✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda Pogba ya cire kwalbar giya a gabansa

Pogba ya kawar da kwalbar giya a gabansa a lokacin taron manema labarai.

Dan wasan tsakiya na kasar Faransa da kungiyar Manchester United, Paul Pogba, ya zama dan wasan kwallon kafa Musulmi na farko da ya kawar da kwalbar giya a gabansa yayin taron manema labarai a Gasar Cin Kofin Nahiyar Turai.

An ga Pogba, wanda Musulmi ne mai ibada sau da kafa, yana kawar da kwalbar giya daga gaban teburin da yake zaune yayin hira da manema labarai kafin wasan farko da Faransa ta buga da Jamus.

Faransa ta samu nasara a wasan na daren ranar Talata da ci 1 da nema a kan Jamus din.

Ga mabiya addinin Musulunci dai giya haramun ne, don haka ake ganin cire kwalbar giyar da Pogba ya yi na da nasaba da rashin goyon bayansa ga tallata kamfanin da ya dauki nauyin gasar.

Hakan da ya yi na zuwa ne bayan da Cristiano Ronaldo  ya nuna tsanarsa ga lemon kwalba na Coca-Cola a yayin hira da manema labarai,  jim kadan kafin wasan Portugal da Hungary, inda ya kawar da kwalaben lemon guda biyu a gabansa.

Ronaldo, wanda a baya ya taba cewa ya tsani ganin dansa yana shan lemukan kwalba ya cire kwalaben na Coca-Cola ne daga teburin da yake zaune inda aka jiyo shi a harshen Portugal yana fadar cewa: Agua ‘Sha ruwa!’

Daga nan an gano shi ya dauko gorar ruwa wacce ya ajiye gabansa har ya kammala hirar da manema labaran yana mai yi wa Coca-Cola kallon kyama.