✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Yadda nake kai ’ya’yana daji ’yan bindiga suna lalata da su’

Ta bayyana yadda take kai ’ya’yan cikinta da na ’yan uwanta wurin ’yan bindiga a daji su yi lalata da su.

An cafke wata matar aure da take kai ’ya’yan cikinta da na ’yan uwanta wurin ’yan bindiga a cikin daji inda suke yin lalata da su.

Matar ta bayyana yadda take kai wa ’yan bindiga ’ya’yan nata da ’ya’yan ’yan uwanta ne bayan da rundunar ’yan sanda ta musamman kan yaki da ’yan fashin daji da ’yan ta’adda sun samu nasarar cafke ta tana tsaka da wannan aika-aika.

Wakilinmu ya ruwaito cewa matar tana yi wa ’yan bindigar safarar ’yan mata zuwa Dajin Galadimawa ana aikata alfasha da su.

Rundunar ’yan sandan ta IRT wadda Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya ya kafa, ta titsiye matar inda ta bayyana yadda son zuciya ya rufe mata idanu ta shiga wannan harka.