Daily Trust Aminiya - Yadda rikici ya yi awon gaba da masu zaben Sarkin Kano
Subscribe

Yadda rikici ya yi awon gaba da masu zaben Sarkin Kano

Kalubalen da ke gaban kwamitin sulhu

Rikicin da ke faruwa a tsakanin Masarautar Kano da bangaren Gwamnan Jihar, Dokta Abdullahi Ganduje na ci gaba da jan hankalin al’ummar Najeriya, inda ya kai dattawan Arewa da fadar Shugaban Kasa shiga cikin lamarin.

Wannan yana tasowa ne bayan da sababbin sarakunan da aka kirkiro suka warware rawunnan wadansu daga cikin manyan hakiman tsohuwar masarautar da suka koma karkashinsu, wadanda hudu daga cikinsu su ne masu zaben Sarkin Kano da suka hada da Madakin Kano, Hakimin Dawakin Tofa, Alhaji Yusuf Nabahani da Makaman Kano, Hakimin Wudil, Alhaji Abdullahi Sarki-Ibrahim da  Sarkin Dawaki Mai Tuta, Hakimin Gabasawa, Alhaji Bello Abubakar da kuma Sarkin Ban Kano, Hakimin Dambatta, Alhaji Mukhtar Adnan da masarautun Bichi da Gaya suka yi .

Masarautar Kano dai tana daya daga cikin manyan masarautu ba ma a Najeriya kadai ba, a daukacin Afirka ta Yamma, saboda dimbin jama’ar da take da su da kuma karfin tattalin arzikin jama’arta.

Hedkwatar masarautar wato birnin Kano ya kasance cibiyar kasuwanci a Arewa da Najeriya da Jamhuriyyar Nijar.

An yi sarakunan Habe sama da 40 kafin Fulani suka karbi mulki a 1805 inda Sarki mai ci a yanzu Muhammadu Sanusi II ne Sarki na 14 a jerin Fulani bayan da ya gaji marigayi Ado Bayero a shekarar 2014 wanda kuma shi ne mahaifin Sarkin Bichi na yanzu, Aminu Ado Bayero.

A lokacin Jamhuriyya ta Biyu, tsohon Gwamnan Jihar Kano marigayi Alhaji Abubakar Rimi ya kirkiro karin masarautu, amma zuwa gwamnatin marigayi Alhaji Sabo Bakin Zuwo sai ta rusa su. Daga nan ba a sake tado batun ba, sai a bana, inda a farkon watan Mayu, Gwamna Abdullahi Ganduje ya sanya hannu a kan dokar kirkiro masarautun Bichi da Gaya da Rano da Karaye, bayan Majalisar Dokokin Jihar ta kafa dokar haka.

Ana kirkiro masarautun takaddama ta kaure inda masu zaben Sarkin Kano hudun suka garzaya kotu, kuma a cikin watan Yuni, kotun ta soke dokar majalisar.

Hakan ya tilasta gwamnatin jihar sake gabatar da kudirin dokar  kirkiro sababbin masarautun ga majalisa wadda ta sake zama ta amince da ita, kuma Gwamna Ganduje ya sanya mata hannu.

Rikicin gwamnati da Fadar Kano ya kara dagulewa bayan Babbar Kotun Jihar Kano a karkashin Mai shari’a A.T. Badamasi ta yi watsi da bukatar masu zaben Sarkin Kano na ta hana sababbin sarakunan da aka kirkiro ci gaba da aiki, kafin a kammala shari’a kan karar da suka kai gaban kotu.

Sannan sulhu a tsakanin bangaren Gwamna da Sarkin Kano ya kara dagulewa bayan da bangaren Gwamnan ya shimfida wasu sharudda da ya ce sai an bi sannan sulhu zai tabbata, kuma daga cikin sharuddan har da cewa lallai Sarki Sanusi II ya bai wa Gwamna Ganduje hakuri.

Haka aka ci gaba da zaman doya da manja a tsakanin bangaren Gwamna da Masarautar Kano, duk da cewa wadansu manyan sarakuna da fitattun ’yan Najeriya daga ciki da wajen jihar sun yi ta kokarin sulhunta bangarorin biyu.

Kuma rigimar ta kai wannan batun na neman zama babbar barazana ga tsaro a jihar.

Manyan hakiman Kano da rikicin ya yi gaba da su

A tsakiyar watan jiya ne rikicin ya ci wadansu manyan hakimai kuma masu zaben Sarkin Kano bayan da Mai martaba Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauke hakimai biyar da suka ki yi masa mubayi’a, wadanda biyu daga cikinsu masu zaben Sarkin Kano ne. Hakiman da aka cire sun hada da Sarkin Bai Hakimin Dambatta Alhaji Mukhtar Adnan, daya daga masu zaben Sarkin Kano, wanda ya zama hakimi a 1954, abin da ya sa ya fi kowane hakimi dadewa a Masarsutar Kano, inda ya shafe shekara 64 yana hakimci kafin a sauke shi. Yana daga cikin wadanda zabi sarakuna uku wato marigayi Sarkin Kano Muhammadu Inuwa da marigayi Sarkin Ado Bayero da Sarki Muhammadu Sanusi II. Sai Barden Kano Hakimin Bichi Alhaji Idris Bayero, wanda uba yake ga Sarkin Bichi Alhaji Aminu Ado Bayero da Madakin Kano Hakimin Dawakin Tofa Alhaji Yusuf Nabahani wanda shi ne Shugaban Masu Zaben Sarkin Kano da Matawallen Kano Hakimin Minjibir, Alhaji Aliyu Ibrahim Ahmed da kuma Hakimin Tsanyawa Alhaji Sarki Aminu.

Sarkin ya maye gurabunsu da Alhaji Abdulhamid Ado Bayero Hakimin Bichi da Alhaji Mu’awiyya Abbas Sanusi, Hakimin Tsanyawa da Dokta Abdullahi Maikano Rabi’u, Hakimin Dawakin Tofa da Alhaji Wada Ibrahim, Hakimin Dambatta da Malam Isma’il Sarkin Fulani, Hakimin Munjibir, sai kuma Alhaji Labaran Abdullahi, Hakimin Makoda

Biyu daga cikin hakiman da aka cire wato Madaki da Sarkin Bai na cikin mutum hudu da suka shigar da karar Gwamnan Jihar Kano kan sababbin sarakunan da aka nada a kotu, suna kalubalantar kirkiro sababbin masarautu inda suka nemi kotu ta hana wadanda aka yi kara sauke su daga mukamansu ko daukar wani mataki da zai taba aikinsu na masu zaben Sarkin Kano.

Masarautar Rano ma ta sallami hakimanta 6 daga cikin 10 da take da su da suka hada da Hakimin Tudun Wada da Doguwa da Kura da Garun Malam da Takai da  Bebeji.

Sai Masarautar Gaya da ta sallami hakimai biyar da suka hada da Hakimin Wudil Alhaji Abdullahi Sarki-Ibrahim da na Gabasawa Alhaji Bello Abubakar, dukkansu  masu zaben Sarkin Kano. Sauran su ne Hakimin Warawa da na Dawakin Kudu da na Garko. Masarautar Karaye ta sallami hakimai biyu, na Rimin Gado da na Kiru.

Yadda kan Kanawa ya rarrabu

Kirkiro sababbin masarautun ya raba kan Kanawa inda aka samu kafuwar wasu kungiyoyi biyu da suka hada da Kungiyar Masu Kare Muradun Kano (Kano Concern Citizens Initiatibe) a karkashin jagorancin Alhaji Bashir Othman Tofa da wadansu malaman jami’a da na addini da suke adawa da kirkiro sababbin masarautun. Hujjojin da akasari suke kafawa sun hada da yadda yin hakan zai kawo rarrabuwar kawuna da rashin jituwa a tsakanin mutanen jihar da suke da addini da al’ada da da harshe iri daya. Kuma sun ce ko Bature da ya ci Kano da yaki, daya daga cikin yarjejeniyar da aka yi da shi, shi ne ba za a raba Kano ba.

Yayin da Kungiyar Kano Concern Citizens Initiatibe take adawa da kirkiro masarautun, sai wata kungiya da ta kira kanta da Kungiyar Kanawa Masu Mutunci, (Kano Integrity Forum-KIF) a karkashin jagorancin Farfesa Abdu Salihi, tsohon kwamishina a gwamnatin Malam Ibrahim Shekarau ta bayyana, inda ta shaida wa duniya cewa tana goyon bayan kirkiro masarautun da aka yi a jihar.

Kungiyar ta ce, masu adawa da kirkiro masarautun suna ina a 1991, aka yi wa Masarautar Kano ayaga ta hanyar tura wadansu hakimai da ke cikin Masarautar Kano zuwa Jihar Jigawa ta yau inda suka zama Masarautun Dutse da Ringim?

Kungiyar ta kuma ce kirkiro masarautun zai samar da ayyukan yi ga dimbin matasan jihar, kuma sababbin masarautun za su ba da dama wajen kara bude yankunan karkara su samu bunkasar abubuwan more jin dadin rayuwa irin su asibitoci da manya da kananan makarantu da sauransu. Kano Integrity Forum ta ce kirkiro sababbin masarautu rahama ce ga Jihar Kano, inda ta nuna rashin jin dadi kan yadda ake cece-ku-ce kan kirkiro masarautun.

A wata tattaunawa da Aminiya, Shugaban Kungiyar (KIF), Farfesa Abdu Salihi, ya ce kirkiro sababbin masarautun zai sa a samu ci gaba a fannin samar da aikin yi da bunkasa ilimi da kiwon lafiya a yankunan karkarar jihar, inda ya kawo misalai da ayyukan fadada asibitoci da makarantu da Gwamna Ganduje ya ce zai yi a sababbin masarautun.

Ana cikin haka ne kuma sai gwamnatin Jihar Kano ta ce ta samu bukata daga wasu kungiyoyi da suke neman a cire Sarki Muhammadu Sanusi daga karagar sarauta. Kuma ana ganin wannan ne ya sanya dattawa da masu fada-a-ji na Arewa da kuma ita kanta fadar Shugaban Kasa suka hanzarta shigowa cikin batun don yi wa tufkar hanci ta hanyar kafa wani kwamiti don shiga tsakani a samu maslaha.

Kalubalen da ke gaban Kwamitin Abdulsalami

A wannan mako ne Kungiyar Dattawan Arewa ta kafa wani kwamiti a karkshin jagorancin tsohon Shugaban Kasa Janar Abdulsalami Abubakar  don kawo karshen sa-toka-sa-katsin da ke tsakanin Sarkin Kano da Gwamnan Jihar Kano Dokta Abudullahi Ganduje. Kwamitin ya ce zai yi ganawar sirri da shugabannin biyu a mabambantan lokuta domin fahimtar kowanne daga cikinsu tare da gano hanyar da za a bi don warware matsalar cikin sauki.

Sai dai ana cikin haka Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya tafi Saudiyya don yin Umara inda ya ce da zarar ya dawo zai gana da kwamitin a Abuja.

Kwamitin mai mutum 10 ya kunshi Alhaji Adamu Fika da Janar Muhammadu Inuwa Wushishi da Farfesa Ibrahim Gambari da Dokta Umaru Mutallab da Dokta Dalhatu Sarki Tafida da kuma Sheikh Shariff Ibrahim Saleh, sai Shugaban Majalisar Gwamnonin Najeriya kuma Gwamnan Jihar Ekiti, Kayode Fayemi da kuma Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari.

Wani masani da gidan rediyon BBC ya tattauna da shi da ya nemi a sakaya sunansa ya ce “Bisa la’akari da manyan mutanen da ke cikin kwamitin, muna da kwarin gwiwar cewa za a cimma matsaya dangane da wannan rikici.Wani abu ma shi ne Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi suna jin maganar ’yan kwamitin.”

Masanin ya ce wannan sulhu zai iya daukar fuska uku kamar haka:

1.’Yan kwamitin za su iya lallashin Gwamna Ganduje ya rushe sababbin sarakunan hudu domin komawa yadda ake a da wato Sarki daya a Kano. 2. Ko kwamitin ya ja hankalin Sarki Sanusi ya hakura ya zauna da sarakunan hudu da Gwamna Ganduje ya nada su zama sarakuna biyar a jihar kamar yadda al’amarin yake kafin cire Jihar Jigawa daga Kano. 3. Ko idan kwamitin ya so zai iya tsayawa a tsakiya ta hanyar barin Sarki Sanusi a matsayin Sarki Mai Daraja ta Daya, su kuma sauran sarakunan hudu su kasance masu daraja ta biyu.

Sai dai tuni gwamnatin Kano ta ce kada ma kwamitin ya nemi a rusa sababbin sarakunan a cikin batutuwan da za a tabo lokacin sulhun.

A cewar masanin, “Gwamna Ganduje da Sarki Sanusi za su shiga yanayin gaba kura baya sayaki kasancewar duk wanda ya bujire wa matakin da kwamitin ya dauka to za a yi masa kallo marar son maslaha.”

Ya ce rikicin ya janyo raba zumunci a tsakanin ’yan uwa, inda misali aka ‘gwara’ kan ’ya’yan marigayi Sarki Ado Bayero da na marigayi Sarki Sanusi. Har wa yau ya ce “Idan ka dubi abin da ya faru a Dambatta, an cire Sarkin Bai an sa Wada Waziri wanda dan uwa ne ga Sarkin Bai ka ga ke nan zumunci ya rabu.Sannan ga yadda aka cire Hakimin Minjibir aka dora dagaci ya maye gurbinsa, to ka ga ai husuma ta hadu. Haka idan ka dubi yadda aka hada masarautun da ba sa jituwa wuri daya. Misali yaya za a yi a ce Wudil na karkashin Gaya? Ko kuma Gwarzo na karkashin Karaye? Saboda haka wannan sulhu zai yi matukar tasiri a tsakanin jama’a kuma muna matukar farin ciki da shi. Allah Ya sa ’yan kwamiti su lalubo bakin zaren.”

Yanzu dai Kanawa da sauran jama’ar Najeriya sun zuba ido su ga yadda za ta kaya bayan kwamitin ya kammala tattaunawa da bangarorin biyu.

More Stories