✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda rashin wutar lantarki ke durkusar da masana’antu a Kano

An rufe yawancin masana’anatu, masu kananan sana’o’i na kokawa, masu masana’antu na samar wa kansu mafita

A yanzu haka Jihar Kano ta kara shiga matsanancin rashin wutar lantarki, kasa da wata biyu bayan Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na KEDCO da ke samar wa jihohin Kano da Katsina da Jigawa ya yi karin kudin wutar lantarkin.

A watan Mayu ne Gwamnatin Tarayya ta sahale wa kamfanonin rarraba wutar lantarki, ciki har da KEDCO, su kara kudin lanatrakin a sirrince, abin da ya tada kura a kasar nan, bayan kafafen watsa labarai sun bankado lamarin.

Ko a baya da Gwamnatin Tarayya ta yi karin farashin, ta ce hakan zai sa a samu wadatar wutar lantarki a Najeriya.

Sai dai kuma matakin ya zama gara jiya da yau ga al’ummar jihar, inda aka samu karuwar matsalar kuma hakan ya durkusar da kamfanoni da kasuwanci da kuma sana’o’i manya da kanana da dama; musamman masu bukatar wutar irin masu yin kankara da ruwan sanyi da adana danyen nama ko kifi da sauransu.

Kan haka ne Aminiya ta zaga don gane wa idonta halin da matsakaita da kananan sana’o’i ke ciki a Jihar Kano da yadda suke gudanar da harkokinsu a wannan yanayi na rashin wutar lantarki, ga kuma tsadar man fetur da iskar gas da dangoginsu.

A unguwannin masana’antu na Sharada da Dakata, Aminiya ta iske layuka da dama na kamfanoni baki daya sun daina aiki, a wasu layukan kuma akwai ’yan kalilan da ba su fi uku ba da ta samu suna aiki.

Wadanda ta riska suna aiki da dama sun rage yawan aikin da suke yi, ko sun rage kwanakin aikin, ko kuma ma’aikata.

Aminiya ta gano cewa hatta masu sayar da abinci da ruwan sha da ke kai-komo sun ragu matuka a wuraren.

A wani layin ta iske wani babban kamfani na aiki kuma yana samun wadatacciyar wutar da ba ta rawa, amma ba KEDCO din ke ba shi ita ba, kamfanin ne ya samar tun kafuwarsa, kamar yadda shugaban wurin ya bayyana.

Matsakaitan sana’o’i:

Shugaban Kungiyar Masu Masana’antu ta Jihar Kano, Alhaji Hussaini Saleh, ya ce samun tsayayyiyar wutar lantarki ita  ce kashin bayan kowace sana’a da ke son dorewa, don haka rashin wutar lantarkin da ita ce mafi araha a Najeriya ya durkusar da fiye da kashi 60 cikin 100 na masana’antun da ke jihar.

Ya ce a baya iskar gas ke biye wa wutar lantarki wajen araha, amma yanzu ita ma ta yi tsadar da kamfanoni sun gwammace su sayi fetur duk tsadarsa su yi ayyukansu da shi.

“Duba farashin man dizal yadda ya yi ninki uku na kudin wutar lantarki, daga lita daya a kan Naira 200 zuwa Naira 700, gaya min yadda masu karamar sana’a za su samu riba idan suka yi aiki da shi?

“Mun samu labarin yadda wasu daga cikin kamfanonin suka dawo yin rabin aikin da suke yi a da, wasu kuma kashi 25 kawai za su iya yi, wasu ma sun durkushe ke nan har abada, duk saboda tsadar wadannan sinadaran,” inji shugaban.

Ya ce a baya tsadar farashin Dala ce ke wahalar da su kuma duk da ta sake tsada daga Naira 400 zuwa Naira 700, yanzu abin ya taru ya cude da na tsadar wutar lantarki da gas da man fetur; wanda dole al’umma su gani a farashin abubuwan da suke saye.

Shugaban ya kuma ce wannan matsala tun kafin ta kai haka ta sa jihohin Arewa, musamman Kano da Jigawa da Katsina ba su iya gwada kwanji da masana’antun da ke Kudancin Najeriya irin su Legas da Enugu, balle a kai ga sauran yankin Afirka.

Ya ce, “Dalilin da na fadi haka shi ne, jihohin Legas da Enugu na samun wutar lantarki ta gas a kan Naira 42, mu kuma a nan a kan Naira 70 ne.

“Idan ka duba, a Kano a wata muna biyan kudin lantarki Naira miliyan 60; Kamfani mai girma irin namu, mai aiki irin namu kuma a Kudu na biyan Naira miliyan 18.

“To, ka lissafa wannan kudi a shekara ka ga nawa zai ba ka? Kuma wannan a farashin wutar lantarki ne da ta fi kowace araha ma.”

Shi ma dai Ibrahim Bashir Nasambo da ke da masana’antar sarrafa roba da mai a Unguwar Sharada, ya ce babbar matsalar da suke fuskanta ita ce injinansu na bukatar wutar awa uku kafin su dauki zafin da za su fara sarrafa robobi.

“Don haka a duk lokacin da aka dauke wuta kafin awa ukun, aikinsu ya koma baya, kuma wutar nan da kati take lissafi, don haka ya zamo musu asara ke nan.

“Wani kalubalen da muke fuskanta kuma shi ne tsadar kayayyaki ta kowace fuska; ga tsadar wutar lantarkin bayan ma rashin ta, ga tsadar mai a Najeriya,” inji shi.

Shi ma wani mai masan’antar sarrafa robobi a Unguwar Dakata, Muhammad Kabir, ya ce su a yanzu sun daina kukan rashin samun riba, kokarin biyan albashin ma’aikatansu suke yi da kuma yadda za su samu hanyar ci gaba da gudanar da kamfanonin da kuma hanyoyin samun wutar lantarki mai karko.

Ya ce babban abin da ke ci musu tuwo a kwarya a yanzu shi ne yadda za su sayi fili da kudinsu, su kuma sayo turakun wayoyin lantarki su dasa, kawai sai Kamfanin KEDCO ta ba wa wasu dama su ja wuta ta jiki, kuma sun fara samun kudin shiga ta nan ke nan.

Masu kananan sana’o’i

Mun tattauna da wasu mata da muka tarar suna sayar da abinci a unguwar masana’antu ta Dakata, domin jin yaya ciniki yake, musamman a yanzu da masana’antun yankin ke durkushewa.

“Cinikin nan fa ba kamar da ba, harkokiinmu sai durkushewa suke yi saboda kamfanoni da masana’antun da ke ta rufewa.

“Kin ga shekaruna bakwai da fara sayar da abinci a wajen nan kuma a lokacin ana samun ciniki sosai, nakan yi cinikin kusan Naira dubu goma a rana, amma yanzu ba na iya sayar da taliya leda daya.

“Kin gani da idonki ga rabin a mazubi ga kuma rabi na leda a ajiye,” inji ta.

Wata mai sayar da kosai da ke makwabtaka da mai abincin ta ce, “Kamar yadda kika gani kosai nake sayarwa a wajen nan kusan shekara goma ke nan.

“Yawancin masu masana’antun nan a wurina suke sayen abinci.

“A baya na samu kudin da na yi wa kaina da ’yan uwa da abokan arziki alheri da wannan sana’a, amma yanzu na fara tunanin dainawa saboda kudina ba sa fita balle a kai ga maganar samun riba.”

Ta ci gaba da cewa “Komai ya yi tsada, daga kayan abincin zuwa kudin mota, ga babu ciniki saboda rashin masu saye.”

Masu masana’antu

Shugaban Kungiyar Masu Masana’antu ta Jihar Kano, Alhaji Hussaini Saleh, ya ce suna fata a samu gyara a bangaren wutar lantarki nan ba da jimawa ba.

Ya ce idan ma hakan bai samu ba, suna fatar samun sauki da zarar an kammala aikin bututun iskar gas na Ajaokuta zuwa Abuja zuwa Kaduna zuwa Kano (AKK), wanda Gwamnatin Tarayya ta kaddamar shekara uku zuwa hudu da suka gabata.

Ya ce idan aka samu hakan, masana’antu da dama za su samu ragin asarar da suke yi da kusan kashi 40 cikin 100.

Shi ma Alhaji Ibrahim Nasir na masana’antar robobi da ke Sharada ya ce duk da cewa sun sha magana da gwamnati da sauran masu ruwa-da-tsaki irin su Ma’aikatar Kasuwanci da Masana’antu ta Jihar Kano ba tare da samun wani sauyi ba, sun zauna da KEDCO sun koka musu kan suna bukatar wutar awa 12 mafi karanci, ba wai awa ukun da ake ba su ba a yanzu.

To sai dai ya ce har yanzu ba su ga komai a kasa ba kan maganar.

A nasa bangaren, Alhaji Muhammad Kabir na Dakata, rokon gwamnati ya yi ta samar musu tituna masu inganci da kuma ingantattar wutar lantarki, tare da rage musu farashinta, domin samun saukin durkushewar da masana’antun ke famar yi.

Shi ma wani mai tireda ya ce ya fara harkar ce sanadiyar rufe masana’antar da yake aiki a Dakata, sai dai ya ce babu wani ciniki.

Don haka ya roki ’yan siyasar jihar su karkatar da akalar kudaden da suke samu zuwa farfado da masana’antun domin hakan zai rage rashin aikin yi ga matasa da rage matsaloli a jihar.

“Da za su rika sayen masana’antun ko ba za su tallafa musu ba, ai kudin dai aljihunsu zai dawo kuma a lokaci guda sun dauki matasa aiki, dubi yadda suka rika sayen fom din takara na miliyoyin Naira.

“Dubi kuma wadanda ake tuhuma da satar biliyoyin Naira na al’umma.

“Da a ce masana’antu da ASUU suka bai wa kudin ai da tuni an wuce wurin,” inji shi.

Dalilin karancin wutar lantarki a Kano

Cikin wata sanarwa da kamfanin KEDCO ya raba wa manema labarai, ya ce rashin wuta a jihar ya faru ne sakamakon karancin iskar gas daga bangaren da ke samar da wutar lantarki na kasa.

Kamfanin KEDCO ya ce hakan ne ya sa aka rage wutar da ake bai wa kamfanin domin ya rarraba ga jihohin Kano da Jigawa da kuma Katsina.

Sanarwar da Shugaban Sashen Sadarwa na kamfanin, Alhaji Ibrahim Sani Shawai ya sanya wa hannu ta ce yanzu haka ana ba su Megawatt 120 ne daga Megawatt 368 din da ake ba su a baya.

Hakazalika ya ce ragin Megawatt 248 da aka samu ya sa masana’antun da ke jihohin uku suke fuskantar wannan matsala.

A karshe kamfanin ya ce al’ummar jihohin su kara hakuri, domin kamfanin na hada gwiwa da Babban Bankin Najeriya (CBN) wajen tabbatar da mutane sun ci moriyar kudaden wutar da suke biya.

To sai dai yayin hada wannan rahoto, sassan kasar nan da dama na fama da rashin wutar lantarkin tun daga ranar 12-6-2022, sakamakon lalacewar wani daga cikin dirkar kamfanin na kasa da ke ba da wutar lanatarki, kamar yadda kamfanin ya ba da sanarwa.

Wannan matsala dai karo na hudu ke nan a cikin shekara daya ana samun ta.