✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda rikicin Abuja ya yi ajalin mutum 8

Rikcin ya rikide zuwa na kabilanci a Kasuwar Katako da ke yankin Dei-dei

Yankin Deidei mai dauke da kasuwanni sama da biyar a Abuja ya fada cikin halin tarzoma, da ya kai ga ajalin mutum takwas.

Lamarin ya biyo bayan mutuwar wata mata da wani dan acava ya goyo, inda wata tankar iskar gas ta bi ta kanta bayan faduwar babur da take kai, ta mutu nan take.

Lamarin ya faru ne a wata mahadar hanya da ta nufi daya daga cikin kasuwannin yankin da misalin karfe 11 na ranar ta Laraba, kamar yadda Aminiya ta sami labari.

Wasu da aka zanta da su a wajen sun bayyana cewa, matukin babur din ya tsira da rauni, ciki har da hannunsa da motor ta taka.

Dayyabu Abdullahi wani da ya zanta da Aminiya ya ce rigimar ta fara ne bayan wasu matasa daga kasuwar katako daura da inda hatsarin ya faru sun bukaci da a mika musu dan acabar daga hannun abokan sana’arsa da ke kokarin ba shi agaji.

“A karshe sun samu nasarar kwace shi sannan suka shige da shi cikin kasuwarsu duk da jini da yake zuba daga jikinsa.

“Gabanin hakan sun banka wa babur dinsa wuta, kuma daga nan ba a sake jin duriyarsa ba,” inji Malam Dayyabu.

Ya ce matasan, wadanda ’yan kabilar Igbo ne, sun kuma kwace babura daga hannun wasu ’yan acaba kusan goma suka cinna musu wuta a wajen.

Daga bisani rigimar ta koma ta kabilanci a tsakanin bangarorin biyu, kamar yadda Aminiya ta samu labari.

An kuma cinna wuta kan shaguna kusan 20 a cikin kasuwar ta katako, sai kuma motoci kamar 10 da a ka kona a tashar mota da ke kasuwar, kamar yadda wakilinmu ya kirga.

Yawancin wadanda suka rasa ran nasun, sun mutu ne a sakamakon harbin su da aka yi a lokacin da suka yi dafifi a kusa da wani masallaci da ke wajen, bayan isowar jami’an tsaro da misalin karfe daya na rana.

Surajo Abubakar wani da ya zanta da Aminiya ya ce mutum biyu sun rasa ransu a kowane daya daga cikin masallacin biyu.

Malam Surajo ya ce sai akwai karin mutum biyu da suka rasu a wani kemis da ke kusa da kasuwar Tumatur ta Deidei, inda aka garzaya da wadanda suka tsira da raunuka.

Ya ce an yi harbin ne daga cikin kasuwar ta katako, sai dai ya ce babu tabbacin ko harbin na jami’an tsaro ne ko kuma na masu gadin kasuwar ne.

Mutum na bakwai ya rasa ransa ne a bakin hanya bayan ya gudo daga cikin kasuwar ta dauke da raunuka na sara, inda ya fadi kasa ya mutu.

Sai kuma na karshe da ke zargin ya ritsa da shi kansa matukin babur din, bayan matasan sun shige da shi cikin kasuwar kuma ba a sake jin duriyarsa ba.

A bangare guda kuma, an fasa gilasan motoci kimanin 20 a kan babbar hanya ta Deidei inda matasa ’yan acaba suka rika auka wa motocin masu wucewa ta wajen, bayan tantance direban motar.

Tini dai zaman lafiya ya dawo yankin a yammacin na Laraba, inda jami’an tsaro ke sintirin da bayar da kariya ga ’yan kasuwa da ke ta fitowa zuwa babbar hanya ta Deidei don zuwa inda suke da zama, sai kuma kariya musamman ga kasuwar ta katako.