✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Pantami ya daura auren Yusuf Buhari da Gimbiya Zahra

Alhaji Aminu Dantata ne waliyyi, Mamman Daura kuma uban ango.

Garin Bichi ya yi cikar kwari a yayin da manyan mutane da abokan arziki suka yi dafifi a Fadar Sarkin Bichi, Alhaji Nasir Ado Bayero domin shaida daurin auren ’yarsa, Gimbiya Zahra, da angonta Yusuf Buhari, dan Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Gimbiya Zahra ita ce ’yar Sarkin ta farko da ya aurar bayan hawansa mulkin Masarautar Bichi, wadda ya bayyana cewa zai damu matuka saboda rabuwa da ita, duk da cewa dakin miji za ta.

Daurin auren Gimbiya Zahra da ango Yusuf Buhari ya gudana ne a jajibirin babban bikin da aka shirya mika wa Sarkin Bichi Alhaji Nasir Ado Bayero sandar mulki, wanda zai gudana a ranar Asabar.

Tun da safiyar Juma’a aka girke jami’an tsaro domin tabbatar da doka da oda a Bichi, gabanin isowar mahalarta daurin auren da aka shafe makonni ana tattaunawa a kai, wanda kuma Ministan Sadarwa, Isa Ali Pantami ya jagoranci daurawa.

Malam Maman Daura, wanda dan kawun Shugaba Buhari ne, ya kasance uban ango, a yayin da babban attajiri, Alhaji Aminu Dantata, kuma shi ne waliyyin amarya.

Tsohon Shugaban Kasar Nijar Mahamdou Issoufou da Tsohon Shugaban Kasar Najeriya, Goodluck Jonathan da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar na daga cikin mahalarta daurin auren.

Gwamnoni da sarakuna da ministoci da manyan jami’an gwamnat da attajirai da ’yan siyasa da sauran jama’a na daga cikin mahalarta daurin auren.