✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rasuwar Bankaura ta girgiza Kannywood

Ban taba ganin inda aka yi hayaniya da shi ya daga murya ba.

A ranar Talata da ta gabata ce Allah Ya yi wa fitaccen jarumi a Masana’antar Kannywood, Umar Malumfashi rasuwa.

Marigayin wanda aka fi sani da Bankaura ko ‘Yakubu Kafi Gwamna’ a cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango ya rasu ne bayan fama da ya sha da rashin lafiya.

Marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke Unguwar Hausawa bayan Masallacin Murtala da ke Kano a Yammacin ranar Talata bayan sallar Magariba.

Tijjani Faraga, daya daga cikin manyan jaruman Kannywood da ya ziyarci mamacin a lokacin yana jinya ne ya tabbatar wa da Aminiya hakan.

“Ya kwanta jinya a asibiti kusan sau uku, kuma da yake cutar ba ta tashi ba ce ita ce ajalinsa.

Yadda ya samo sunan Bankaura

Aminiya ta samu labarin cewa ya samo sunan Bankaura ne tun lokacin da yake karatu a Makarantar Sakandiren Government Day Secondary School, Malumfashi inda tun a lokacin suke gudanar da wasanni na ban dariya.

Ya kasance jigo a wasannin da ake gudanarwa a makarantar, wadanda dalibai ne gudanarwa karkashin jagorancin malamai.

Tsohon Kwastam ne

Haka kuma marigayin tsohon ma’aikacin Hukumar Kwastam ne kafin rasuwarsa.

Sai dai Aminiya ba ta samu gamsasshen bayani ba kan ko ritaya kafin rasuwarsa ko bai yi ba.

Ta’aziyya

Da yake bayyana yadda ya kaku da rasuwar mamacin, fitaccen marubuci Nazir Adam Salihi ya rubuta cewa, “Innalillahi wa inna ilaihirraji’un.

“A 1998 na fara aiki da shi a wani fim da na shirya na kuma rubuta mai suna “Naira Da Kwabo”

“Tun daga wannan rana muke ta ayyukan alheri kama daga kan wasannin kungiyoyin wasan kwaikwayo zuwa ga fina-finai masu gajeren zango har zuwa fim dinmu Mai dogon zango na Arewa 24, wato Kwana Casa’in.

“Ban taba ganin inda aka yi hayaniya da shi ya daga murya ba.

­Mutumin kirki na kowa, Allah Ya jikan Yahya Malumfashi. (Kafi-Gwamna/ Bankaura)”