✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rashin tsaro ke barazana ga Zaben 2023 a Arewa

Kauyuka da dama ba kowa a Neja.

Saura wata takwas a gudanar da zaben 2023, sai dai dimbin matsalolin tsaro da suka hada da ta’asar ’yan bindiga da rikicin kabilanci da na addini da kuma farfadowar kungiyoyin Boko Haram da ISWAP da Ansaru na iya kawo cikas ga Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) wajen gudanar da zabe a daruruwan kauyuka musamman a Arewa kamar yadda Aminiya ta gano.

Jibgin matsalolin tsaro a jihohin Kaduna da Neja da Katsina da Sakkwato da Benuwai da Filato suna iya hana miliyoyin jama’a kada kuri’a a kananan hukumomi da dama a jihohin da ba za a iya isa gare su ba, saboda tashin hankali.

A wasu jihohin ’yan bindiga sun mamaye kauyuka suna juya su, yayin da aka kori wasu daga kauyukan suka koma zama a sansanonin gudun hijira.

Kwararru sun ce matukar Gwamnatin Tarayya ba ta ba sojoji umarnin daukar matakin da ya dace a wasu sassan kasar nan ba, ba za a iya yin zabe a daruruwan unguwanni kauyuka ba.

Mazauna da ’yan siyasa a sassan kananan hukumomin Birnin Gwari da Giwa da suka fi shan wahalar maharan a Jihar Kaduna, sun ce zai yi wuya a yi zabe a wasu kauyukan yankunan biyu saboda rashin tsaro.

Tuni ’ya’yan Kungiyar Jama’atu Ansaril Muslimina Fi Bilad al-Sudan, da aka fi kira da Ansaru, da suka mamaye dajin yankin Birnin Gwari suka yi barazanar hana gudanar da harkokin siyasa a yankin.

Mazauna yankin sun ce akwai unguwanni da kauyuka 60 a Birnin Gwari da ’yan ta’addar suka kore su, yayin da suka mamaye kauyukan mazabu bakwai daga cikin 11 na yankin.

Wani mazaunin Gundumar Kuyallo da ke Birnin Gwari ya ce tuni Ansaru take daukar sojojinta daga kauyukan da suke karkashinta kuma tana ci gaba da wa’azin hana shiga siyasa bisa hujjar ’yan siyasa ba su inganta rayuwarsu.

“Suna kara yawa tare da daukar matasa daga kauyuka kamar Tsohuwar Kuyallo da Unguwar Gwandu da Kwasakwasa duka a Gundumar Kuyallo.

“Abin bakin cikin shi ne wasu daga mutanenmu suna ganin ’yan ta’addar a matsayin masu ceto su daga ’yan bindigadon haka ba a samun turjiya kan hana harkokin siyasar ba,” inji shi.

Ya ce Ansaru na ladabtar da matasa, musamman ’yan acabar da suke lika fostar ’yan siyasa, inda ya yi gargadin cewa matukar ba a dauki mataki cikin gaggawa ba, lamarin zai gagari gwamnatin Najeriya.

Wani basarake kuma dan siyasa a garin Birnin Gwari da ya nemi a sakaya sunansa ya zargi gwamnati da hukumomin tsaro da gaza tunkarar ’yan ta’addar.

Ya ce a matsayinsa na shugaban al’umma a yankinsa akwai sassan da suke karkashinsa da ba zai iya zuwa ba saboda ’yan ta’addar sun kwace su.

“Lamarin ya kazanta inda ’yan jami’an tsaro da aka ajiye a wadannan yankuna ba su iya bin wasu hanyoyin kamar hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari sai da rakiyar jami’an tsaro cikin shiri.

“Wasu lokuta ko da rakiyarsu, ’yan ta’addan kan kai musu hari su kashe su,” inji shi.

Ya ce, babu yadda wani dan siyasa zai iya shiga wadannan yankuna don kamfe kuma INEC ta tura malamin zabe da kayan aiki tamkar ta tura shi a kashe ne.

“Matukar Gwamnatin Tarayya ba ta tsara tare da kaddamar da hare-haren sojoji a daukacin yankunan ba kafin 2023, babu zaben da zai gudana a wadannan kauyuka, don babu wanda zai sa rayuwarsa a hadari, har da ni kaina,” inji shi.

Shehu Hassan, mazaunin Gundumar Fatika a yankin Giwa, ya ce wajibi ne Gwamnatin Tarayya ta lura da yadda Hukumar Zabe ta Jihar Kaduna ta kasa gudanar da zaben kananan hukumomi a wasu kauyukan Birnin Gwari da Giwa a bara, saboda ’yan bindiga sun mamaye su.

A Kudancin jihar fiye da mutum dubu 200 ne aka raba da muhallinsu sakamakon tashin hankali da ayyukan ’yan bindiga a kauyukan kananan hukumomin Kaura da Zangon Kataf da Kauru da Kachiya.

“Ba ma jin za a yi zabe a wasu kauyuka kafin babban zaben badi. Wannan na nufin za a tauye masu zabe da dama,” inji Luka Biniyat Kakakin Kungiyar Mutanen Kudancin Kaduna (SOKAPU).

Danladi Amos na kauyen Dogon Noma a iyakar kananan hukumomin Kachiya da Kaura ya ce tun kai hari a kauyensu wata biyu da suka gabata, mutane da dama sun kaurace wa gidajensu saboda tsoron sake kai musu hari.

“Mutane suna son yin zabe idan gwamnati za ta kare kauyukansu kafin karshen bana,” inji Rabaran John Joseph Hayab, Daraktan Gidauniyar Global Peace Foundation a Najeriya kuma Shugaban Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) ta Jihar Kaduna.

Ya ce kauyukan suna zargin ana yawan kai musu hare-haren ne don a karya musu gwiwa kan zaben 2023.

Kauyuka da dama ba kowa a Neja

Mazauna kauyuka da dama da suke fama da ta’asar ’yan bindiga a kananan hukumomin Neja sun ce da wuya a iya yin zabe mai zuwa yankunan.

Akalla akwai kauyuka da unguwanni 308 a kananan hukumomin Rafi da Shiroro da Bosso da Munya da Mariga da Kwantagora da Magama da Mashegu da Wushishi da Rijau da suka zama kufai saboda yawan kai musu hare-hare.

Sai dai Aminiya ta samu labarin cewa tsaro ya inganta a kananan hukumomin in ban da ta Rafi, inda mutane da dama da suke gudun hijira ba su koma gidajensu ba.

Ta samu labari daga Shugaban Sashin Ayyuka na Hukumar INEC a Jihar Neja, Mohammed Babatunde Yusuf cewa wadanda suka cancanci kada kuri’a daga rumfunan zabe 270 ne aka raba da muhallansu.

Kuma daga wannan adadi, 46 sun fito ne daga kananan hukumomin Munya, 100 daga Mariga, 62 daga Shiroro da 62 daga Rafi.

Wani hakimi a yankin Rafi da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya a watan Nuwamban bara cewa, bisa halin da ake ciki ba ya da tabbacin za a gudanar da zabe a yankin.

“A Rafi lamarin bai gyaru ba, saboda har yanzu mutane da dama ciki har da ni muna zaune ne a wajen garinmu a matsayin ’yan gudun hijira. Ba za mu yi kasadar komawa gida ba, saboda babu jami’an tsaron da za su kare mu,” inji shi.

Wakilinmu ya jiyo cewa a Karamar Hukumar Rafi, Gundumar Kushirke har yanzu tana karkashin ikon ’yan bindigar ne, yayin da mutanenta suke zaman gudun hijira a yankin Birnin Gwari a Jihar Kaduna da Kagara da Pandogari a Jihar Neja.

Wani mazaunin Munya da ya nemi a sakaya sunansa, ya ce zai yi wuya a yi zabe a kauyukan karamar hukumar da dama, inda ya ce har zuwa yanzu ana kai hare-hare a wasu wuraren.

’Yan bindiga na ba mutane umarnin barin kauyukansu a Filato

Binciken Aminiya ya gano cewa a Kudancin Jihar Filato, musamman Karamar Hukumar Wase, zaben na 2023 na fuskantar kalubale daga ta’asar ’yan bindiga.

Haka lamarin yake a wasu kauyukan Karamar Hukumar Bassa da ke Arewacin Filato, inda ake kai wa juna hare-hare a tsakanin Fulani makiyaya da kabilun yankin, lamarin da ya kassara kauyuka da unguwanni da dama.

A ’yan shakarun nan, mazauna Wase karamar hukuma mafi girma a Jihar Filato na fuskantar matsalar tsaro da suka hada da ’yan bindiga da suka ruguza harkokin tattalin arziki da na rayuwa a wasu sassan yankin.

Aminiya ta ruwaito cewa kauyuka da dama da suke harkokin kasuwancin shanu da hatsi duk an kaurace musu saboda ’yan bindiga sun fatattaki mutane inda suka tilasta su neman mafaka a garin Wase da sauran sassan karamar hukumar.

Wani mazaunin Wase, Abdullahi Usman, ya ce mutane sun gudu daga kauyukan Bangalala da Aduwa da Shabindi da Shengem da Tapga da Dogon Ruwa da suke gundumomin Bashar da Kadarko na karamar hukumar.

Usman ya ce halin da ake ciki zai yi wuya zaben 2023 ya gudana a yankunan, matukar jami’an tsaro ba su shawo kan matsalar ba.

A cikin mako guda kauyukan Sabon Zama da Gindin Dutse da Anguwan Tsohon Soja da Anguwan Yuhana da Anguwan Mangu an aike musu takardun gargadi kan su bar kauyukan cikin kwana biyar ko su fuskanci yaki.

Ubale Pinau, mazaunin kauyen Pinau a yankin Wase ya ce wasu mazauna kauyukan tuni sun gudu daga yankin don kauce wa fada da makiyaya.

A Karamar Hukumar Bassa da ke yankin Sanatan Arewacin Filato, Monday Adamu mazaunin Miyango ya ce kauyuka irin su Jebu Miyango da Heek duk an kaurace musu saboda yawan hare-hare.

“Idan tashin hankalin ya ci gaba, babu shakka zai shafi zaben badi saboda babu wanda zai sa kansa a halaka. Idan babu mutanen to wane ne zai shiga zaben?” Ya tambaya cikin damuwa.

Akwai tsoron ba za a iya zabe a sassan Katsina ba

A Jihar Katsina, Aminiya ta jiyo cewa kauyukan da dama da suke kananan hukumomin da lamarin ya fi shafa ba za su iya zabe ba, saboda matsalolin tsaron suna ci gaba.

Misali a Karamar Hukumar Batsari, wani da ya nemi a boye sunansa ya ce, daga cikin mazabu 11, biyu ne kawai za a iya gudanar da zaben cikin natsuwa.

“Baya ga garin Batsari babu wata mazaba da za ta bugi kirjin cewa tana da tsaron da za a yi zaben.

“A zaben kananan hukumomi wasu rumfunan zaben an mayar da su garin Batsari ne don mutane su jefa kuri’a, yayin da sauran ba a iya zuwa gaba daya,” inji shi.

Ya ce wasu sassan garin da wuya mutum ya yi tafiyar kilomita biyu ba tare da haduwa da ’yan ta’adda dauke da miyagun bindigogi ba.

“Muna biyan fansa a nisan da bai fi kilomita uku ba daga nan Batsari, to ka gaya min ta yadda za ka raba kayan zabe. Baya ga haka wa zai ji dadin zuwa rumfar zabe a lokacin da ake garkuwa mutanenmu da dama?

“Wasu har yanzu ba a sake su ba, bayan an biya fansa!” Ya koka.

Haka a Karamar Hukuma Jibiya wani mazaunin yankin ya ce a halin da ake ciki mazabu hudu kacal ne za a iya yin zabe daga cikin 11.

“Baya ga mazabun Jibiya A da Jibiya B da Kusa da kuma Riko, babu wata mazaba da za a samu kashi 30 cikin 100 a yanzu. Wurare kamar Bugaje da Mallamawa gaba daya babu kowa, sauran mazabun kamar Gangara da ’Yangayya da Mazanya da Faru/Maje da Farfaru ba za a samu kashi 30 cikin 100 na mutanensu ba,” inji shi.

Ya ce a mazabar ’Yangayya, Kukar Babangida ce kawai ake da dan zaman lafiya, yayin da a Mazanya, Magamar Jibiya ce za a iya samun sararin yin zaben.

Wani mazaunin Faskari, Abdullahi Musa Faskari ya ce, a mazabu 10 na yankin a hedkwatar karamar hukumar ce kawai mutane za su iya yin zabe cikin natsuwa, yayin da daukacin rumfunan zabe da suke kauyuka babu zaman lafiya, wasu ma babu kowa an gudu.

Haka lamarin yake a galibin kananan hukumomin Safana da Kankara da Danmusa da Sabuwa da Dandume da sauransu.

Mazauna kauyuka a Benuwai za su yi zabe a sansanonin gudun hijira

Akwai tsoron zabe ba zai yiwu a wasu kananan hukumomin Jihar Benuwai ba, saboda matsalolin tsaro.

Ana alkanta hakan da ta’asar Fulani makiyaya da ’yan bindiga da kuma rikicin kabilanci da suka sa mutane guduwa daga daruruwan unguwanni da kauyuka masu dimbin masu kada kuri’a a kananan hukumomin Guma da KatsinaAla da Gwer ta Yamma da Logo da Kwande da Ado da Ukum da Okpokwu da Agatu da Konshinsha da Oju da sassan Makurdi.

Wadanda aka raba da muhalli suna zaune ne a sansanonin gwamnati ko rumfuna a sassan jihar.

Wani mazaunin yankin Guma, Jonah Ortese ya ce lamarin ya yi muni saboda ci gaba da kai sababbin hare-hare da ke raba mutane da muhallinsu a kusan kullum.

“Katuna zabenmu sun bace. Ina da tabbacin mutane da dama daga cikinmu ba za su yi zabe mai zuwa ba,” inji Ortese.

Sai dai wani basarake a yankin Logo, Cif Joseph Anawah ya ce tsaro ya inganta a yankinsa inda ya ce za a iya yin zaben 2023 in aka ci gaba da haka.

Mun yi tanadi ga ’yan gudun hijira —INEC

Duk da tsoron da ake nunawa, Hukumar INEC, ta ba da tabbacin cewa babu dan gudun hijirar da za a hana shi kada kuri’a a zaben na badi.

Kwamishinan INEC na Kasa Mai Kula da Labarai da Ilimantar da Masu Zabe, Barista Festus Okoye ne ya bayyana haka, inda ya ce akwai tsare-tsare na ba ’yan gudun hijirar damar yin zaben mai zuwa.

Rahotanni daga Lami Sadik da Mohammed I. Yaba da Ahmed Ali (Kaduna) da Hope Abah Emmanuel (Makurdi) da Ado Musa Abubakar (Jos) da Abubakar Akote (Minna) da Tijjani Ibrahim (Katsina)