✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Najeriya ta ciyo bashin tiriliyan N2.5 a wata uku

Kawo yanzu bashin da ake bin Najeriya ya haura Naira tiriliyan 38.

Ofishin Kula da Basuka na Kasa (DMO) ya ce Najeriya ta ciyo bashin Naira tiriliyan biyu da biliyan 500 a cikin wata uku a bana.

Ofishin ya bayyana cewa Naira tiriliyan 2.5 din da kasar ta ciyo bashi daga watan Yuni zuwa karshen watan Satumban shekarar 2021 da muke ciki, ya sa yawan basukan da ake bin kasar sun haura Naira tiriliyan 38.

“Alkaluman sun nuna basukan cikin gida da kasashen waje da Gwamnatin Tarayya da jihohi da Birnin Tarayya suka ciyo ya kai Naira tiriliyan 38.005, wato Dala biliyan 92.626;

“Hakan ya faru ne a sakamakon takardun lamunin Eurobond na Dala biliyan hudu da Gwamantin Tarayya ta bayar a watan Satumba,” a cewar DMO.

Sanarwar da ta fitar ta ce Gwamnatin Tarayya da jihohi da Hukumar Kula Da Birnin Tarayya sun ciyo basukan a cikin watanni uku ne baya ga Naira tiriliyan 35.465 da ake bin su kafin nan.

Da yake bayani kan hikumar takardun lamumin Eurobond na Dala biliyan hudu da Gwamnatin Tarayya ta bayar a watan Satumba, ofishin bayyana cewa hakan zai taimaka wajen kara yawan kudaden da ke asusun Najeriya na kasashen waje da kuma kare darajar Naira.