✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rashin yarda ke shafar kasuwanci —Shugaban bankin Sterling

Shugaban bankin Sterling ya ce rashin amana na kawo cikas ga kasuwanci

Shugaban bankin Sterling Bank, Abubakar Suleiman, ya bayyana rashin amana a matsayin babbar matsalar da ke kawo nakasu ga ci gaban kasuwar kayayyaki a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne a jawabinsa ga taron shirin SABEX, wanda ke bunkasa hadahadar kaya ta fasahar Blockchain. Taken taron da aka gudanar ta intanet shi ne: Kayayyakin noma a matsayin haja masu samun karbuwa.

Shirin SABEX na cinikayyar kayan noma na kawo mu’amalar kasuwanci tsakanin manoma da masu dakunan ajiya da cibiyoyin kudi da sauran masu ruwa da tsaki a harkar noma a Najeriya.

An tsara SABEX ne ta yadda ’yan kasuwa manoma na iya jinginar da amfanin gonarsu da ke ajiye a matsayin kadara domin karbar rancen bunkasa kasuwancinsu.

Suleiman ya ce manufar taron ita ce samar da yarda a kasuwar kayan gona, saboda yanzu yarda ta yi karancin a bangaren, tsakanin manoma, kananan ’yan kasuwa, da masu fitar da kaya kasashen waje da sauransu.

Ya ce yana da muhimmanci a samu yarda a bangaren biyan kudi, hadin gwiwa, hajoji, farashi, jigila, da sauransu.

“Akwai bukatar samar da kudade a bangaren kamar bangaren kadarorin zamani,” inji shi.

Babban Daraktan ya jaddada bukatar fadadawa da inganta kasuwancin kayan gona ta hanyar samar da ingantattun amfanin gona da kasuwarsu, tare da sauya tsari da kuma karfin jari a bangaren.

Ya ce SABEX na da nufin samar da yarda da kuma saukake kasuwancin amfanin gona, ta yadda hulda za ta yi sauki tsakanin manoma, masu saye, masu kudi, masu gudanar da dakunan ajiya da sauran masu harkar kasuwancin kayan noma a Najeriya.

A jawabinsa na bude taron, Dokta Adedoyin Salami, wanda malamin jami’a ne kuma mamba a Makarantar Kasuwanci ta Legas, ya ce noma babban bangare ne, shi ne kuma ya dauki kashi daya bisa hudun tattalin arzikin Najeriya.

Ya ce kasuwar kayayyaki ta kunshi harkar makamashi da karafa da noma da kiwo da kuma kudaden cryptocurrency.

Salami, wanda masani ne kuma mai ba da shawara kan tattalin arziki, ya ce duk da nakasun da bangaren noma yake samu, amma har yanzu yana samar da kaso mai tsoka na ayyuka —a tsawon shekaru, duk kuwa da illar da annobar COVID-19 ta yi wa tattalin arzikin Najeriya, ya rika samum koma-baya na wata shida a jere a 2020.

Babban mai jawabin, wanda mamba ne a Kwamitin Taron Tattalin Arzikin Najeriya (NESG) kuma Shugaban Majalisar Ba da Shawara kan Tattalin Arziki na Gwamnatin Tarayya (EAC), ya ce hajojin da Najeriya ke samarwa za su iya gogayya da takwarorinsu na duniya, duk da cewa Najeriya ba ta kai wasu kasashen ba cigaba.

Ya ce a matakin duniya kuma akwai babbar dama ta zuba jari a abubuwa na zahiri a Najeriya, musamman bangaren ajiyar kayan gona da ban ruwa, saboda yawancin noman da ake yi a kasar yanzu na damina ne kuma sai lokaci zuwa lokaci.

Ya ce harkar noma na iya yin tasiri matuka ga Najeriya ta bangaren hadahadar kudade, inganta samuwar abinci, rage talauci, samuwar kudade, fadada hanyoyin samun kudaden shiga, da kuma rawar da hukumomi za su taka wajen tabbatar da gaskiya, karfin jari, daidaita tsare-tsare, da hulda da masu ruwa da tsaki, karfafa kirkire-kirkire da sabunta dokoki don dacewa da zamani da kuma tsarin duniya.

Shi kuma Mataimakin Shugaban Hulda da Gwamnati na kamfanin Olam, Ade Adefeko, ya bayyana saba alkawari, rashin amana, da rufa-rufa a matsayin matsalolin da ke kawo nakasu ga kasuwanci a Najeriya.

Ya ce akwai bukatar tsinkaya, daidaita farashi da kuma yin gyara a kasuwar kayan gona.

A cewarsa, duk da cewa akwai dama mai yawa a bangaren, ana bukatar tsara kasuwar ta yadda kayan manomi za su samu farashi mai kima a lokacin da ya dace.

Manajan Darakta kuma shugaban kamfanin AFEX Commodities Exchange Limited, Ayodeji Balogun, ya ce Najeriya na samar da kimanin tan miliyan 28 na hatsi a duk shekara, amma tan miliyan 1.4 ne kawai take iya adanawa, wanda mako biyu kacal zai iya yi mata. Amma kasashen Afirka ta Kudu da China na iya adana abin da suka noma 100%.

Ya ce karancin wurin ajiya ya sa duk lokacin da aka samu matsala a kan hanya tsakanin yankin Arewa da Kudu, kamar yadda COVID-19 ta sa aka sanya dokar kulle bara, sai farashin abinci ya tashi.

Don haka ya ce samar da rumbunan ajiya a sassa daban-daban na Najeriya zai taimaka wajen magance matsalar.

Shugabar Kayayyakin Kasuwanci ta FMDQ, Jumoke Olaniyan, ta ce duk da cewa akwai gyara wurin inganta kasuwanci a Najeriya, gyaran da aka yi wa musamman Dokar Kamfanoni da Dangoginsu wadda ta fayyace sha’anin rance da hajojin kasuwar hadahadar kudade ta Najeriya, ya ba da aminci ga amfani da kayan rance a matsayin kadara, wadda ke da wuyar karyewa.

Ta ce bayansu, akwai wasu ka’idoji da Hukumar Hadahadar Hannun Jari (SEC) ta fitar, kamar ka’idojin kasuwar kwastomomi, jingina, da sauran tsare-tsare.

Olaniyan ya ce akwai bukatar zuba jari sosai don bunkasa kasuwanci, kuma kasuwar ainihi ta irin wadannan kayyayaki ita ce kasuwar hannun jari.

Ta ce a fahimtar FMDQ, samar da rance zai taimaka wa kasuwancin kayayyaki har ya haifar wasu rassa.

Dakta Tayo Aduloju, Babban Darakta, Manufofin Jama’a da Ci gaban Cibiyoyi a Kungiyar Tattalin Arzikin Najeriya (NESG) ne ya jagoranci zaman.