✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda nasiha ta jawo wa matashi rasa hannu daya a Kano

Ya yanke shi da wuka a kasan hammata, lamarin da ya kai ga yanke hannun.

Wani matashi a Jihar Kano mai suna Salisu Hussaini ya rasa hannunsa guda daya a dalilin nasiha da ya yi wa wani abokinsa mai suna Abubakar Ayuba kan ta’ammali da miyagun kwayoyi.

Likitoci a asibitin kashi na Dala, sun yanke hannun matashin sakamakon rubewa da fara yi bayan sara da wuka da abokin nasa ya yi masa a unguwar Fagge da ke Kano.

A zantawar da Aminiya ta yi da wani dan uwa ga wanda ake yanke wa hannun mai suna Auwal Hussaini ya yi karin haske kan yadda lamarin ya faru.

A cewarsa, “Salisu ya je wajen Abubakar don yi masa fada kan rigimar da suke da wasu da kuma ta’ammali da miyagun kwayoyi da ake zarginsa da yi.

“Shi ne ya yi zuciya ya ciro wuka ya yanke shi a kasan hammata,” in ji shi.

Bayanai sun ce yankan wukar ya yi sanadin rasa hannun matashin, wanda ‘yan uwansa suka koka tare da neman a bi wa dan uwansu hakkinsa.

Ita ma mahaifiyar matashin mai suna Zulaihat Abubakar, ta bayyana cewa danta ba ma’abocin neman fada bane, don ya fi mayar da hankali wajen neman na kansa.

“Lafiya kalau mu ke zaune da iyayen Abubakar a unguwa amma ya yi wa Salisu wannan illa, kullum yarona cikin neman na kansa ya ke baya fada da kowa,” a cewarta

Kazalika, mahaifiyar ta musanta labarin da ake cewa masu kwacen waya ne suka farmaki dan nata.