✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ni da ’ya’yana muka tsira daga harin ’yan ina-da-kisa —Ohakim

Maharan sun kai harin ne da nufin kashe tsohon gwamnan.

Tsohon Gwamnan Jihar Imo, Ikedi Ohakim, ya bayyana yadda shi da ’ya’yansa suka tsallake rijiya da baya a harin da aka kashe ’yan sandan da ke tsaron lafiyarsa.

Aminiya ta ruwaito yadda mahara suka kai wa ayarin motocin Ohakhim farmaki a ranar Litinin, suka kashe ’yan sanda da ke tsaron lafiyarsa a Karamar Hukumar Ehime Mbano da ke Jihar Imo.

A tattaunawarsa da kafar TheNiche mai yada labarai ta Intanet, tsohon gwamnan ya ce, “Muna tafiya tsakanin Isiala Mbano zuwa wadannan mutanen suka tare mu.

“Sun kawo mana farmaki ta baya suka dinga harbi babu kakkautawa, na dauka na mutu ina tare sa ’ya’yana — mace da namiji.

“Abin da ya ceci ni shi ne wannan motar sulken; Ina raye a yau ne saboda Ubangiji ya nufa da kuma taimakon motar sulke.

“Sai dai abun takaici shi ne sun kashe mana yara hudu ciki har direbana; Gaskiya ne mun rasa mutum hudu kuma abun ya dame ni. Wane laifi suka yi musu?”

Ohakim, ya ce bayan direbansa ya tsere daga wajen, maharan “Sun bi bayanmu suna harbin tayar motarmu. Ubangiji Ya taimake mu tayar motar tana iya tafiya ko babu iska.

“Tayar ta dauke mu tsawon minti 20 kafin mu iso gida kafin ta sace gaba daya.

“Direban yana da kwarewa sosai, ya dinga musu yawo da hankali har muka bace musu a daidai Mahadar Umuahia, daga nan ya bi wata hanya su kuma suka kasa gane inda muka yi.

“Bayan mun dawo ne gidan gwamnati suka aike da karin jami’an tsaron da suka kawo gawarwarkin yaran nawa da suka kashe.

“Wannan ya fi karfin a ce ’yan awaren IPOB ne gaskiya. Wadannan kwararru ne, sun samu horo sosai. Sun zo a cikin mota kirar BMW. Sun zo da nufin kashe ni ne.”