bar maku gado na dukiya mai yawa. To ka da su rude ki da wannan, ke ma ki tashi ki zage damtse ki nemi naki.’

 

Shawara ga mata matasa?

Su kasance sun yarda da kansu kuma su rinka daukar darasi daga kura-kurensu na baya. Sannan su kasance suna daukar shawara daga mashawarta na kwarai don su cimma burinsu.