✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ni da matata muka yi fama da COVID-19

Matar a kwanta bayan mijin ya fara murmurewa, amma nata ya fi tsanani duk da cewa ma'aikaciyar jinya ce

Daga cikin mutanen da suka warke daga cutar coronavirus a Najeriya akwai Gboyega Akoshile da matarsa.

Gboyega Akoshile, kakakin Gwamna Babajide Sanwo-Olu na Legas, ya bayyana irin fadi-tashin da suka yi da cutar har zuwa warkewarsu.

Mun zanta da shi ne washegarin ranar da ya koma bakin aiki (5 ga Agusta, 2020), bayan shafe makonni suna fama da cutar.

— Yadda abun ya fara

Ya ce abun ya fara ne daga alamun zazzabi da ya fara ji a ranar 1 ga watan Yuli, 2020.

“A hanyata ta komawa gida na biya wani kantin sayar da magani na sayi maganin malariya da paracetamol, kamar yadda aka bukata, na tafi gida.

“Daga yammacin 2 ga wata zuwa safiyar 3 ga wata sai abin ya yi tsanani; daga ciwon kai sai na fara jin sanyi da ciwon gabobi.

“A ranar ina da aikin shirya wa maigidana taron ‘yan jarida, amma ban sanar da kowa ba saboda a lokacin kowa na yin nesa-nesa da juna.

— An yi wa kowa a gidan gwajin COVID-19

“Ranar Alhamis da yamma sai na ce wa matata ya kamata a yi mana gwajin COVID-19, na fahimtar da ita bukatar mu tabbatar da matsayinmu.

“Ta fahimce ni, duba da cewa tana iya yiwuwa na dauki kwayar cutar, musamman ganin yadda yaduwar cutar ke karuwa a yankuna”, inji shi.

Jami’in kiwon lafiya dauke da kwalbar samfurin gwajin cutar Coronavirus

Ya ce an yi wa matar tasa gwajin ne a Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa da ke Yaba tare da direbansu, duk da cewa lafiyar direban lau kuma bai nuna wata alama ba.

— Yanayin wahalar da na sha

“Ni kuma cikin ‘yan sa’o’i har alamomin cutar sun bayyana a tare da ni har na firgita, a rayuwata ban taba jin yadda nake ji ba a lokacin.

“Tafiya daga Marina zuwa Ikeja ta zamar min kamar birnin New York na kasar Amurka zani daga Legas. Ba zan iya kwamanta irin radadi da zugin da na ji ranar ba.

“Haka na yi ta juyi a cikin mota, abun da zan iya tunawa kawai shi ne na ji muryar direba yana cewa ‘Allah Ya ba ka lafiya’.

“Ko da muka isa gida idanuna sun koma jawur, na koma kamar mai harara-garke.

“Matata ma’aikaciyar jinya ce, amma firgita. Duk da haka ta yi ta maza ta fara duba ni, ta kuma dage cewa mu tafi asibiti.

“A asibiti na gaya wa likita cewa an yi mini gwajin COVID-19, amma ya ce bari ya kara ba ni magunguna malariya.

“Na sha magungunan ranar Asabar da safe da yamma har zuwa safiyar Lahadi amma ba ta sauya zani ba.

— Bayan fitowar sakamkon gwaji

“Ranar Lahadi da yamma ne sakamakon gwajinmu ya fito wanda aka tura mana ta email.

“Na kadu fiye da tunani da gani cewa dukkanninmu mun kamu da cutar, ni da matata da kuma direba.

“Nan take na kira na sanar da direba. Da alama yana cikin wadanda ba ta yi wa illa domin har yanzu bai nuna wata alamar cutar ba.

“Shi bai ma damu ba, amma duk da haka na matsa cewa ya killace kansa na kwana 14 a gida kar ya harbi wasu”.

Bayan sanin matsayinsa sai ya sanar da Gwamna Sanwo-Olu da kuma Shugaban Ma’aikatan Gidan Gwamnatin Jihar Legas, Tayo Ayinde wanda nan take ya tsara yadda za a kula da lafiyarsa.

— Lokacin jinyar COVID-19 a gida

“Likitoci sun zo suka ce mu killace kanmu a gida suka nuna mana hanyoyin hanayaduwar  cutar.

“Yawancin abubuwan na san su saboda ina cikin masu wayar da kai na kwamiitn yaki da cutar a jihar.

“Cikin kwana biyu suka fara jinya ta gadangadan. A lokacin na daina jin dandano ko kanshi kuma dukkannin alamun cutar sun bayyana a jikina.


“Bayan kwana takwas zuwa tara da fara kula da ni sai damuwa da kuma radadi da ke damu na suka ragu na fara dawowa hayyacina.

“Bugawa jinina da zafin jikina da na’urar SPO2 dina sun koma daidai, har zan iya yin dan aikace-aikace, har daga baya na fara aiki daga gida”.

SPO2 wata ‘yar na’ura ce da ake amfani da ita wajen auna yanayin tafiyar iskar oxygen a jikin mara lafiya

— Da sauran rina a kaba

Ana cikin haka, sai matarsa ta fara nuna alamun cutar daga ranar 5 ga Yuli, aka fara jinyar ta ita ma.

“Yayin da nake samun sauki ita kuma nata sai ya fara tsanani; yanayin shakar oxygen dinta ya sauka kasa da maki 95 da ake bukata.

“A farko abun yana hawa da sauka tsakanin 90 zuwa 94, har yakan kai 95, saboda haka ban yanke kauna ba.

— ‘Mun shiga tashin hankali’

“Bugawar zuciyarta bai daidaita ba, wani lokaci ba laifi, wani lokaci kuma ya sukurkuce.

“Ranar 14 ga Yuli da na ga SPO2 ya nuna kasa da 88,  sai na ce ya kamata a mayar da ita cibiyar kula da masu cutar.

“An kai ta cibiyar Onikan inda ta samu cikakkiyar kulawa irin wadda marasa lafiya ke nema a Amurka”, kamar yadda ya ce.

Daya daga cikin dakunan binciken NCDC inda ake gwajin cutar coronavirus

“Na shiga tashin hankali sosai saboda kwana uku bayan an kai ta sai abun ya tsananta. Ba ta daukar waya, ba ta kira, duk muka kadu!

“Bayan kwana biyar sai muka fara magana da ita ta bidiyo a waya”, inji shi.

Da yake magana game da halin da matarsa ta shiga, Akoshile ya ce, “Yawanci ba COVID-19 ke kashe mutane ba, wasu rashe-rashen lafiya ne ke tsananta matsalar.

— Tana kasa tana dabo

“Ba mu sani ba ashe matata na da cutar nimoniya da kuma matsalar taruwar jini.

“Duk ba a sani ba saboda da farko ba su taba kwantar rashin lafiya ba da farko.

“Kowa a gidan lafiyarsa kalau har zuwa lokacin da aka samu baullar COVID-19.

Wani jami’in kiwon lafiya daga cikin gidan gilashi yana daukar samfuri daga jikin wata mata da ake yiwa gwajin coronavirus a jihar Ogun

“Yana da muhimmanci a rika zuwa ana yin cikakken gwajin lafiya ko da sau daya ne a shekara.

“Da mun san tana da matsalolin tun da farko da tun zuwa likitocin da farko da sun tunkari matsalar kafin ta yi tsanani haka”.

Ya yaba wa gwamnatin jihar da jami’an lafiya da direbansa da suka yi kokari wajen ganin matarsa da sauran marasa lafiya da aka kai asibiti ranga-ranga sun samu kulawa da ta dace.

“COVID-19 ba karya ba ce! A rika sanya takunkumi a rika wanke hannu sannan a rika bayar da tazara tare da kiyaye sauran matakan kariyar cutar”, inji shi daga karshe.