✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Naira 100 ta jawo fadan kabilanci a garin Nsukka

Tankiya kan kudin dako ya rikide zuwa rikicin addini da ya haddasa gagarumar asara.

Fadan kabilanci da addini da ya faru a ranar Juma’a 31 ga Oktoban da ya gabata inda wadansu matasa da ake zargin zauna gari banza ne suka far wa al’ummar Arewa mazauna garin Nsukka da ke Jihar Enugu, ya faru ne a kan Naira 100 kacal.

Sarkin Hausawan Nsukka, Alhaji Muhammadu Azaga ya shaida wa wakilinmu cewa Naira dari ce ta jawo rikicin bayan wata yarinya mai suna A’isha ta sayi tumatiri ta dauko dan Keke NAPEP ya kai mata shagonsu.

Ya ce bayan ya kai mata an sauke kayan maimakon ta biya kudin dakon Naira 100 kamar yadda suka yi jinga sai ta ki biya, lamarin da ya haifar da tankiya a tsakaninsu.

A cewar Sarkin an ce da mai Keke NAPEP din ya tsaya a biya shi kudin, amma ya ki karba daga nan ne rikicin ya fara har ya buwaya ya kai wadansu matasa suka yi amfani da wannan dama suka far wa ’yan Arewa suka farfasa shagunansu tare da kwashe musu kadarori.

Alhaji Muhammadu Azaga ya ce “Magana dai magana ce ta wata yarinya mai suna A’isha da dan Keke NAPEP; maganar kudi ce tsakaninsu da mai babur din da ya kawo ta a kan Naira 100. An ce ma za a biya kudin yarinyar ta ki yarda, gaskiya haka ne sanadi”.

Alhaji Muhammadu Azaga ya ce bayan ya dawo daga Obolo (Obolafor) ne ya samu labarin faruwar haka.

Ya ce komai ya wuce ana zaune lafiya wadanda aka lalata musu tebura an tayar da su ana gyarawa, wadansu kuma sun tafi gida, amma na ce su dawo na bude kayana ma yau (Laraba).

Shugabanni sun yayyafa wa rikicin ruwa

Ya ce Shugaban Karamar Hukumar Nsukka, Mista Cosmos Ugwu ya kai musu tallafin shinkafa, sukari da taliyar Indomie.

Ya bayyana cewa rumfunar ’yan Arewa da aka lalata za su kai 100, amma ba zai iya kididdige asarar da aka yi ba saboda wasu shagunan an kwashe kayan ciki an tafi da su.

Sarkin Hauswan ya ce gwamnati ta dauki matakin ba su kariya domin Kwamandan ’Yan Sanda na yankin da shugaban karamar hukumar sun yi kokari “Muna zaune da su kwana ma muke yi da su”, inji shi.

Ya ce shugaban ’yan sanda ya zo daga Enugu, sojoji ma sun yi kokari tare suke kwana da su.

Alhaji Muhammadu Azaga, ya ce babu asarar rai a rikicin sai dai wadanda suka samu raunuka an kai su asibiti wadansu an sallame su wadansu na can, kuma Bishop-Bisho ne suka biya kudin yarinyar gaba daya.

Gwamnati za ta gina masallatan da aka lalata

Sannan ya yi kiran a zauna lafiya da cewa, “Wadanda suke Kudu mazauna Arewa su sani idan wata matsala ta taso muna nan Kudu tana shafar mu, idan kuma daga nan Kudu ta tashi tana shafar mu don haka a zauna lafiya a ci gaba da yin addu’ar Allah ya zaunar da mu da kasarmu lafiya,” inji shi.

A yayin da Shugaban Karamar Hukumar Nsukka Mista Cosmos Ugwueze, ya ziyarci al’ummar Arewar don jajanta musu ya ce Gwamnan Jihar ya bayar da umarnin a sake gina masallatai biyu da masu boren suka kone a Nsukka a ranar Asabar da ta gabata.

Idan za a tuna, matasa ’yan kabilar Ibo sun banka wa Babban Masallacin Nsukka da ke Titin Edem wuta, sannan suka rushe wani masallaci a Mahadar Barracks Junction, lamarin da ya tilasta wa Musulmi ’yan asalin Arewa neman mafaka.

Mista Cosmos Ugwueze wanda ya kai ziyarar ba-zata ga al’ummar Musulmin tare da kansilolinsa a ranar Litinin da ta gabata don duba barnar da aka yi a masallatan biyu, ya ce babu abin da zai yanke tsohuwar alakar zaman lafiyar da ke tsakanin ’yan kabilar Ibo da al’ummar Musulmi a Nsukka.

Ya yi Allah wadai da harin da aka kai ga masallatan biyu da kadarorin Musulmi, inda ya ce sabani a tsakanin mutum biyu bai kamata ta koma ta kai hare-hare a kan Musulmi da wuraren ibadarsu ba.

“Abin da ya faru ranar Asabar da ta gabata abin takaici ne, shekara da shekaru Musulmi da al’ummar Ibo suna zaune lafiya a nan Nsukka.

“Ina tabbatar muku kudirin gwamnati na tabbatar da garin Nsukka ya ci gaba da zama wurin zama mai dadi ga kowa ba tare da la’alkari da addini ko kabila ba.

“Gwamnati za ta sake gina masallatan biyu kuma ta mayar da dukkan kayayyakin da aka sace daga cikinsu,” inji shi.

An yaba wa shugabannin Musulmin Nsukka

Ya yaba wa shugabannin Musulmin Nsukka kan nuna dattako wajen magance lamarin, inda ya ce, “Ina yaba wa salon shugabancinku kan yadda kuka tafiyar da wannan lamari, ku kira mutanenku su dawo su ci gaba da harkokinsu na neman halal ba tare da tsoron za a kai musu hari ko musgunawa ba, domin gwamnati ta shawo kan lamarin”.

Da yake mayar da jawabi, Babban Limamin Babban Masallacin Nsukka, Ustaz Yakubu Omeh wanda ya yaba wa shugaban kan ziyarar da alkawarinsa na hanzarta sake gina masallatan biyu da aka lalata, ya ce harin da aka kai wa masallatan ba zai bata kyakkyawar dangantakar da tsakanin Musulmi da Ibo da ke Karamar Hukumar Nsukka ba.

Shugaban Matasa Musulmi na Nsukka, Ustaz Ibrahim Ugwu, ya yaba wa shugaban ne, inda ya ce ya tabbatar wa al’ummar Musulmin Nsukka cewa zai kare lafiyarsu.

Ugwu wanda shi ne Na’ibin Babban Limamin Babban Masallacin Nsukka ya yaba wa Kiristocin Nsukka wadanda suka boye Musulmi da dama a gidajensu don kare rayuwarsu.